Ronaldo ya gama yajin taka leda, Ko Zidane zai dawo Madrid?

Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran Cristiano Ronaldo zai kawo ƙarshen yajin aikin da yake yi a Al-Nassr inda zai ci gaba da taka leda a gasar Saudiyya ta Saudi Pro League a ranar Asabar. Ɗanwasan na Portugal mai shekara 41 ya ƙauracewa wasa biyu inda ya nuna fushinsa kan yadda ake tafiyar da ƙungiyar. (Sky Sports)
Zaɓen shugabancin Barcelona ne zai tantance makomar ɗanwasan gaba na Ingila Marcus Rashford a Nou Camp. Makomar ɗanwasan na Manchester United ta dogara ne da sake zaɓen Joan Laporta a matsayin shugaban Barca. (Times - subscription required)
Manchester United na harin ɗanwasan gaba na Everton da Senegal Iliman Ndiaye mai shekara 25 idan har Rashford ya zama mallakin Barcelona. (Caught Offside)
Bournemouth na shirin danƙarawa matashin ɗanwasan gaba na Faransa Eli Junior Kroup kwantaragi mai gwaɓi yayin da manyan ƙungiyoyi irinsu Chelsea da Liverpool da Real Madrid da Paris St-Germain ke ribibinsa. (Sun)
Manchester City na shirin lale fam miliyan 100 domin ɗauko ɗanwasan tsakiya na Nottingham Forest da Ingila Elliot Anderson. (Teamtalk)
Bayern Munich na sa ido kan ɗanwasan Atletico Madrid da Argentina Julian Alvarez, wanda Arsenal ke hari. (Christian Falk)
AC Milan na fatan Fulham za ta saye ɗanwasanta na Najeriya mai shekara 26 Samuel Chukwueze, wanda ke taka leda a Ingila a matsayin aro. (Gazzetta - in Italian)
Manchester United na son ɗanwasan tsakiya na Borussia Monchengladbach mai shekara 23 Rocco Reitz, wanda farashinsa ya kai fam miliyan 35. (Fichajes - in Spanish)
Ɗanwasan tsakiya da Manchester United ke nema Sandro Tonali daga Newcastle United, farashinsa zai iya kai wa fam miliyan 100. Ɗanwasan mai shekara 25 na jan hankalin Arsenal da Manchester City dakuma Juventus. (Talksport)
Ana tunanin manyan ƙungiyoyi a Turai za su yi sauye-sauye a watanni masu zuwa, amma Luis Enrique ya ce yana jin daɗi a PSG. (Fabrizio Romano)
Wasu daga cikin ƙunyiyoin sun haɗa da Real Madrid, da ake tunanin za ta iya ɗauko Jurgen Klopp. Ana kuma tunanin Zinedine Zidane zai iya sake dawowa karo na uku. (ESPN)
Shugabancin Liverpool zai tantance makomar kocin ƙungiyar Arne Slot idan har ya gaza samar wa Liverpool gurbin buga gasar zakatun Turai. (Football Insider)










