Zaɓukan da za a maye gurbin wasu manyan jami'an gwamnati

.

Asalin hoton, Social Media handle

    • Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
    • Aiko rahoto daga, Abuja

A yau ne hukumar zaɓen Najeriya ta shirya don gudanar da zaɓukan cike gurbi a wasu jihohin ƙasar 27.

Zaɓukan sun hadar da na 'yan majalisun dattawa na da wakilai da kuma majalisun dokoki na wasu jihohin ƙasar.

Za dai a gudanar da zaɓukan ne sakamakon hukunce-hukuncen kotuna da suka buƙaci a sake gudanar da zaɓukan a wasu rumfuna da mazaɓun 'yan majalisar.

ƙarƙashin dokar zaɓen ƙasar shari'ar zaɓen 'yan majalisa na ƙarewa ne a kotun ɗaukaka ƙara, yayin da na shugaban ƙasa da gwamnoni ke tuƙewa a kotun ƙolin ƙasar.

Wasu dalilan kuma sune saboda muƙaman gwamnati da aka bai wa wasu zaɓaɓɓun 'yan majalisar.

A ranar 25 ga watan Fabrairun bara ne aka gudanar da zaɓukan 'yan majalisun dattawan da kuma na wakilai, tare da na shugaban ƙasar.

Sai kuma a ranar 18 ga watan Maris aka gudanar da zaɓukan 'yan majalisun dokoki na duka jihohin ƙasar, tare da na wasu gwamnoni.

Jihohin da za a yi zaɓukan

.

Asalin hoton, INEC

Bayanan hoto, Za a gudanar da zaɓukan a jihohi 26 na ƙasar

Hukumar zaɓen kasar ta ce za a gudanar da waɗannan zaɓukan ne a jihohi 26 a ƙasar.

Ga jerin jihohin da yankunan da za a gudanar da wannan zaɓe:

Arewa maso yamma: A wannan yanki za a gudanar da zaɓukan a kusan duka jihohin yankin guda bakwai da suka haɗar da Kaduna da Kano da Jigawa da Katsina da Sokoto da Kebbi da kuma Zamfara.

Arewa ta tsakiya: Hukumar INEC za ta gudanar da irin waɗannan zɓuka a jihohi hudu da ke wannan yanki da suka haɗar da Benue da Plateau da Nasarawa da kuma jihar Neja.

Arewa maso gabas: Jihohin da za a gudanar da zaɓukan a wannan yanki sun hadar da Borno da Bauchi da Taraba da Yobe da kuma jihar Adamawa.

Kudu maso yamma: A wannan yanki za a gudanar da zaɓukan a jihohin Legas da Ondo da kuma jihar Oyo.

Kudu maso kudu: Za a gudanar da zaɓukan a jihohin Delta da Akwa Ibom da Bayelsa da kuma jihar Cross River a wannan yanki.

Kudu Maso gabas: Jihohin da za su fuskanci zaɓukan a wannan yanki su ne Ebonyi da Anambra da kuma jihar Enugu

Jami'an gwamnati da za a maye gurbinsu

Akwai 'yan majalisun dokokin ƙasar da shugaban kasar Bola Tinubu ya naɗa wasu muƙamai ciki har da ministocinsa, wadanda suma ake sake zaɓuƙansu a yau.

A kundin tsarin mulkin Najeriya, idan aka bai wa zaɓaɓɓen ɗan majalisa muƙami a majalisar zartaswar ƙasar, to dole ne ya sauka daga kan kujerar da aka zaɓe shi, domin bayar da dama a sake zaɓar wani a kujerar.

'Yan majalisun dokokin ƙasar da suka samu muƙamai a majalisar zartaswar sun haɗar da:

Femi Gbajabiamila

.

Asalin hoton, Femi Gbajabiamila

Bayanan hoto, Tsohon kakakin majalisar wakilan ƙasar ya zama shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa

Tsohon kakakin wakilan ƙasar ,wanda a baya yake wakiltar mazaɓar Surulere 1 daga jihar Legas.

Za a sake zaɓen kujerarsa, bayan da shugaba Tinubu ya naɗa shi a matsayin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa.

Femi Gbajabiamila ya daɗe a majalisar wakilan Najeriya, wanda yake a majalisar tun shekarar 2003, inda ya riƙe muƙamai kama daga shugaban masu rinjaye har zuwa kakakin majalisar

David Umahi

.

