Sabuwar shekara- sabuwar rayuwa, abin da ya sa na hakura da kwankwaɗar barasa

..

Asalin hoton, Thinkstock

"Sabuwar Shekara, Kuma ni ma Sabo", haka suke cewa.

Ga wasu da dama, ranar 1 ga watan Janairu rana ce ta yi wa kai alƙawura na kyautata lafiya, taka-tsantsan wajen kashe kuɗaɗe da sa ran tsara rayuwa ta gaba.

An yi imanin miliyoyin jama'a suna cikin wannan busasshen Janairu a wannan shekarar,.

Gangamin lafiya na bainar jama'a da ake yi wa laƙabi da 'Alcohol Change UK' (Gangamin yaki da shan barasa a Birtaniya) ya soma ɓulla a shekarar 2013.

Masu shirya gangamin sun ce yin wata guda ba tare da an kusanci barasa ba, yana iya taimaka wa mutum samun lafiyayyen bacci, da ƙara kuzari da taimaka wa lafiyar kwakwalwa.

A daidai lokacin da mutane da dama za su yi bikin marhabin da watan Fabrairu ta hanyar sake ɗaga ƙwalabe ko kwalbar barasa, akwai kuma yawan mutane da ke ƙaruwa da suka sake tunani a kan wannan ɗabi`a ta hanyar rage kwankwaɗar barasa matuka gaya tsawon shekarar.

Emma Bricknell, mai shekara 45, asalinta daga Landan ta fito, ta sauya matsuguni zuwa Arewacin Ireland shekaru 18 da suka gabata.

Ta daina shan barasa tsawon wata 8 a watan Mayu na 2021, sakamakon abin da ta kwatanta da “mafi munin buguwar da ta taɓa yi da giya a rayuwarta” kuma a yanzun take tafiyar da rayuwarta yawanci cikin nadamar abin da ta aikata a baya.

`Na fi kazar-kazar a yanzu`

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

“Ban daɗe da daina shan giya ba, kuma ban sake waiwayarta ta ba, ba na shanta,” kamar yadda ta bayyana.

“Ina fita ba tare da na sha ba, na tsarkake rayuwata zuwa ga yadda ya dace. Ina matukar kaunar hakan, na fi da kazar-kazar, ba na tsoro ko ɗari-ɗari da kowa a yanzun.

“Alaƙata – wasu sun kyautatu, wasu mutanen na yanke hulɗa da su – na fi ganin hasken lamurana yanzu kuma na gane ya kamata in ja da baya.”

 Sai dai Emma ta ce ta tsinci kanta cikin yanayi da wasu suke matsa-mata lamba ta shiga sahunsu, kuma tana jin cewa ƙaurace musu da ta yi, ta jefa su cikin tsoro da rashin tsaro “kamar yadda yake nunawa a shan barasarsu”

Emma ta ce ta ci gajiyar alfanun hakurar da ta yi da shan barasa.

Ms Bricknell tana tunanin mutanen Arewacin Ireland suna da wata dangantaka da ta shafi barasa idan aka kwatanta da mutane da suke sauran ƙasashe.

“A wajena, gangamin abu ne mai matuƙar kyau, sai dai ina ganin ya kamata Arewacin Ireland ta kalli gaba ɗaya, yadda muke sabga da barasa,” in ji ta

“Ban taɓa ganin mutanen da suke ɗirkar barasa a wajen binne gawa irin su ba. Raɗin suna barasa, bukukuwan aure barasa''.

“Akwai ainihin dangantaka mara tsafta ga lamarin nan, akwai kuma ƙaton hoto a game da yadda ka karya lamarin a Arewacin Ireland.”

Masu shirya gangamin sun yi gargaɗin cewa ƙauracewa gaba ɗaya, tana iya zama matsala ga waɗanda suka dogara da barasa.

A 2022 wani rahoto na Stormot yana cewa illa ko lahanin da amfani da ƙwayoyi da barasa ke hadasawa a Arewacin Ireland “sun yi tasiri kuma suna iya ƙara tabarbarewa”

A sassan Birtaniya, akwai adadin mutane da suka mutu sakamakon barasa a 2021, inda Arewacin Ireland ta zama ta biyu, kamar yadda Ofishin ƙididdiga na ƙasa ya yi bayani.

Bayanan da Hukumar Kididdiga Da Bincike ta Arewacin Ireland ta tattara, sun nuna mutane 350 daga 17,558 da aka yi rajistar mutuwarsu a 2021, sun mutu ne saboda wasu dalilai na barasa.

Karin kashi 53.9 a yawan adadin da aka samu shekara 10 baya.

'Ba na bukatar barasa domin jin daɗin rayuwata'

..

Asalin hoton, Emma Bricknell

Mal Byrne daga ƙungiyar East, kungiyar taimako wadda take aiki da mutanen da suke tafiyar da batutuwa na amfanin kwayoyi da barasa, ta ce duk wanda yake son rage matsalar barasa, ciki har da rage kwankwaɗarta matuƙa gaya, to ya nemi shawara ta ƙwararru ko likitoci kafin ya fara.

“Dogaro da barasa, yana iya shafar lafiyar jiki da ta ƙwaƙwalwa, kuma ba kamar ɓacewar wasu alamomi na shan wasu miyagun abubuwa ba, janyewa daga shan barasa, tana iya haddasa gagarumar rashin lafiya a jikin mutum.”

Mista Byrne ya ce suna amfani da wata dabara ta mayar da hankali a kan mutum na tsawon lokaci “maimakon kaurace wa amfani da barasar gaba ɗaya”

Robert Boyd, mai shekaru 38, daga Londonderry, ya ce ya rage shaye-shayensa bayan kammala jami`a, da ya gane cewa kwankwaɗar barasa ba abu ne mai ɗorewa ba, musamman ga mutumin da ke aikin kwana.

''Na gaya wa abokaina na daina shan barasa, saboda ba zan iya zuwa wajen aiki cikin maye ina ta warin giya ba''.

Robert ya ce rikicewar tsadar rayuwa, na nufin mutane sun fi fahimta idan abokansu ba su iya fita yawo da daddare ba.

Kodayake Mista Boyd ya zaɓi kada ya sha barasa a kai a kai, ya ce yana ganin “ana ta holewa cikin dare kuma a matsayinsa na jigo dole na sha barasa”.

“A da, da an yi maka dariya ko shegantaka ƙin halarta ko ƙin gayyatarka yawon dare ko shagulgula, amma a yanzun bana tunanin haka lamarin yake,” kamar yadda ya bayyana.

“Bugu da kari, matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita a yanzun, da tsadar kayan shaye-shaye idan an fita, mutane sun soma fahimta idan abokai ba su fita yawon dare ba.