Yaƙin Tigray: Ana zargin sojojin Eritrea da yi wa mata fyaɗe duk da yarjejeniyar zaman lafiya

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata da kungiyoyin ba da agaji sun ce ana ci gaba da cin zarafin mata duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a yaƙin basasar Habasha

Gwamnatin Habasha ta saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da dakarun Tigray da ke arewacin ƙasar a watan Nuwamban bara, a wani mataki na kawo ƙarshen yaƙin basasar da aka shafe shekaru biyu ana fafatawa.

Sai dai, kungiyoyin ba da agaji da mazauna yankin, sun faɗa wa BBC cewa ana ci gaba da far wa fararen hula - musamman ma cin zarafin mata.

Wannan labari na ɗauke da abubuwan da za su tayar da hankalin masu karatu wanda ya haɗa da cin zarafin mata.

A ranar da gwamnatin Habasha ta sha hannu da abokan adawarsu daga yankin Tigray don cimma yarjejeniyar zaman lafiya – dukkan bangarori na cikin annashuwa – Letay kuwa ta shafe tsawon daren ɓoye a karkashin gada, inda take jin yadda ƙarar harbin makamai a kusa da ita.

Ita ce kaɗai daga yankin arewa maso gabashin Tigray da ta tsira daga fyaɗe da sojojin Eriteria ke yi wa mata.

"Bayan faruwar lamarin, na yi wata dogon tsuma kafin na dawo cikin hayyacina. Na ɓoye kaina har sai da sojojin suka tafi.’’

Mun sauya sunan Letay da wasu waɗanda aka yi wa fyaɗe da suka faɗa wa BBC labaransu, don kare su daga tsangwama da ɗaukar fansa.

A cikin shekara biyu da aka ɗauka ana yaƙi a arewacin Habasha, kungiyoyi da dama da suka haɗa da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin ƙare hakkin ɗan adam da kuma ‘yan jarida, sun ɗauki bayanai na yadda sojojin Eriteria da ƙawayensu da kuma mayaƙa suke yi wa mata fyaɗe.

An kuma zargi dakaru daga Tigray da yi wa mata fyaɗe a yankin Amhara a kokari da suke yi na dannawa zuwa babban birnin ƙasar.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ana tsammanin cewa dubban ɗaruruwan mutane ne suka mutu a yaƙin
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Cikin shekara biyu, daga watan Nuwamban 2020, bangarorin biyu sun yi faɗa don samun iko da Tigray. Ana tsammanin cewa dubban ɗaruruwan mutane ne suka mutu a yaƙin.

An yi fatan cewa bayan yarjejeniyar zaman lafiyar da aka sakawa hannu a watan Nuwamba, hakan zai sa a dakatar da cin zarafi da ake yi wa mutane.

Sai dai, mata da ma’aikatan lafiya da kuma kungiyoyin ba da agaji sun faɗa wa BBC cewa ba a dakatar da cin zarafin mata ba.

Na yi magana da Letay ta wayar tarho – saboda gwamnati ba ta bai wa ‘yan jarida damar zuwa yankin Tigray ba.

"Hakan ya faru da ni sau biyu. Laifin me na yi? Kamar ni na yi wa kaina fatan haka.’’

Letay ta ce sojojin Eriteria biyu sun yi mata fyaɗe kafin watan Janairun 2021 – inda na soja na ukun yaki yin abin da saura suka aikata.

"Biyu daga cikinsu sun yi abin da suke so kafin su tambayi na ukun cewa shi ma ya yi, amma ya ce a’a. Ya ce: ‘Me zan yi da ita? Gawa ce a kwance.”

Bayan yi mata fyaɗe a karon farko, Letay ta nemi agajin lafiya da taimakon lafiyar kwakwalwa, inda ta shiga cikin kungiyoyin mata da ke goyon bayan waɗanda aka yi wa fyaɗe.

A ranar da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiyar, Letay ta fita domin taimakon wata yarinya da aka yi wa fyaɗe, kafin ita ma ibtila’in ya faɗa mata.

