Waɗanne abubuwa Donald Trump ya yi a kwanaki 100 na farkon mulkinsa?

- Marubuci, By the Visual Journalism Team
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- Lokacin karatu: Minti 6
A ranar da ya sha rantsuwa 20 ga watan Janairu, shugaban Amurka Donald Trump ya yi alkawarin cewa zai gudanar da mulki a kwanaki 100 na shugaban ƙasa wanda ba a taɓa gani ba a tarihin ƙasar.
Tsawon gomman shekaru, ana ɗaukar kwanaki 100 a matsayin gwaji na yadda kamun ludayin sabon shugaban ƙasa zai kasance - lokaci na waiwaye don duba irin ci gaba da sabuwar gwamnatin ta kawo.
Alkaluma na wannan lokaci sun nuna mana irin ci gaba da gwamnatin Trump ta samu kan wasu alkawura da ta ɗauka daga ƙarin haraji, kamawa da mayar da ƴan ci-rani gida da kuma rage kashe kuɗaɗe da gwamnati ke yi.
Farin jinin gwamnati
An kwatanta irin farin jinin gwamnatin Trump a wa'adi na biyu da irin waɗanda ya gada - wata hukuma ce ke gudanar da irin wannan gwaji idan sabuwar gwamnati ta cika kwanaki 100 - Ta ɗauki gomman shekaru tana yin haka.
Trump shi ne shugaba na farko bayan yaƙin duniya da ya yi shugabanci sau biyu ba a jere ba, wanda ya sa farin jinin gwamnatinsa ya kasu kashi biyu.
A nan, mun duba dukkan shugabannin ƙasar da aka zaɓa bayan yaƙin duniya na II, da kuma yadda kamun ludayin gwamnatocin suka kasance a kwanaki 100 na farko.
Gwamnatin John F Kennedy ta samu farin jinin al'umma da ya kai kashi 83 yayin da Ronald Reagan ya samu kashi 67. Joe Biden da Bill Clinton ba su samu farin jini sosai ba a kwanaki 100 na farkon shugabancinsu, sai dai sun samu sama da kashi 50.
Trump shi ne shugaban ƙasa na farko bayan yaƙin duniya da ya samu ƙasa da rabin goyon bayan al'umma a kwanaki 100, a dukkan wa'adin mulkinsa biyu.
Wa'din mulkin Trump na biyu ya kasance mai yawan magoya baya da kuma farin jini, inda ƴan jam'iyyar Republican tara cikin goma ke goyon bayansa idan aka kwatanta da kashi 4 na ƴan Democrat.
Babu alkaluman da ke nuna irin farin jinin da waɗanda suka karasa w'adin mulkin wani shugaba suka samu, kamar Lyndon B Johnson, wanda ya zama shugaban ƙasa a 1963 bayan kisan gillar da aka yi wa Jonh F Kennedy.
Hukumar da ke tattara alkaluman farin jinin mai suna Gallup ya gudanar da wata kuri'a jin ra'ayin jama'a daga 1-14 ga watan Afrilu, lokacin da kasuwanni ke cikin tsaka mai wuya bayan ƙarin harajin Trump.
Sai dai kashi 44 sun nuna cewa an samu sauyi ba irin kuri'ar ra'ayi da aka gudanar kan Trump ba, wanda ya nuna daidaito lokacin watanni uku na farkon wa'adin mulkinsa na biyu.
An gudanar da kuri'ar jin ra'ayin kan mutum 1,000.
Ɗaukar mataki nan take
Trump ya yi alkawari lokacin yaƙin neman zaɓensa cewa zai ɗauki mataki nan take kan manyan batutuwansa. Ya sha alwashin cewa a ranarsa ta farko zai rage farashin kayayyaki da yi wa waɗanda ake zargi da tayar da hankali a majalisar dokokin ƙasar a 2021 afuwa.
Bai samu nasarar cimma waɗannan abubuwa duka ba, sai dai idan za a duba irin matakai da shugaban ƙasa ke ɗauka, Trump shi ne shugaban da yake yin abubuwa cikin sauri a wannan lokaci - inda ya ɗauki matakai kan abubuwa da dama waɗanda gwamnatin tarayya za ta aiwatar ba sai majalisa ta amince ba.
Wannan ya haɗa da umarnin da ke bisa doka. Trump ya ɗauki matakai da dama a kwanaki 100 na farkon mulkinsa fiye da kowane irin shugaban ƙasar Amurka cikin shekara 100 da suka gabata.
Ya riga da ya ɗauki matakai sama da rabin wanda ya yi lokacin mulkinsa na farko - kuma kusan kashi 90 na yawan waɗanda Joe Biden ya yi a tsawon mulkinsa na shekara huɗu.
Ɓangaren tattalin arziki
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Trump ya samu nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa a watan Nuwamban 2024, bayan da ya yi alkawarin rage farashin kayayyaki da bunƙasa ayyuka ga Amurkawa. Mutane da dama sun yi na'am da irin alkawuransa - kamar yadda aka gani a ɓangaren farashin hannayen jari bayan da ya samu nasara.
Farashin hannayen jarin sun kasance suna ƙaruwa a farkon mulkin kowane shugaban ƙasa. Sai dai a ɓangaren Trump hannayen jarin ba su ƙaru ba sun kasance yanda suke musamman bayan ƙara haraji.
Hannayen jarin sun yi matukar faɗuwa lokacin da Trump ya ɓullo da sabbin haraje-haraje kan kayayyaki da ke shiga ƙasar, wanda kuma ya shafi duniya baki-ɗaya ranar 2 ga watan Afrilu.
