'Tinubu ya gaza wajen kare hakkin Dan’Adam a Nijeriya'

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Kungiyar kare hakkin bil'Adama ta Amnesty International ta bayyana damuwa a kan yadda shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya gaza, wajen bin matakan kare hakkokin bil'Adama a kasar cikin watanni shida da hawansa kan karagar mulki.

Wannan korafi dai yana kunshe ne a wata takarda da Amnesty ta gabatar wa gwamnatin Najeriyar, bayan wani rahoto da ta fitar.

A cikin rahoton ta yi tsokaci game da batutuwan kare hakkin bil'Adama da aka yi biris da su, da kuma shawarwarin abin da ya kamata a yi.

Daraktan kungiyar ta Amnesty International a Najeriya, Isa Sanusi ya shaida wa BBC cewa sun gabatarwar gwamnatin Najeriya da takardar ce domin su yi amfani da ita

“ Wata takadace mu ka gabatar wa gwamnatin Najeriya domin ta yi amfani da ita kuma ya bata manuniya ko matashiya dangane da yadda za’a yi a magance matsaloli na hakkin dan 'Adam da hakkin jama’a da take hakkin bil’ Adama wadanda sun yi katutu a cikin kasar”, in ji shi.

Kungiyar Amnesty International ta ce ta bada shawarar gudanar da bincike kan abubuwan da aka yi a baya na kashe- kashen mutane da na zalinci .

Ta ce ta yi wannan kiran ne saboda a duk lokacin da sabuwar gwamnati ta zo a Najeriya ta kan manta da abin da ya faru a baya musaman ma idan ba ta da wani ra’ayi na siyasa kuma idan abu ne da ya shafi’ ‘talaka ko marasa karfi’

“ Misali manoma da suke kauyuka da wasu jihohi irinsu Zamfara , Katsina da Sokoto wadanda an yi mu su kisan gila, an yi wa matansa da 'yayansu fyade mun ce a tabbatar da cewa an bi kaddin kowace matsala, an yi bincike an gano su waye ne suka yi wannan laifin"

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Manufarmu ita ce a tabbatar cewa an yi adalci tare da tabbatar da cewa ba bu wani da yake rayuwa a doron kasa wanda yana ji yana gani an fi karfinsa an zalince shi kuma rasa yadda zai yi " in ji shi.

Kungiyar ta Amnesty International ta ce gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gaza wajan kula da wadannan batutuwa na kare hakkin bil’Adama a cikin watannin 6 da ta yi kan mulki.

Sai dai wannan ya sa wasu na ganin cewa Amnesty International ta yi hanzari wajan bayyana gwamnatin Tinubu a matsayin wadda ta gaza

"Ba mu yi gajen hakuri ba domin wata shida ya isa a gane inda gwamnati ta dosa. Da za mu fidda wannan rahoto ne wata daya bayan kafa gwamnati, toh wata shida ina ganin akwai adalci saboda ko wannan makon an bayar da rahoto a wani kauyen Zamfara an kwashe mutane 100" in ji shi

Yankin Arewa maso yammacin Najeriya musaman jihohin Zamfara da Katsian da wasu sassan jihar Kaduna na ci gaba da fuskantar barazana da ga yan bindiga ko 'yan fashin daji duk da ikirarin da mahukunan kasar suke yi a kan cewa sun karya lagwonsu