Yadda sabon harajin Najeriya zai shafe ku a 2026

Asalin hoton, Bayo/X
- Marubuci, Usman Minjibir
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
A ranar 1 ga watan Janairun 2026 ne ake sa ran sabuwar dokar haraji ta Najeriya za ta fara aiki wadda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya saka wa hannu domin amincewa ta zama doka.
An dai ta tunanin cewa za a dakatar da fara aiwatar da harajin kafin sabuwar shekara sakamakon zarge-zargen cushe da aka yi wa dokar ta haraji, wadda aka ce ta bambanta da asalin wadda majalisar dokoki ƙasar ta amince da ita.
A ranar 30 ga watan Disambar 2025 ne shugaba Tinubu ya sanar da cewa babu buƙatar dakatar da fara aiwatar da harajin domin hakan zai katse wa Najeriya burinta na samar da cigaban da ake buƙata.
Sai dai ya ce yana sane da irin zarge-zargen da ake yi dangane da cushe a dokar kuma yana aiki da majalisar dokokin ƙasar wajen samar da mafita.
Yanzu dai abin da al'ummar Najeriyar ke son sani shi ne ta yaya wannan haraji zai shafe su daga ranar 1 ga watan Janirun sabuwar shekarar 2026? BBC ta yi nazarin dokar harajin ga kuma bayanan da ta tattara.
Wane ne zai biya haraji?

Asalin hoton, Getty Images
Duk wani ɗan Najeriya da ke samun kuɗin shiga a Najeriya walau dai ma'aikaci ne ko ɗan kasuwa ko masu shirye-shirye a kafafen sada zumunta ko masana'antu ko kamfanoni, za su biya haraji.
Haka kuma dokar ta ce duk wani ɗan Najeriya da ke neman kuɗi a ƙasashen waje amma kuma yana zaune gida Najeriya, to shi ma zai biya wannan haraji.
Sai dai kuma tanade-tanaden dokar harajin sun keɓe duk wanda kuɗin shigarsa bai wuce ₦800,000 a shekara ba daga biyan harajin kuɗin shiga. Wannan yana nufin cewa ma'aikatan da ke karɓar albashi mafi karanci ba za su biya harajin kuɗin shiga ba.
Nawa ne harajin?
Hukumar tattara harajin ta tarayya wato FIRS, wadda yanzu ta koma Nigeria Revenue Service wato NRS, a kundin da ta fitar ta nuna cewa kasancewarku ƴan Najeriya ba shi ne zai sa ku biya harajin ba illa dai yawan samun da kuke yi, inda ta saka sharaɗin da sai mutum ya kai zai fara biyan haraji.
- Babu haraji a kan N800,000 ta farko
- N2,200,000 za a biya kaso 15 na kuɗin
- N9,000,000 za a biya kaso 18 na kuɗin
- N13,000,000 za a biya kaso 21 na kuɗin
- N25,000,000 za a biya kaso 23 na kuɗin
- N50,000,000 za a biya kaso 25 da kuɗin
Jerin mutane da abubuwan da aka ɗauke wa haraji
Bisa kundin hukumar tattara harajin ta Najeriya, an ɗauke harajin daga kan wasu kuɗade da mutane kamar haka:
- Mutumin da ke samun kuɗi daidai da albashin ma'aikacin Najeriya mafi ƙanƙanta na N72,000, a wata.
- Mutumin da samunsa a shekara bai wuce N1,200,000 ba.
- Kyauta (babu haraji a kyauta).
- Kuɗin da mutum ke tarawa na fansho.
- Kuɗin fansho da garatuti.
- Kuɗin insorar lafiya.
- Asusun lamunin gidaje.
- Riba a kan kuɗaɗen rance na mutumin da ke cikin gida yake son ya malleke shi.
- Kuɗaɗen insora.
- Kuɗin sallamar ma'aikaci daga aiki da ba su wuce N50,000,000 ba.
- Kuɗin da aka sayar da gidan da aka ma'aikaci ya mallaka bayan shekaru yana zaune a ciki.
- Kuɗin da mutum ya sayar da wata kadara da bai wuce N5,000,000 ba.
- Sayar da motoci na ƙashin kai da ba su wuce biyu a shekara ba.
- Riba a kan hannun jarin da ba ta kai N150,000,000 a shekara ko kuma N10,000,000.
- Kuɗaɗen jinƙai da na ƙungiyoyin addini (waɗanda ba don riba aka kafa su ba)
- Ƙananan masana'antu da uwar kuɗin jarinsu ba ta wuce N100,000,000 ba ko kuma gabaɗaya jarin bai wuce N250,000,000.
- Ƙananan ƴan kasuwa da suke tasawa.
Harajin da aka ɗauke kan kayayyaki (VAT) da suka haɗa da:
- Kayan abinci.
- Kuɗin haya.
- Harkoki da kayan karatu.
- Harkar lafiya.
- Magunguna.
- Ƙananan kamfanoni da ribarsu ba ta wuce N100,000,000 ba.
- Fetur, dizel da kayan wuta mai amfani da hasken rana.
- Kayan noma - Takin zamani, iri, abincin dabbobi da dabbobi masu rai.
- Saye ko lamuni ko hayar kayan aikin gona.
- Na'urorin da nakasassu ke amfani da su kamar abin jin magana da kujerar masu nakasa da abin rubutu makafi.
- Sufuri - motar haya wadda ba mutum ne ya ɗauke ta shata shi kaɗai ba.
- Motoci masu amfani da wutar lantarki da kayansu.
- Kayayyakin jinƙai.
- Kayan jarirai.
- Kayan tsaftar mata . tawul da audugar mata.
- Ƙasa da gine-gine.
Harajin da aka ɗauke na kuɗaɗe da bankuna ke cirewa (Stamp duties):
- Aikewa da kuɗin da bai wuce N10,000 ba.
- Albashi.
- Aikewa da kuɗi tsakanin banki guda.
- Aikewa da takardun kuɗaden lamuni da hannun jari na gwamnati.
- Dukkanin takardun da ke ɗauke da hannun jari.
Mutanen da aka yi wa sassauci
- Ma'aikacin da albashinsa na shekara bai wuce N20,000,000, zai rinƙa biyan kaso 18 maimakon 25.
- Sassaucin kaso 20 a shekara ga (Masu biyan kuɗin haya).
Ta yaya za a cire harajin?

