Keta haƙƙin ɗan'adam na ƙaruwa ne ko raguwa a Najeriya?

Lokacin karatu: Minti 3

Akwai haƙƙoƙi da ke tattare da kowane ɗan'adam kuma akwai dokoki da aka shata na kare haƙƙi ɗan'adam a duniya.

Saboda muhimmancin ɗan'adam ne Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar 10 ga watan Disamba a matsayin ranar kare haƙƙin ɗan'adam ta duniya.

Kuma an keɓe ranar ne domin tunawa da yarjejeniyar da aka amince ta kare haƙƙin ɗan'adam a ranar 10 ga watan Disamban 1948.

Kuma haƙƙoƙin ɗan'adam sun ƙunshi yin rayuwa da ƴanci ba tare da la'akari da launin fata da jinsi da ƙasa da ƙabila da harshe da addini ko bambancin ra'ayi da zamantakewa ko kuma wani matsayi ba.

Amincewa da kuma jaddada muhimmanci da dacewar haƙƙin ɗan'adam a rayuwarmu, shi ne taken bikin ranar ta bana. Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce mutunta haƙƙin ɗan'adam zai iya ƙarfafa wa al'umma don samar da makoma mai kyau.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya ce, "Haƙƙin ɗan'adam shi ne ginshikin zaman lafiya da adalci da kuma hada kan al'ummomi."

Akwai dokoki na haƙƙin ɗan'adam na ƙasa da ƙasa waɗanda suka yi tanadin matakin da gwamnatoci za su ɗauka da kuma aiwatar da hanyoyin nisantar wasu ayyukan da za su kai ga take haƙƙin ɗan'adam, domin tabbatar da ƴanci na ɗan'adam ko kuma ƙungiyoyi.

Domin mutunta haƙƙin ɗan'adam ne aka samar da matakai da dokoki domin aiki da su don neman mafita ga matsalolin al'ummar duniya.

Sai dai a ƙasashe da dama da suka amince da dokokin yarjejeniyar kare haƙƙin ɗan'adam na ci gaba da saɓawa da kuma ƙalubalantarsu.

'Matsalar ta fara ƙamari a Najeriya'

Najeriya na ɗaya daga cikin ƙasashen da ake gudanar da bikin wannan rana kuma ɗaya daga cikin batutuwan da ake dibawa a ƙasar shi ne yadda ake keta haƙƙin mutane a matakin jihohi a Najeriya, inda ake zargin ana kama abokan hamayya da masu sukar gwamnati, ana kwazzaba masu.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam a ƙasar sun ce al'amarin ya fara kamari, har aukuwarsa na neman zama wani ruwan dare a jihohin Najeriyar.

Galibi dai, idan ana magana kan korafe-korafen da suka shafi keta hakkin bil'Adama a Najeriya, hankali ya fi karkata ne ga gwamnatin tarayya.

Batun kama wasu yara 'yan asalin jihar Kano, da ake zargi suna da hannu a zanga-zangar da aka yi a watannin baya ta nuna damuwa game da tsadar rayuwa a kasar ya ja hankali a Najeriya, kasancewar wasunsu da dama yara ne ƙanana da kuma yanayin da aka tsare su.

Ɗaya daga cikin lauyoyin da suka tsaya wa yaran Barista Hamza Nuhu Dantani, ya ce akwai dokoki da dama da aka saɓa na keta haƙƙokin yaran.

"Ɗauko su da aka yi daga Kano zuwa Abuja an tauye haƙƙinsu domin a Kano ake zargin an aikata laifi,"

"An tauye masu haƙƙinsu na rashin kai su kotu a lokacin da ya kamata a kai su kotun, kuma an muzgunawa rayuwarsu a yanayin da aka tsare su," in ji Barista Hamza Nuhu Dantani.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun kuma nuna damuwa kan abubuwan da suka faru a kwanan baya inda aka zargi gwamnatocin jihohi da dama kan keta haƙƙin ɗan'adam, kamar Kano da Sakkwato da Kaduna da Yobe.

Ƙungiyar Amnesty International a Najeriya ta ce matsalar ta fara yin ƙamari a ƙasar, musamman kamen da ake yi wa masu amfani da shafukan sada zumunta idan sun yi furucin da bai yi wa gwamnati daɗi ba, kamar yadda Malam

Isa Sanusi, darakta kungiyar a Najeriya ya shaida wa BBC.

"Matsalar take haƙƙin ɗan'adam a Najeriya na neman zama ruwan dare a jihohi kuma gwamnoni ne ke nuna cewa ba a isa a soke su ba, ba za a iya faɗa masu gaskiya ba. Saboda yawanci waɗanda ake kamawa waɗanda suka fito ne suka nuna cewa gwamnatin jiha ta gaza sai a yi amfani da jami'an tsaro a kama shi," in ji Malam Sanusi.

Ya ƙara da cewa al'ummar da suka zaɓi shugabanni suna da haƙƙi su faɗa masu gaskiya idan har sun ga cewa shugabannin sun gaza.

Ya ce dokokin Najeriya sun yi tanadi ko da a ce wani ya yi suka tare da cin zarafin shugabanni.

Masu sharhi kan al'amura na ganin, yayin da ya kamata mahukunta su rika nuna halin adalci da dattaku idan aka yi masu tsokaci irin na gyara kayanka, su ma masu tofa albarkacin baki wajibi ne su guji ture kurtun alhaki garin neman ladan.