Ƴan wasan ƙwallon ƙafa na buƙatar hutu - Kompany

Lokacin karatu: Minti 1

Kocin Bayern Munich Vincent Kompany ya yi kira da a ƙayyade yawan wasannin da kowanne ɗan wasa zai iya bugawa duk shekara sakamakon damuwar da ake nunawa kan lafiyar ƴan wasa.

Kungiyar Kompany na fafatawa a sabuwar gasar zakarun Turai da aka yi wa garambawul - wanda a yanzu ke da ƙarin aƙalla wasanni biyu kafin a kai ga zagayen gaba - da kuma gasar cin kofin duniya ta ƙungiyoyi 32 na farko da za a fara a bazara mai zuwa.

Buƙatar Kompany ta biyo bayan iƙirarin da ɗan wasan tsakiya na Manchester City Rodri ya yi cewa ƴan wasan na dab da shiga yajin aiki domin nuna adawa da ƙaruwar yawan wasanni.

Tsohon kyaftin ɗin City ya ce "Buga wasanni 75 zuwa 80, zai iya haifar da lamarin da zai fi ƙarfin ɗan wasa."

"Shawarar da ne ke bayar wa a kodayaushe shine a ƙayyade adadin wasannin da kowanne ɗan wasa zai iya bugawa. A ƙayyade, a kuma sanya lokacin hutun dole da kowanne ɗan wasa zai ɗauka."

Bayern za ta iya buga wasanni har zuwa 64 a kakar wasa ta bana, inda kakarta za ta iya ci gaba har zuwa ranar 13 ga watan Yuli - lokacin da za a buga wasan ƙarshe na cin kofin duniya ta ƙungiyoyi.

Da yawa daga cikin ƴan wasanta kuma za su buga wasannin tawagogin ƙasashensu.