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan tambaya na yawan fitowa ne daga ɗaiɗaikuwar mutane kuma abin da ya kamata a sani shi ne akwai haraji iri biyu dangane da masu aiki da ƴan kasuwa.
- Harajin ƴan kasuwa:
Wannan na ɗaya daga cikin harajin da ake da Harajin Ɗaiɗaiku wato "Personal Income Tax" wanda kuma ƴan kasuwa da masu ƙananan masana'antu ke biya ta hanyar zuwa su zauna da jami'an hukumar tattara haraji domin bayar da bahasi.
Masu biyan wannan haraji kan biya harajin ne a ƙarshen shekara bayan yin la'akari da ribar da uwar jarinsu ta samar musu.
Sai dai kuma bankunan da suke hada-hada a ciki na da damar sanar da hukumar tattara harajin irin hada-hadar da daiɗaikuwar ke yi wadda ta kai naira miliyan 25 ko naira miliyan 50 ga kamfanoni.
- Harajin ma'aikata - "PAYE"
Shi ma wannan haraji ne da ɗaiɗaikuwar jama'a da suke biya musamman ma'aikata waɗanda suke ɗaukar albashi.
A wannan tsarin na biyan haraji da ake kira da biyan haraji daidai samu ko kuma "PAYE", ana cire wa ma'aikata harajin ne a kowane wata kuma daga tushe.
Misali, wasu ma'aikatun da ba na gwamnati ba suna mu'amila da manyan kamfanoni ko kuma ƙwararru kan haraji da kan cire kuɗaden harajin tun daga tushe. Saboda haka shi ma'aikaci ana cire harajin nasa daga tushe kamar yadda ake yanke kuɗin fansho da na lamunin gida.
Me zai faru da kuɗaɗen jama'a a asusun banki?
Wannan tambaya ce da ke zuciya da laɓɓan mafi yawan ƴan Najeriya inda ake ta zulumi cewa idan aka fara aiwatar da sabon harajin to bankuna za su rinƙa cire haraji daga asusun mutane.
Wannan ba gaskiya ba ne - babu ruwan banki da kuɗaɗenku da ke hannunsu walau dai a ajiye a cikin asusu ko kuma masu shige da fice.
Rawar da banki kan taka ita ce kawai su rinƙa sanar da hukumar tattara haraji dangane da shige da ficen kuɗin da suka kai miliyan 25 ko 50 a duk watanni uku.
Harajin da bankuna za su cire
Bisa wannan sabuwar doka ta haraji, bankuna suna da damar cire haraji na naira 50 a duk hada-hadar da ta kai naira 10,000 zuwa sama, wato kuɗin da aka tura ko kuma a karɓa.
Wannan bayani ma na cikin wasiƙun da bankunan suka aikewa da abokan hulɗarsu tun kafin ranar 1 ga watan na Janairun 2026.
Wannan tsarin ba zai shafi kuɗin albashin mutum da ke shiga asusun bankinsa ba da kuma kuɗin da aka tura daga banki iri ɗaya.
A baya dai, wanda aka tura wa kudi ne kaɗai ake cirewa wannan harajin, amma yanzu tsarin zai shafi wanda ya tura kuɗin ma.
Bankunan sun fayyace cewa wannan haraji ya banbanta da kuɗin da bankuna ke cirewa da aka saba gani ba kuma ake aike wa mutum da saƙo a lokacin da yake tura kuɗi.










