Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fitattun ƴan Najeriya da suka rasu a shekarar 2025
Kamar kowace shekara 2025 ta zo kuma ta wuce da abubuwa da farin cikin da kuma akasin haka.
Shekarar ta 2025 ta kasance ɗaya daga cikin shekaru mafiya tarihi ga Najeriya, ta yadda ƴan ƙasar da dama ba za su taɓa mantawa da su ba.
Abubuwa da dama sun faru waɗanda za su ci gaba da zama a zukatan wasu ƴan ƙasar har natsawon laokaci.
Shekara ce da fitattun ƴan ƙasar - kama da shugabanni da ƴansiyasa da malamai da ƴan kasuwa da dama suka mutu.
Cikin wannan muƙala za mu duba manyan mace-macen da suka girgiza ƴanƙasar a wannan shekara.
Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari
A tsakiyar watan Yuli ne Najeriya ta samu wani labari da ya shiga kundin tarihinta na rauswar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari, wadda ya rasu ranar Lahadi 13 ga watan na Yulin shekarar ta 2025.
Fadar shugaban Najeriya ta ce ya rasu da misalin ƙarfe 4:30 "sakamakon doguwar jinya".
Mutuwar Buhari ta girgiza ƴan ƙasar da dama ciki har da manyan ƴansiyasar ƙasar, waɗanda aka gani suka sharɓar kuka a wajen jana'izarsa.
Shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya bayar da umarnin yi wa Buhari jana'izar ban girma a mahaifarsa da ke Daura ta jihar Katsina, Inda shi da kansa ya jagioranci gudanar da jana'izar a gaban dimbin al'umma ciki har da manyan ƴansiyasa da sojojin ƙasar.
Sheikh Dahiru Bauchi
Da asubahin ranar Alhamis ta 27 ga watan Nuwamban 2025 ne Allah ya yi wa fitaccen jagoran ɗarikar Tijjani a Najeriya, Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi rasuwa
Fitaccen malami ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga koyar da al'kur'ani, littafin Musulmi mafi girma.
Shehun malamin na ɗaya daga cikin malamai a Najeriya da suke sadaukar da rayuwarsu wajen yi wa addinin Musulunci hidima.
Cikin wata hira da Shehun Malamin ya yi da BBC a 2019 ya ce abu biyu da ya fi ƙauna a rayuwarsa shi ne karatun Alƙur'ani da kuma sanya fararen tufafi.
Birgediya Janar M Uba
A ranar 18 ga watan Nuwamban 2025 ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya tabbatar da mutuwar jajirtaccen jami'in sojin ƙasar, Birgediya Janar Musa Uba, wanda mayaƙan ƙungiyar Iswap suka kashe a jihar Borno.
Tun da farko wasu rahotonnin kafafen yaɗa labaran ƙasar suka fara ruwaito cewa mayaƙan ISWAP sun yi garkuwa da jami'in sojin a wani kwanton ɓauna da suka yi wa sojojin.
Kodayake daga bisani sojojin ƙasar sun ƙaryata cikin wata sanarwa da suka fitar, amma daga baya mutuwarsa ta tabbata bayan da mayaƙan ISWAP suka fitar da wani bidiyo da ke nuna yadda suka halaka shi.
Rundunar sojin ƙasar dai ba ta ce komai ba game da bidiyon ISWAP ɗin da ke yawo a intanet.
Sai dai cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar 18 ga watan Nuwamba, Shugaba Tinubu ya ce mutuwar janar ɗin "ta kaɗa" shi.
Olubadan Oba Olakulehin
A farkon watan Yuli ne shi ma Sarkin Ibadan da ake yi wa laƙabi da Olubadan, Oba Owolabi Olakulehin, ya rasu bayan fama da jinya.
Mutuwar basaraken mai shekara 90 a duniya ta girgiza ƴan Najeriya da dama, musamman mazauna yankin kudu maso yamacin Najeriya.
Basarake mai ɗimbin farjin jini a wajen al'ummarsa, duk da yake shekarasa guda a kan garakar sarautar kafin rauswarsa.
Marigayin ya kasance, sarkin Ibadan na 43 a lokacin da ya hau karaga a 2024.
Aminu Alhassan Dantata
A makon ƙarshe na watan Yuni ne shahararren ɗankasuwar nan Alhaji Aminu Ɗantata ya rasu.
