Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilan da za su sa alawar cakuleti kara tsada
Yayin da wasu ke hakura da wasu burukansu na sabuwar shekara, wani mai bincike a jami'ar Oxford, ya yi ikirarin cewa cakuleti ba abu ne da yanzu zai zamo mai saukin samu.
Farashin cakuleti ya tashi da kusan kashi 15 cikin 100 a shekarar da ta gabata, a cewar ofishin kididdiga na Birtaniya.
Dr Tonya Lander, ta jami'ar Oxford da ke bincike kan makomar abinci ta zayyana wasu dalilai biyar da za su iya haddasa tsadar cakuleti.
Na farko guguwar El Nino da sauyin yanayi da kalubalen da abubuwan da ake hada cakuleti ke fuskanta da kuma harajin shigar da kayayyaki da ma illar yadda al'ummar Ghana ke komawa hakar zinare maimakon noman Gahawa.
Ta ce wasu daliban Ghana ne suka ja hankalinta wajen gudanar da bincikenta ba ma su kadai ba har da na kasashen Cote d'Ivoire da na Indonesia, wadanda suna daga cikin kasashen da ake noman gahawa da ake hada cakuleti da ita.
Dr Lander ta ce, farashin gahawa ya dan daidaita a shekaru 25 da suka gabata.
Amma, a shekaru biyun da suka wuce ya tashi inda ya kai ana sayen tan daya a kan fam dubu takwas, ma'ana farashin ya ninka har sau uku ke nan.
Mai kamfanin da ke samar da cakuletin kamfanin Hampshire chocolatier, shi ma ya fuskanci tsadar gahawar.
Ya ce, yayin da ake ci gaba da cinikin cakuletin, farashinta ya yi tashin goron zabi.
Mai kamfanin ya ce, duk da tsadar cakuletin, cinikinta bai ragu ba saboda bukatarta da mutane ke yi.
Hatta cakuletin da ake hadawa a gida ma farashinsa ya tashi.
Kate Rumsey, da ke hada cakuleti a gida, ta ce tana shirin bunkasa sana'arta ta hanyoyin da dama amma hakan ya gagara.
Ta ce kayan da ake hada alawar cakuletin farashinsu ya tashi, "sannan mu kuma ba mu canja wani abu daga cikin abubuwan da muke amfani da su wajen hada cakuletin ba a don haka dole mu kara farashin kayanmu."
Ta kara da cewa labarin tashin farashin gahawa ya taimaka sosai saboda masu siyan kayan sun fahimci dalilin na kara farashin cakuletin.