'Gazawar gwamnonin arewa ce matsalar da yaran da aka kama suka shiga'

Lokacin karatu: Minti 3

Al'umma a faɗin Najeriya na ci gaba da bayyana takaicinsu kan bidiyon yaran da aka gurfanar gaban kotu daga wasu jihohin arewacin ƙasar.

Yaran waɗanda gwamnati ta zarga da cin amanar ƙasa, sun bayyana a hotuna da bidiyo mabanbanta cikin yanayi na galabaita, ta yadda wasunsu ko tsayuwa ba sa iya yi.

Masu ruwa da tsaki da kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun yi tir da wannan mataki na kai yara ƙanana gaban kotu, tare da bayyana shi a matsayin cin zarafinsu.

Ra'ayi na bayan nan shi ne wanda gwamnan jihar Baushi Bala Abdulƙadir Muhammad ya bayyana wa BBC kan lamarin, wanda ya ce ya samu kiraye-kiraye daga sassa daban na ciki da wajen Najeriya kan lamarin.

Ya ce "wannan abu ya bamu tsoro tare da nuna babu tausayi abin ya ƙazanta gabatar da yara wadanda ba su balaga ba gaban kotu.

" Mu kuma a matsayinmu na gwamnoni ya nuna mana akwai abin da ya kamata mu yi wanda ba ma yi na kula da yara. Idan aka yi kame ya kamata a riƙa duba yadda yaran da aka kama su ke a gidajen tsaro da sauransu".

Kamar mafi yawan wadanda suka rigaye shi bayyana ra'ayinsu, Bala Muhammed ya ce ya saɓawa doka haɗa waɗannan yara da manya a gidajen yari, wanda idan ba a bi a hankali ba, babu abin da hakan zai haifsar sai ƙarin 'kangara' ga yaran.

An tambayi Gwamnan me yasa tun tuni a matsayinsu na jagorori ba su ɗauki matakin bibiyar waɗannan yara da aka kama ba sai yanzu?.

Sai ya ce da farko babu wanda zai amince da tarzoma da fasa dukiyoyin gwamnati, musammam jagororin al'umma hakan barazana ce.

"Sai dai mu ba mu san waɗannan ƙananan yaran aka kama ba, sai da hotunansu suka bayyana, waɗansu ma almajirai ne da ke gaban malamansu, kuma kasan babu ƙidaya a irin wannan kamen," in Bala.

Ya kuma bai wa gwamnan jihar Kano inda aka ce waɗannan yaran da yawansu daga nan suka fito kariya kan cewa bai sansu ba, ballanta su da suke jihar Bauchi.

"Amma dama muna sane da cewa an kama, mun ɗauka za a yi adalci a ajiye su gidan yara a riƙa kula da su kamar yadda doka ta tanada ana ba su abinci to amma fitowar hotunansu sun ɗaga mana hankali.

"Mun yi tir da wannan ƙuduri da gwamnatin tarayya ta yi. Saboda akwai dokoki iri-iri da suka kare yara ƙanana da ba su balaga ba, waɗanda muka rattaba hannu akai bisa yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya," in ji Gwamnan Bauchin.

Ya ce ƙa'idojin da aka kawo daban-daban na sharadi gabanin asake su duka abin takaici ne.

Bala ya shaida wa BBC cewa ko matakin mayar da shari'ar hannun babban mai shari'a na ƙasar ihu ne bayan hari, domin an riga "an gama galabaita, yara sun sha wahala kuma zuciyarsu a bushe".

Wasu yaran da aka kama almajirai ne suka shiga zanga-zangar ba tare da sanin iyayensu ba, kamar yadda gwamnan ya bayyana.

Ya ce za su cika ka'idojin beli da aka shimfiɗa a kotu domin kuɓutar da yaran.

Amma suna buƙatar a kula da su bayan karbo su.

Dole a gayawa gwamnantin tarayya ba a cin zarafin ɗan adam musamman ƙananan yara, daga yankin da su ne suka zaɓi wannan gwamnati, in ji Bala Mohammed