Abin na da matukar wahala wajen gano ainihin waɗanda aka yi wa fyaɗe a yaƙin na Tigray.

Waɗanda aka yi wa fyaɗen na tsoron fitowa su yi magana a daidai lokaci kuma da aka katse hanyoyin sadarwa lokacin da ake gwabza faɗa.

A cewar alkaluma daga hukumar lafiya a yankin Tigray, ta ce bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya a watan Nuwamba da Disamba – an samu rahotannin yi wa mata 852 fyaɗe a sansanonin da aka kafa domin taimakon waɗanda aka yi wa fyaɗen.

Kungiyoyin ƙare hakkin ɗan adam da na bayar da agaji da ke aiki a Tigray, sun ci gaba da ɗaukar bayanai na waɗanda aka ci wa zarafi.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kungiyoyi da dama sun kafa sansanoni don taimakon waɗanda aka yi wa fyaɗe a yaƙin

Adiama, wadda ta fito daga garin Zalambesa a arewacin Tigray, ta ce wani sojan Eritrea ya ci zarafinta a karshen watan da ya gabata.

"Su huɗu ne amma soja ɗaya ne ya yi min fyaɗe. Sun yi niyyar kashe ni, amma sai suka yi tafiyarsu bayan aikata min fyaɗe.’’

Ita ma Mulu Mesfin, wadda ta yi aiki da waɗanda aka yi wa fyaɗe a babban asibitin Tigray da ke Mekelle tun fara yaƙin, ta aiko min da sakon murya a lokacin da take tafiya cikin asibitin.

"Akwai waɗanda aka yi fyaɗe da dama a wajen da nake. Sun fito ne daga yankuna daban-daban na Tigray. Yawancinsu an yi musu fyaɗe ne a cikin wata ɗaya ko biyu da ya wuce.”

A cewar Mulu, da wasu jami’an lafiya da muka tattauna da su, sun ce sojojin Eritrea ne suka aikata yawancin laifukan cin zarafin, yayin da kuma ake zargin mayaƙa daga yankin Amhara da dakarun gwamnati da laifin aikata fyaɗe.

Eritrea na raba iyaka ne da Tigray, kuma suna da daɗaɗɗen gaba tare da dakarun yankin TPLF – wani abu da ya sa suke goyon bayan gwamnatin Habasha a yaƙin.

A mako da ya gabata, aka ga shugaban ƙasar Eriteria Isaias Afwerki, a bainar jama’a lokacin da ya kai ziyara Kenya, wanda abu ne da ba a saba gani ba.

Mista Isaias, wanda ya fito daga ƙasar da babu takamaimen ‘yancin ‘yan jarida, ya fusata lokacin da ‘yan jarida suka yi masa wasu tambayoyi. Ya yi watsi da dukkan zargin da ake yi wa sojojin ƙasar na aikata fyaɗe fyaɗe a yankin Tigray.

"Kowa na magana kan laifukan take hakkin ɗan adam da ake zargin sojojin Eritrea na aikata fyaɗe da ɗebe dukiyar jama’a, wannan shaci faɗi ne kawai na wasu mutane da yaɗa karya,’’ in ji shi.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaba Isaias Afwerki ya musanta dukkan zargin take 'yancin ɗan adam da ake yi wa dakarun Eritrea

Mun aike da dukkan zarge-zarge da ke cikin wannan rahoto zuwa ga ministan sadarwa na gwamnatin Habasha da kuma kungiyar Haɗin Kan Afirka da suka jagoranci cimma yarjejeniyar zaman lafiya, domin ji daga garesu, sai dai, basu ce uffan ba.

Yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a watan Nuwamba ta kawo canji mai kyau a yankin Tigray. Babu wani sauran faɗa. Ana kuma kai kayan agaji da suka haɗa da abinci da kuma magani zuwa birane da garuruwa, yayin da layukan sadarwa da bankuna ma suka dawo aiki.

