Kotun ɗaukaka ƙara ta ba Trump damar ci gaba da tsarin harajinsa

Asalin hoton, OTHERS
Shugaba Trump ya bayyana hukuncin wata kotu na dakatar da harajin da ya lafta wa kasashen duniya a matsayin abin tsoro, kuskure kuma mai alaka da siyasa.
A ranar Laraba ne wasu manyan alkalai suka yanke hukuncin cewa Mista Trump ya saba wa kundin tsarin mulki wajen lafta wa kasashen da ke shigar da hajojinsu Amurka haraji, inda ta ce wannan iko ne na majalisar dokokin kasar.
Hakan ya sa lauyoyin Trump suka daukaka kara, inda a ranar Alhamis kotun daukaka kara ta dakatar da hukuncin waccan kotun ta farko tare da bai wa Trump damar ci gaba da aiwatar da tsarin harajin nasa yayin da take ci gaba da sauraron karar.
Shugaba Trump ya bayyana hukuncin kotun farkon – wanda ya dakatar da shirin nasa na lafta haraji da cewa mummuna ne da ya saba kuma siyasa ce kawai.
Mai ba wa Shugaba Trump shawara kan harkokin kasuwanci Peter Navarro ya ce, batun wannan haraji, ya zauna daram.
Ya ce : ''Kotun ta gaya musu cewa , su je su aiwatar da tsarin ta wata siga, inda ya ce ko da sun yi rashin nasara a kotu, za su iya bullowa ta wata hanyar – yana mai bayar da tabbacin cewa manufa da tsarin harajin na gwamnatin Trump na nan daram.''
Navarro ya ce, batun a yi amfani da kotuna wajen dakatar da Trump aiwatar da abubuwan da ya yi wa Amurkawa alkawari, dole ne a dakatar da shi.
Daman tun kafin hukuncin karamar kotun na hana gwamnatin Trump aiwatar da tsarin lafta harajin, shugaban ya dage tsarin har zuwa watan Yuli domin samun damar cimma yarjejejiniya da kasashen da abin ya shafa.
Fadar gwamnatin Amurka, ta yi kakkausar suka a kan hukuncin kotun ta farko.
Tana mai zargin alkalan kotun da yin kafar ungulu ga yunkurin shugaban kasar na magance gibin kasuwanci na Amurka.
A yanzu dai bayan hukuncin kotun farko da kuma wannan hukuncin na wucin-gadi na kotun daukaka kara, ana sa ran batun zai kai har ga kotun koli, idan a karshe kotun daukaka karar ta yi hukuncinta na karshe
To amma a halin yanzu dambarwar na kara rura wutar rashin tabbas, a kan yarjejeniyar da Shugaba Trump zai yi da shugabannin kasashen duniya, da kuma kara haifar da rashin tabbas a kasuwannin duniya.