Sai dai Trump ya yi amai ya lashe kan wasu daga cikin haraje-harajen mako ɗaya bayan lafta su, abin da ya janyo kasuwanni suka farfaɗo. Amma rashin tabbas ɗin da ya haifar na ƙoƙarin kyautata kasuwar duniya ya sa tattalin arzikin duniya shiga wani hali.
Wani abu mai muhimmanci shi ne yadda Amurkawa ke kallon tattalin arzikin ƙasar.
Masu saye sun nuna damuwa kan yaƙin kasuwanci da Trump ya janyo a watan Afrilu, inda mutane da dama suka fuskanci raguwar kuɗaɗen shiga da kuma fuskantar hauhawar farashi.
Shi kansa Trump ya ki yin watsi da cewa za a iya samun koma-bayan tattalin arziki, amma ya ɗau alwashin cewa matakansa za su haifar da ɗa mai ido.
Ba za a iya fayyace yadda wasu ɓangarorin tattalin arzikin ƙasar ke ciki ba a wannan lokaci - ciki har da hauhawar farashi, wanda aka ce zai iya sake ƙaruwa sakamakon tsare-tsaren haraji na Trump.
Kasuwanci da haraji
Shugaba Trump ya kare matakinsa na lafta sabon haraji a duniya ta hanyar cewa zai haifar da ƙarin ayyukan yi da kuma masana'antu ga Amurkawa - kuma zai rage koma-baya da kasuwannin ƙasar ke samu.
A bara, Amurka ta saya ko kuma shigo da kayayyaki sama da wanda ta sayar, ko kuma ta fitar.
Bambanci tsakanin wannan shi ake kira rashin daidaito a kasuwanci. Kasuwannin Amurka sun kasance cikin rashin daidaito na gomman shekaru - yanzu Trump na son kawo karshen hakan.
Sai dai ana fargabar cewa sabbin harajin Trump zai haifar da tasiri mara kyau - abin da ya janyo mutane da dama suka yi ta rububin sayan kayayyaki bayan sake zaɓan Trump.
Kuɗin yawan kayayyaki da aka shiga da su Amurka a watan Janairu kaɗai ya kai dala miliyan 329 - wanda rabon da a ga irin haka a wata guda tun aƙalla 1992, alkaluma kuma da suka ɗan ragu a watan Febrairu.
Duk da dakatar da wasu haraji da Trump ya lafta a wata sanarwa ranar 9 ga watan Afrilu, akwai rahotanni da ke cewa Amurkawa na ƙara sayan kayayyaki saboda fargabar rashin tabbas.
Har yanzu akwai haraji mai tsanani kan kayayyaki daga China da za su shiga Amurka, sai dai Trump ya nuna alamar cewa zai iya rage harajin idan za a iya cimma matsaya da China.
Matakai kan shige da fice
Trump ya yi ƙakkausar suka kan ɓangaren shige da fice na Amurka kafin ya koma kan mulki, inda ya sha alwashin ƙorar baki da suka shiga ƙasar ba bisa ka'ida ba da ba a taɓa ganin irinsa ba, da kuma kawo karshen samun shaidar zama ɗan ƙasa kai-tsaye wanda yanzu waɗanda aka haifa a Amurka ke samu.
Sai dai bai ƙori baki da yawa kamar yadda ya yi alkawari ba kawo yanzu, kuma kotuna sun daƙile yunkurinsa na kawo karshen shaidar zama ɗan ƙasa kai-tsaye ga wasu yara.
Wani mataki da shugaban zai yi iƙirarin samun nasara shi ne hana masu shiga Amurka ba bisa ka'ida ba ta iyakar Mexico.
A watan Maris ɗin 2025, an kama ƴan ci-rani 7,000 a kan iyakar - idan aka kwatanta da sama da 137,000 a watan Maris ɗin 2024, lokacin mulkin Biden.
Babu alkaluma da yawa kan shige da fice wanda zai iya nuna kwanakin 100 na mukin Trump ya samu nasara a ɓangaren.
Sai dai shugaban ƙasar da tawagarsa sun yi amfani da raguwar kame a kan iyaka, da kuma ƙaruwar waɗanda jami'an kwastam da na shige da fice ke tsarewa a cikin ƙasar, wajen iƙirarin cewa sun samu nasara a ƙoƙarinsu na daƙile masu shiga ƙasar ba bisa ka'ida ba da kawo gyara a iyakar da Biden bai ɗauki mataki ba.
A lokaci guda, an samu raguwar waɗanda ake mayarwa gida, kuma an fuskanci matsaloli a ɓangaren shari'a.
Idan aka ci gaba da samun ƙaruwar waɗanda ake tsarewa, akwai fargabar cewa cibiyoyin tsare mutane na jami'an kwastam da na shige da fice za su cika makil - har a rasa wuri.
Yayin da ake samun tirka-tirka a kotu, za a mayar da hankali kan makomar tsarin shige da fice na gwamnatin Trump cikin kwanaki 100 masu zuwa.
Za a yi alkalancin sauran tsare-tsaren Trump kan abubuwan da zai cimma cikin watanni kaɗan masu zuwa.
Yadda Amurkawa za su mayar da martani kan matakai da yake ɗauka a kan iyaka, yaƙin kasuwanci da ke gaban ƙasar da kuma sauyawar farashin kayayyaki, zai iya nuna cewa ko Trump shi ne shugaban da zai janyo rarrabuwa a zamanin yanzu.