Marigayin ya rasu yana da shekara 94 da haihuwa a shekarar miladiyya, amma a shekarar hijira yana da shekara 97, kamar yadda sakatarensa Mustapha Abdullahi ya shaida wa BBC a lokacin rasuwar tasa.
Hamshaƙin attajirin ya rasu ne a Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa bayan fama da jinya, kamar yadda wani ɗansa ya shaida wa BBC.
An kuma binne shi a maƙabartar Baƙi'a da ke birnin Madina a ƙasar Saudiyya.
Bayanai sun nuna cewa marigayin ya sha bayyana sha'awarsa cewa "Allah ka kashe ni a wannan gari" a duk lokacin da ya ziyarci garin Madina da ke Saudiyya.
Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi
A farkon watan Afrilu ne Shi ma tsohon Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi ya suwa yana da shekara 92.
Mutuwar basaraken ta girgiza al'ummar arfewacin Najeriya, musamman mazauna Kano sabioda farin jininsa tsakanin al'umma.
Kafin rasuwarsa, Alhaji Abbas Sanusi ya kasance babban ɗan majalisar Sarki a lokacin marigayi Sarki Ado Bayero a matsayin Wamban Kano da Sarki Aminu Ado Bayero na 15.
Sarkin Muhammadu Sanusi II ne ya fara naɗa shi sarautar sarkin Dawakin tsakar gida hakimin Ungogo a 1959, sannan a 1963 kuma Sarkin Kano Inuwa ya yi ɗaga likkafarsa zuwa Dan Iya.
Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi
A ranar Juma'ar farkon watan Afrilu ne aka wayi gari da rasuwar fitaccen malamin addinin musulunci a Najeriya, Sheikh Idris Abdul'aziz Dutsen Tanshi.
Rasuwar malamin ta girgiza ƴanƙasar da dama musamman mabiya mazhabar Ahlussunna da ke ganinsa a matsayin jigo a tafiyar.
Malamin mai shekara 68 ya rasu ne bayan fama da jinya, inda har ya je neman lafiya ƙasashen Indiya da Saudiyya.
Sheikh Tanshi ya rasu ya bar mahaifiyarsa da mata guda uku da kuma ƴaƴa 32.
Edwin Clark
A daren ranar Litinin, 17 Fabrairu na shekarar 2025 ne, dattijon yankin Neja Delta da ke kudancin Najeriya kuma tsohon kwamashina, Edwin Clark ya rasu, inda ya rasu yana da shekara 97 da haihuwa.
Edwin ya kasance wani babban jigo a yankin kudancin Najeriya, kuma tsohon shugaban ƙungiyar rajin kare yankin Neja Delta ta Pan Niger Delta Forum (PANDEF), inda yake yawan fitowa yana magana kan halin da ƴan yankinsa ke ciki.
An haife shi ne a garin Kiagbodo da ke yankin Ijaw na jihar Delta, ya yi aiki tare da gwamnan mulkin soja Samuel Ogbemudia, da Janar Yakubu Gowon tsakanin shekarun 1966 zuwa 1975.
Yana cikin sanatocin jamhuriya ta uku a zamanin mulkin Shehu Shagari, inda suka yi wata uku a majalisa a shekarar 1983.
Ya riƙe muƙamin kwamashinan yaɗa labarai a shekarar 1975.
Janar Abdullahi M Adangba (mai ritaya)
A farkon watan Nuwamban 2025 ne Allah ya yi wa tsohon shugaban ma'aikata na fadar shugaban Najeriya Manjo Janar, Abdullahi Mohammed Adangba (mai ritaya), rasuwa.
Janar Adangba (mai ritaya), ya kasance shugaban ma'aikatar fadar gwamnatin Najeriya a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo da Umaru Yar'Adua.
Marigayin ɗan asalin jihar Kwara, ya rasu yana da shekara 86 a duniya, kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta bayyana a saƙon ta'zaiyyar rasuwarsa.
Shugaba Tinubu ya ce ba za a man ta irin gudunmowar da mariogayin ya bayar a fagen tsaron Najeriya, musamman sauye-sauyen da ya kawo a hukumomin leƙen asirin ƙasar.
Manjo Adangba ya kasance tsohon gwamnan tsohuwar jihar Bendal tsaknin 1975 zuwa 1976.