Mahaukaciyar guguwar Haiyan: Jiya da yau

Hotunan garuruwan Philippines da mahaukaciyar guguwar Haiyan ta yiwa barna.

Garin Anibong da ke kusa da birnin Tacloban
Bayanan hoto, Hotunan Philippines da aka dauka ta sama na nuna irin barnar da mahaukaciyar guguwar ta yi a kwaruruwa irin su Tacloban da ke tsibirin Leyte da Guiuan, na lardin Gabashin Samar. Wannan garin Anibong ne da ke kusa da birnin Tacloban.
Mahaukaciyar guguwar ta watsa jiragen kasa zuwa gabar teku.
Bayanan hoto, Jiragen ruwa a gabar Anibong kusa da birnin Tacloban, inda mahaukaciyar guguwar ta yi mummunar barna.
Birnin Tacloban: Jiya da Yau
Bayanan hoto, A garin Tacloban, birni mafi girma kan tsibirin Leyte, kimanin mutane 10,000 ne ake fargabar sun mutu.
Wata mata na laluben kayanta a Tacloban. AP
Bayanan hoto, Wadanda suka tsira sun fara laluba buraguzan gidajensu don ganin abubuwan da suka tsira.
Jiya da yau - Filin saukar jiragen sama na Tacloban
Bayanan hoto, Mahaukaciyar guguwar ta yi barna a filin saukar jiragen sama na Tacloban, inda ta rusa gine-gine, ta tumbuke bishiyu, tare da kifar da motoci.
Cikin filin jiragen saman Tacloban. Reuters
Bayanan hoto, Jiragen soji na iya sauka a yanzu dauke da kayan agajin da ake matukar bukata.
Garin Guiuan - Jiya da yau
Bayanan hoto, Guiuan na cikin garuruwan da mahaukaciyar guguwar ta fara sauka kuma tayi matukar barna.
Masu dibar ganima a shagon ajiye kayayyaki.
Bayanan hoto, An samu rahoton dibar ganima a wasu shagunan ajiya bayanda karancin abinci ya addabi mutane.