Daga Bakin Mai Ita tare da Ilyan Laure

Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo:
Daga Bakin Mai Ita tare da Ilyan Laure

Filin Daga Bakin Mai Ita na wannan makon ya karɓi baƙuncin mai fitowa a finafinan Hausa na Kannywood, Ibrahim Abdullahi Fagge - wanda aka fi sani da Ilyan Laure.

An haife shi a unguwar Fagge da ke birnin Kano, kuma ya yi firamare da sakandare a birnin.

Ya ce tun yana ƙarami yake sha'awar fitowa a finafinai. Fim dinsa na farko shi ne Daɗin Kowa na tashar Arewa 24.

Sai dai ya fi shahara da fim ɗinsa mai suna Laure, wanda ya ce ya fi sonsa a cikin duka finafinan da ya fito.