Guguwar MIlton ta raba ɗaruruwan mutane da gidajensu a Florida

Ɓarnar da guguwar Milton ta yi

Asalin hoton, REUTERS/Marco Bello

Lokacin karatu: Minti 2

Guguwar Milton na ƙara bazuwa a sassan Florida lamarin da ke janyo iska mai ƙarfi da ambaliya tare da jefa mutum sama da miliyan biyu da kuma masana'antu cikin halin rashin wuta.

An tabbatar da mutuwar mutane a DSt Lucie da ke gabar gabashin Florida sai dai ba babu ƙarin bayani kan adadin su.

Gwamnan jihar, Ron DeSantis ya ce guguwar ta yi wa kusan gidaje 125 ɓarna - galibinsu tafi da gidanka.

An rage ƙarfin guguwar daga maki biyar zuwa ɗaya - amma tana ci gaba da yin ɓarna.

Gidaje da wuraren kasuwanci miliyan biyu a halin da ake ciki ba su da lantarki. Zuwa dare, da yawan unguwanni za su zama kufai yayin da jami'an agajin gaggawa ke gargaɗin cewa akwai haɗari a amsa kiran waya saboda walƙiya.

Rundunar ƴansanda ta gaɓar Atalantik ta ce an yi mace-mace a wani wurin shaƙatawa bayan da guguwar ta yi dirar mikiya cikin abin da bai wuce minti 20 ba.

Ofishin ƴansanda na St Lucie ya bayyana motocin da suka kife sannan suka yi tafiyar ɗaruruwan mitoci.

Hukumomi a jihar sun aike da kusan jami'an tsaro 10,000 tare da abincin mutum miliyan 20 da kuma lita miliyan 40 na ruwa domin rarrabaa mutanen da guguwar ta yi wa ta'adi.

Fiye da gidaje miliyan 2.6 da wuraren kasuwanci suna cikin duhu a sassan Florida , a cewar ƙididdigar baya-bayan nan.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ta kuma yi tasiri a wasu jihohin inda kimanin kwastamomi 70,000 suke fama da rashin wuta a North Carolina sai wasu 37,000 a Georgia.

Wasu ɓangarorin filin wasan ƙwallon baseball mai karɓar ƴan kallo mutum 42,000 a Florida sun yi yaga yaga sakamakon mahaukaciyar guguwar ta Milton.

Yayin da iska mai gudun kilomita 205 duk sa'a ta faɗa St Petersburg, tarkacen rufin filin wasan na Tropicana Field sun tarwatse.

Kafofin yaɗa labarai sun ce ana amfani da filin wasan a matsayin mafaka ga jami'an bayar da agaji amma babu rahotannin jikkata.

Filin wasan gida ne ga babbar ƙungiyar ƙwallon Baseball ta Tampa Bay Rays.

Mutane a birnin St Petersburg na Florida suna fama da matsalar ruwan sha bayan da aka tilasta wa jami'ai rufe hanyoyin samar da ruwan sha sakamakon ɓarnar da guguwar ta yi.

Jami'ai sun ce matakin zai iya kai wa har zuwa lokacin da za a kammala muhimman gyare-gyare kuma za a iya yin hakan ne kawai idan aka tabbatar cewa ba zai janyo wata matsala ba idan ma'aikata suka fita waje, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

An shawarci duka mazauna jihar da su tafasa ruwa kafin sha ko yin girki ko ma wanke baki.

Cibiyar da ke sa ido kan guguwa ta ƙasa ta ce guguwar Miton a yanzu tana raguwa daga gaɓar gabas maso kudancin Florida".

A wani saƙo a shafin X, hukumar ta ce har yanzu guguwar na janyo iska mai ƙarfi da kuma mamakon ruwa".

..

Asalin hoton, Getty Images