Asalin hoton, X/David Umahi

Bayanan hoto, Ministan ayyuka na Najeriya

An zaɓi David Nweze Umahi - wanda shi ne tsohon gwamnan jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin Najeriya - a matsayin sanatan da ke wakiltar Ebonyi ta Kudu a majalisar dattawan ƙasar.

Sai kuma kuma bayan rantsar da majalisa ta 10 ne, sai shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanya sunansa cikin jerin mutanen da yake son naɗawa muƙaman ministoci a ƙasar.

Bayan da majalisar dattawan ta tantance shi ya zama sabon ministan ayyuka na ƙasar.

David Nweze Umahi ya kasance tsohon gwamnan jihar Ebonyi har sau biyu, tsakanin 2015 zuwa 2023, sai dai kafin nan ya riƙe muƙamin mataimakin gwamnan jihar.

Ibrahim Geidam

.

Asalin hoton, .

Bayanan hoto, Ministan kula da ayyukan 'yan sanda na Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Yoben da ke kudu maso gabashin ƙasar - wanda kuma zaɓaɓɓen sanata ne da ke wakiltar Yobe ta gabas a majalisar dattawan ƙasar - na daga cikin 'yan majalisun da za a sake zaɓen kujerarsu.

Sanata Ibrahim Geidam ya far zuwa majalisar dattawan ƙasar ne tun a shekarar 2019 bayan kammala wa'adin mulkinsa na biyu a jihar Yobe.

Shugaban ƙasar Bola Tinubu ya naɗa shi a matsayin sabon ministan kula da ayyukan 'yan sanda na ƙasar.

Olubunmi Tunji-Ojo

.

Asalin hoton, X/Olubunmi Tunji-Ojo

Bayanan hoto, Ministan cikin gida na Najeriya

Ministan cikin gida na Najeriyar ya kasance zaɓaɓɓen ɗan majalisar wakilan ƙasar daga jihar Ondo da ke kudu maso yammacin ƙasar.

Olubunmi Tunji-Ojo, ya je majalisar wakilan ƙasar ne tun shekarar 2019.

Sai dai bayan ƙaddamar da majalisar ta 10 ya samu sunansa cikin jerin sunayen da shugaba tinubu ya aike wa majalisa domin tantancewa, daga nan ne kuma ya samu muƙamin ministan cikin gida.

Dakta Tanko Sununu

.

Asalin hoton, Tanko Sununu

Tanko Sununu zaɓaɓɓen ɗan majalisar wakilai ne daga jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Tun shekarar 2019 ɗan majalisar ke wakiltar mazaɓar Yauri Shanga da Ingaski a majalisar wakilan ƙasar.

Shugaba Tinubu ya naɗa shi ƙaramin ministan ilimin ƙasar bayan da ya samu shiga kunshin ministocin ƙasar.

Wane shiri 'yan sanda suka yi?

.

Asalin hoton, Nigerian Police

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Babban sifeton 'yan sandan ƙasar, Olukayode Egbetokun, ya bayar da umarnin taƙaita zirga-zirgar ababen hawa a kan tituna da ruwa da sauran hanyoyin zirga-zirga a wuraren da za a gudanar da waɗannan zaɓuka, tun daga ƙarfe 12:00 na daren ranar Juma'a zuwa ƙarfe 6:00 na maraicen ranar Asabar.

Cikin wata sanarwa da rundunar 'yan sandan ta fitar, ta ce dokar taƙaita zirga-zirgar ba ta shafi masu muhimman ayyuka ba, kamar ma'aikatan kashe gobara da 'yan jarida da jami'an INEC da likitoci da masu sanya ido a zaɓukan.

“Sifeton 'yan sanda ya umarci duka jam'iyyun siyasa, da 'yan takara da magoya bayansu da su bi doka da oda, domin kuwa 'yan sanda ba za su lamunci duk wani yunƙuri na kawo cikas ga zaɓen ba'', in ji sanarwar.

Haka kuma sanarwar ta ƙara da kiran mutane da su kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba da zai niya kawo cikasa ga zaɓukan.

Babban sifeton 'yan sandan ya kuma ce rundunar ta kammala duk wasu shirye-shirye domin tabbatar da cewa an gudanar da zaɓen cikin kwanciyar hankali da lumana.