‘Na biya kimanin naira miliyan 30 don kare 'yata daga babanta mai lalata yara'

Zanen wata uwa da 'yarta

Lokacin da aka ɗaure mahaifin 'yarta saboda lalata da ƙananan yara, Bethan ta sha mamaki da jin cewa yana haɗuwa da 'yar tata bayan an sako shi daga . Wannan ne haɗarin da take ƙoƙarin guje wa.

A wajen kotun Cardiff, wata mace ce ke zaune tana jira cikin zaƙuwa. Bethan ba ta taɓa shiga kotun sauraron ƙararrakin zamantakewa ba a baya, amma yanzu ta zo don kare haƙƙin 'yarta - wadda aka ɗaure mahaifinta saboda laifin cin zarafi ta hanyar lalata.

Lokacin da aka yanke masa hukunci a watannin da suka wuce, an ba shi umarnin nisantar 'ya'yansa - amma hakan bai hana shi bibiyar yarinyar ba.

Shi da Bethan sun yi aure lokacin da aka haifi yarinyar, sabaoda haka shi ne ke riƙe da ikon kula da ita, inda yake da damar saka baki kan lafiyarta, da iliminta, da kuma inda za ta zauna.

Bethan "na cikin damuwa" game da abin da zai faru idan aka sako shi daga gidan yari. Tana fargabar zai iya cire yarinyar daga makaranta ba tare da saninta ba, kuma idan hakan ta faru dole sai an bi ta hannun kotu.

"Mutum ba zai taɓa yafe wa kan sa ba," in ji ta.

Bisa taimakon iyayenta, Bethan ta nemi kotu ta janye haƙƙin kula da 'yarta daga hannun tsohon mijin nata kuma ta hana shi ganinta kwatakwata - har ta shafukan sada zumunta - har sai ta kai shekara 18.

Duk da ƙazantar abin da tsohon mijin nata ya aikata, an faɗa wa Bethan cewa lamarin ba sauƙi ba ne. Ta ce mutum ne "mai wayau" kuma ta yi fargabar zai iya shawo kan kotun cewa ya tuba.

Ba ta alfarmar samun tallafi a ɓangaren shari'a, kuma tun kafin zaman farko, tuni har kuɗin lauya ya fara taruwa a kanta.

Ba don kwanan nan ba, ana sauraron irin waɗannan ƙararraki ne a ɓoye, kuma ba a bai wa 'yan jarida damar ɗaukar rahoto a kansu.

BBC ta bi sawun shari'ar Bethan tsawon wata shida da suka gabata.

A kotun, Bethan ta zauna a bayan wani katako saboda kar a dinga hangenta. Mahaifin 'yar tata - wanda ba shi da lauya - ya bayyana ne ta bidiyo daga gidan yari.

Tsohon mijin nata ya faɗa wa kotu cewa ya mainta cewa an kulle shi ne saboda laifukan da ya aikata "masu girma ne", kuma ya ce ya zo ne kawai saboda 'yarsa idan tana so ta ci gaba da hulɗa da shi.

Ya yi ta rubuta mata wasiƙu duk mako, amma daga baya dole ya haƙura - saboda zaman gidan yari.

Ita dai Bethan abu ne mai "wuyar gaske" sauraron sa ko kuma "shiryawa da mutumin da ya jefa cikin uƙuba".

Zanen wata uwa da 'yarta
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

'Yar Bethan na cikin yara 80,000 da tsinci kan su a gaban kotu.

"Ko da a ce mutum yana gidan yari saboda lalata da yara, zai ci gaba da riƙe matsayinsa na uwa ko uba," in wata ma'aikaciyar kula da yara - tana mai bayyana Bethan a matsayin "mai juriya" saboda halin da take ciki.

Ma'aikaciyar ta ci gaba da zama da Bethan da kuma 'yarta, tare da kai wa mahaifin yarinyar ziyara a gidan yari.

Ana ci gaba da shari'ar cikin sauri, kuma Bethan ta koma kotun Cardiff wata uku bayan haka.

Rahoton da ma'aikaciyar al'ummar ta fitar ya soki ɗabi'un tsohon mijin Bethan. Ya fashe da kuka yana cewa "ba zai iya zama mahaifin da 'yarsa take buri ba", kafin daga baya ya gaode wa kotun.

Ya yi fatan za a sake duba lamarinsa bayan an sake shi, kuma ya buƙaci a dinga ba shi rahoton shekara-shekara game da halin da 'yar tasa ke ciki.

Bethan ba ta son ko da irin wannan haɗuwar da ba ta kai-tsaye ba. Lokacin da lauyanta ya soki rahoton da ya nemi a ba shi duk shekara, mahaifin 'yar tata ya nuna ɓacin ransa.

"Zai yi matuƙar daraja a wajena," in ji shi.

Yayin da ake ci gaba da shari'ar, kuɗin biyan lauya na ƙaruwa. Don tallafa mata, iyayenta sun tsawaita lokacin biyan kuɗin gidansu da suke ciki - burinsu kawai shi ne kare iyalinsu.

"Ina tausaya wa mutanen da ba su da damar samo irin wannan kuɗin," in ji mahaifin Bethan. "Suna cikin mummunan yanayi."

Zanen wata uwa da 'yarta

Alƙalin kotun ya ba da taƙaitaccen bayani kan abin da rahoton ma'aikaciyar al'umma ya ƙunsa. Bethan ta ji "daɗi sosai" saboda an amince 'yarta ta dinga zama tare da ita a kodayushe, yayin da kuma aka karɓe haƙƙin kula da ita daga hannun tsohon mijin nata.

Mutum ne "mai haɗarin gaske", in ji alƙalin, kuma ya yi watsi da buƙatar ba shi rahoto kan 'yar tasa.

Kazalika, alƙalin ya yarda da buƙatar tsaurara hanyoyin neman sauya hukuncin kula da yarinyar da uban nata zai iya nema idan ya gama zaman gidan yari.

Za a faɗa masa idan 'yarsa ba ta da lafiya, ko kuma idan sun koma wata ƙasa - amma ba wai inda suke ba.

"Na gode dai kawai," in ji Bethan.

Su ma iyayen Bethan sun ɗan ji sa'ida.

"KAron farko cikin shekara uku, sun bai wa 'yata 'yancin yi wa 'yarta tarbiyya cikin yanayin da ya dace, cikin farin ciki," a cewar mahaifiyar Bethan.

Ban da jimurin kawo lamarin gaban kotu, shari'ar ta jawo musu kashe mai yawan gaske - sun kashe fiye da fan 30,000.

Dangin na ganin sauran iyalan da suka samu kan su cikin irin wannan matsalar za su iya kauce wa kashe kuɗi kamar haka idan aka sauya dokar zuwa yadda za a ƙwace haƙƙin kula da yaro daga hannun uwa ko uwa da zarar an ɗaure su kan laifin lalata da yara.

Bethan da iyayenta sun yi imanin cewa kasancewar 'yan jarida a kotun bisa sabon tsarin adalci ya amfane su, kuma zai ci gaba da taimakon wasu nan gaba.

Bethan ta ce yanzu 'yarta za ta "yi yarinta kamar kowa, cikin kwanciyar hankali".

Kuma wata rana, in ji Bethan, za ta bai wa 'ya'yanta labarin mahaifinta - cikin natsuwa da tunani - idan ta girma.

And one day, Bethan says, she will tell her child about their father - sensitively and carefully - when she is old enough.

Wannan labarin ya yi amfani da sunan Betham ne, wanda ba na gaskiya ba ne, don kare rayuwar matar.