Ƴan Barcelona Cancelo da Felix za su buga wa Portugal Euro 2024

Ƴan wasan Barcelona biyu Joao Cancelo da Joao Felix suna cikin wadanda Portugal ta gayyata Euro 2024 da Jamus za ta karbi bakunci a watan Yuni.

Haka kuma tawagar Jamus ta gayyaci Ter Stegen da Ilkay Gundogan da kuma ta Faransa da ta kira Kounde, domin buga wasan da za a fara cikin watan Gobe.

Tuni dai tawaggogin da suka samu gurbin shiga gasar da za a fara daga 14 ga watan Yuni, suke sanar da ƴan ƙwallon da za su buga musu gasar ta Euro 2024.

Koci, Roberto Martinez ya bayyana Cancelo da Felix cikin ƴan ƙwallo 26 da za su buga wa Portugal babbar gasar tamaula ta nahiyar Turai.

Ƴan wasan da Portugal ta bayyana:

Rui Patricio, Diogo Costa, José Sá, Cancelo, Semedo, Pepe, Danilo, António Silva, Nuno Mendes, Rúben Dias, Diogo Dalot, Gonçalo Inácio da kuma Bernardo Silva.

Sauran sun hada da Bruno Fernandes, Rúben Neves, Palhinha, Vitinha, João Neves, Otávio, João Félix, Cristiano Ronaldo, Leão, Francisco Conceiçao, Gonçalo Ramos, Diogo Jota da kuma Pedro Neto.

Cancelo da Felix sun koma Barcelona tun kan fara kakar bana, wadanda suka taka rawar gani a wasannin da ƙungiyar ta kara a bana.

Cancelo ya buga wa Barcelona wasa 41 da cin kwallo biyu, sai kuma Felix da ya yi mata karawa 43 da cin kwallo 10.

Felix shine na uku a yawan ci wa Barcelona ƙwallo, wanda ya yi kan-kan-kan da Ferran Torres da kuma Fermín.