Wasu iyalai sun sake haɗuwa da ‘yan uwansu, inda wasu suka yi magana da juna a karon farko cikin sama da shekara ɗaya. Sai dai, a cewar wani bangare na huɗu na yarjejeniyar: “bangarorin da ke faɗa, ya kamata su yi Alla-wadai da batun cin zarafi da kuma musgunawa mata.”

"Cin zarafi na nufin saɓawa yarjejeniyar ne,’’ in ji Laetitia Bader, darektar kungiyar ƙare hakkin ɗan adam a yankin kusurwar gabashin Afirka. “Wani batu da muke ta magana a kai shi ne muhimmancin ganin waɗanda ke goyon bayan yarjejeniyar su tabbatar da cewa sun fito sun yi magana idan aka samu laifin cin zarafi.”

Kungiyar ta HRW ta ci gaba da yin kira na ganin an bai wa masu bincike masu zaman kansu da ‘yan jarida damar shiga arewacin Habasha.

"Muna nuna damuwa game da ƙoƙarin gwamnatin Habasha na kawo karshen ayyukan kungiyoyin kare hakkin ɗan adam na ƙasa da ƙasa a Habasha, wanda kwamitin Geneza ya kafa,’’ in ji darektar.

Bader ta ce bincike zai yi tasiri in har za a bi wa mutane hakkinsu da kuma yin zaman sulhu.

"Ban taɓa tsammanin za a ci zarafina ba bayan yarjejeniyar zaman lafiya,’’ in ji Hilina.

Matar mai ‘ya’ya uku ta riga da ta tsere daga gidanta da ke Humera zuwa garin Shirao, inda ta yi aiki a matsayin mai sayar da masara a bakin titi.

Ta ce a ranar 16 ga watan Nuwamba, tana komawa gida da yammaci, sai sojojin Eritrea biyu suka tsayar da ita saboda laifin karya dokar takaita zirga-zirga. Ta faɗa musu cewa bata da wata shaida, inda daga nan suka tafi da ita zuwa wani gidan da babu mutane.

Hotunan tauraron ɗan adam da aka ɗauka a ranar 26 ga watan Satumba da kuma kamfanin fasaha na Maxar suka fitar, ya nuna wasu kamar sojojin Eritrea ko kuma na Habasha a garin Shiraro.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An ɗauki shekara biyu ana yaƙin, amma an ɓoye shi ga idon duniya, inda aka yanke hanyoyin sadarwa da kuma takaita shigar mutane zuwa yankin

Hilina ta ce daga irin shiga da kuma harshen da suke magana da shi, ya nuna sun fito daga Eritrea.

"Sun kawo zuwa wani gidan da babu mutane. Sun nuna min bindiga: idan kika yi shiru, ba za mu cutar da ke ba. ‘Don haka, na faɗa musu cewa za su iya yin abin da suke so, amma kada su kasheni.’’

Hilina ta ce an yi mata fyaɗe tsawo daren kafin su barta ta tafi da safe. Tuni kuma ta zubar da cikin da ta samu, inda ta ce ta gwammace ta mutu a kan da ta haifi yaron da ta samu ta hanyar fyaɗe.

A cewar jami’an ba da agaji da BBC ta tattauna da su, sun ce akwai sojojin Eritrea a kusa da garin Shiraro.

Yarjejeniyar zaman lafiyan na son sojojin su bar Tigray, duk da cewa sun fice daga muhimman birane da garuruwa, akwai wasu a wuraren da ke kusa da iyaƙa da Tigray.

Shashu, wata mata mai shekara 80, ta ɓarke da kuka lokacin da muke magana da ita – a kan wayar tarho. Mun tambayeta ko za ta iya ci gaba da tattaunawar sannan ta amince.

Kamar Letay, ita ma Shashu an yi mata fyaɗe har sau biyu – kafin da kuma bayan yarjejeniyar zaman lafiya.

Ta ce irin cin zarafin da maza suka yi mata a wata Nuwamba, har ta kai yanzu bata iya rike fitsari da kuma zama a kan kujera.

"Mutum biyu zuwa uku a kan mutum ɗaya, na ɗimauta sosai. Ya zamanto kamar babu wani sauran abu mai kyau a jikina.’’