'Yanwasan da ƙungiyoyinku na Premier League ke buƙata kafin rufe kasuwar bana

Yoane Wissa, da Gigi Donnarumma, da Eberechi Eze

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Waɗanne 'yanwasa ne za su sauya sheƙa kafin rufe kasuwar bana?
    • Marubuci, Phil McNulty
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Marubucin wasanni
  • Lokacin karatu: Minti 4

Zuwa yanzu ƙungiyoyin gasar Premier League ta Ingila sun kashe sama da fan biliyan biyu a bazarar nan, amma har yanzu akwai cinikin da ba a kammala ba kafin rufe kasuwar a ranar Litinin, 1 ga watan Satumba.

Sashen wasanni na BBC Sport ya duba abin da manyan ƙungiyoyi 10 ke buƙata su yi kafin rufe kasuwar ta bana.

Arsenal

Viktor Gyokeres

Asalin hoton, Getty Images

Yayin da ake tunanin Arsenal ta kammala komai bayan ɗaukar 'yanwasa ciki har da lamba 9 Viktor Gyokeres.

sai kuma lissafi ya sauya saboda raunin da ɗanwasan gaba Kai Havertz ya ji, wanda ya sa ta fara neman ɗanwasan Crystal Palace Eberechi Eze.

Da ma can an yi ta ba da shawara cewa ya kamata Arsenal ta ɗauki ɗanwasa mai buga gefen hagu kamar Gabriel Martinelli, amma ba ta ce komai ba har sai yanzu.

Idan cinikin Eze ya faɗa, to da alama babu sauran wani abu kuma a filin wasa na Emirates.

Chelsea

Xavi Simons

Asalin hoton, Getty Images

Da alama har yanzu mai horarwa Enzo Maresca bai haƙura da ƙarin cefane ba kafin rufe kasuwar, yayin da yake neman Alejandro Garnacho na Man United da ɗanwasan RB Leipzig Xavi Simons.

Sai dai komai zai dogara ne da yawan 'yanwasan da ta iya sayarwa kamar Nicolas Jackson da Christopher Nkunku da Tyrique George.

Kociyan zai kuma so ya ƙarfafa bayansa saboda yadda aka ce Levi Colwill ba zai buga mafi yawan gasar bana ba saboda rauni a gwiwarsa.

Crystal Palace

Palace ba ta yi wata sayayyar kirki ba zuwa yanzu, amma ana sa ran abubuwa za su sauya nan gaba kaɗan saboda mai horarwa Oliver Glasner na neman ɗanwasan gaba da na baya.

Za a yi yunƙurin ne saboda makomar ɗnbaya kuma kyaftin ɗinta Marc Guehi da kuma ɗanwasan gaba Eberechi Eze.

Ana alaƙanta Palace da Jeremy Jacquet na Rennes, yayin da kuma take harin ɗanwasan tsakiya Bilal El Khannouss na Leicester City.

Liverpool

Hugo Ekitike

Asalin hoton, Getty Images

Kociyan Liverpool Arne Slot ya samu kuɗaɗen cefane masu yawa a bana waɗanda ya sayi Florian Wirtz, da Jeremie Frimpong, da Milos Kerkez, da Hugo Ekitike, da Giovanni Leoni.

Amma duk da haka yana fatan sake kashe miliyoyi wajen maye gurbin ɗanwasan baya Jarell Quansah da kuma sama wa Virgil van Dijk abokin aiki.

Ana sa ran za ta nemi Marc Guehi na Crystal Palace. Sai kuma turka-turkar sayen ɗanwasan gaba Alexander Isak daga Newcastle.

Manchester City

Manchester City ta sayi mafi yawan 'yanwasanta tun kafin gasar Club World Cup, kuma wasu majiyoyi sun faɗa wa BBC cewa ta gama sayayya.

An yi ta raɗe-raɗin cewa tana son ɗaukar golan Paris Saint-Germain Gianluigi Donnarumma, amma tabbas wannan zai danganta ne da 'yanwasan da za ta sayar ita ma.

Tottenham ta nuna sha'awar ɗaukar Savinho amma City ta ƙi amincewa zuwa yanzu. Amma idan ta yarda to hakan zai iya ba ta damar sayen ɗanwasan Real Madrid Rodrygo.

Manchester United

Kociyan Manchester United Ruben Amorim ya mayar da hankalinsa kan ɓangaren gaba na tawagar tasa inda ya kashe fan miliyan 200 zuwa yanzu domin sayen Matheus Cunha, da Bryan Mbeumo, da Benjamin Sesko.

Amma a bayyane take cewa United na da matsala a mai tsaron raga, yayin da Andre Onana ya gaza kuma shi ma Altay Bayindir ya fara aikata manyan kurakurai a wasansu da Arsenal.

United na tunanin ɗaukar Gianluigi Donnarumma na PSG, amma anya akwai lokaci na yin wannan babbar sayayyar kafin cikar wa'adi?

Newcastle United

Alexander Isak

Asalin hoton, Getty Images

Har yanzu makomar Alexander Isak na cikin kokwanto duk da yunƙurin mai horarwa Edie Howe na ƙarfafa tawagarsa.

Zuwa yanzu ta sayi Anthony Elanga daga Bournemouth, da Jacob Ramsey daga Aston Villa, da Malick Thiaw daga AC Milan.

Yanzu kuma tabbas hankalinta zai karkata kan ɗanwasan gaba saboda dama tun kafin rikici da Isak tana buƙatar ƙari.

Yanzu dai ta ƙwallafa kan Yoane Wissa amma kuma tana fuskantar turjiya daga Brentford saboda yadda ta ƙi yarda da tayin fan miliyan 40 kan mai shekara 28 ɗin.

Nottingham Forest

Nottingham Forest ta kashe fan miliyan 140 zuwa yanzu domin shirya komawa taka leda a gasar zakarun Turai.

Yanzu haka tana shirin ɗaukar Douglas Luiz daga Juventus. Mai tsaron ragarta Matz Sels ya yi ƙoƙari sosai amma duk da haka za ta so ta sama masa abokin gogayya.

Tottenham Hotspur

Eberechi Eze celebrates with FA Cup

Asalin hoton, Getty Images

Tabbas Tottenham za ta nemi ƙarfafa tawagar mai horarwa Thomas Frank kafin rufe kasuwa, musamman saboda tafiyar kyaftin Son Heung-min da kuma mummunan raunin da James Maddison ya ji.

An ce tana tunanin ɗaukar Yoane Wissa a gaba, da Savinho na Man City a gefen hagu, sannan za su iya neman ɗanwasan tsakiya kamarMaghnes Akliouche na Monaco.

West Ham United

Tsakiyar fili ce babbar matsalar West Ham.

Kociya Graham Potter na buƙatar tsaro a tsakiya, abin da ya sa yake neman Mateus Fernandes na Southampton da Marc Casado na Barcelona.

Tana buƙatar 'yan tsakiya aƙalla; wanda zai tare da kuma wanda zai rarraba ƙwallo.