Juventus na zawarcin Zirkzee, PSG da Barcelona na gogayya kan Jhon Duran

Joshua Zirkzee

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Juventus na sha'awar ɗaukar ɗan wasan gaban Netherlands Joshua Zirkzee a matsayin aro amma ɗan wasan mai shekara 23 ba ya son barin Manchester United. (Sky Sports)

An yi wa Manchester United tayin ɗan wasan Juventus da ƙasar Serbia Dusan Vlahovic, mai shekara 24, a wata yarjejeniyar musaya da Zirkzee. (Teamtalk)

Paris St-Germain na sha'awar siyan Jhon Duran kuma ana kyautata zaton Aston Villa za ta iya karɓar tayin fam miliyan 60 kan ɗan wasan na Colombia mai shekara 21.(Talksport)

Tuni dai darektan wasanni na Barcelona Deco ya gana da wakilan Duran don tattaunawa kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan gaban na Aston Villa. (Sport)

Bayern Munich na son kawo cikas a yunƙurin Manchester United na sayen ɗan wasan Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 26, daga Sporting. (Star)

Real Madrid ta ki amincewa da tayin da aka yi mata na sayen ɗan wasan baya na ƙasar Netherlands Virgil van Dijk, wanda zai zama ɗan wasa mai zaman kansa idan kwantiraginsa na Liverpool ya ƙare a bazara. (Relevo)

Ƙungiyoyin gasar Saudi Pro League na fatan ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Brazil Casemiro, mai shekara 32, daga Manchester United a wannan watan. (Telegraph)

Manchester United da Tottenham na zawarcin ɗan wasan gaban Faransa Randal Kolo Muani a matsayin aro daga Paris St-Germain a wannan watan, yayin da Juventus ma ke sha'awar ɗan wasan mai shekara 26. (Athletic)

AC Milan na son ɗaukar Marcus Rashford, mai shekara 27 a matsayin aro amma duk wata yarjejeniya za ta dogara ne akan Manchester United ta biya wani kaso mai tsoka na albashin ɗan wasan gaban na Ingila. (Guardian)

Real Betis na ɗaya daga cikin ƙungiyoyi da dama da ke fatan ɗaukar ɗan wasan gaban Manchester United da Brazil Antony, mai shekara 24, a matsayin aro zuwa ƙarshen kakar wasa ta bana. (Independent)

Ɗan wasan gaba na West Ham Niclas Fullkrug na cikin ƴan wasan da Juventus ke zawarci a watan Janairu, inda kulob ɗin na Italiya ke son ɗaukar ɗan wasan na Jamus mai shekara 31 a matsayin aro. (Calciomercato)

Ɗan wasan Brazil Matheus Cunha, mai shekara 25, yana nazarin zaɓin da ke gabansa kafin ya yanke shawarar sanya hannu kan sabon kwantiragi da Wolves. (Sky Sports)

Liverpool na shirin miƙa tayi kan ɗan wasan Feyenoord ɗan ƙasar Algeria Anis Hadj Moussa, mai shekara 22. (Football Insider)