Ana korafi kan rufe rajistar Ƴan Nijar mazauna ƙasashen waje da ke zaune a Najeriya

An rufe gudanar da yin rajistar ƴan Jamhuriyyar Nijar mazauna ƙasashen waje da ke zaune Najeriya a yammacin Asabar bayan cikar wa’adin kwanaki goma sha huɗu da hukumar zaɓen ta ƙayyade.
Ana yin rajistar ne game da zaben cike gurbi na yan majalasar dokokin kasar da za su wakilci ‘yan Nijar mazauna kasashen waje a majalisar dokokin kasar.
Babban birnin tarrayar Najeriya Abuja na daga cikin wuraren da ake rajistar.
To sai dai wasu wuraren kamar Jihar Legas za a ci gaba da yin rajistar a ranar Lahadi da Litinin saboda tsaikon da aka samu na kai kayan yin rajistar a wuraren.
Sakamakon cikar wa’adin yin wannan rajista, jama’a da dama sun yi cirko-cirko a gaban ofishin jakadancin Nijar a Abuja inda suke ta yin ƙorafi kan rashin samun yin rajistar.
Ɗaya daga cikin waɗanda ba ta samu yin rajistar ba ta shaida wa BBC cewa kwanan ta huɗu ita da ƴan uwanta suna bin layi amma ba su samu rajistar ba.
Salisu Al-Hussain, wanda ɗan siyasa ne a Nijar kuma ya halarci wurin yin rajistar, ya roki hukumar zaɓe ta Nijar wato CENI da ta ƙara musu lokaci.
“Mu a wurinmu babu zancen kammalawa, sai dai a ce ranar da aka saka ta ƙare, domin mutanenmu ma rabi ba a yi musu ba.
“Mu yanzu zance a ƙara mana lokaci ne, don kwana 15 da aka ba mu ba su ishe mu ba , muna bukatar karin 15 ko da rabin mutanen mu ne mu samu mu yi musu," in ji Salisu Al-Hussain.
Shi ma Alhaji Abubakar Khalid wanda shi ne shugaban ƙungiyar ƴan Nijar mazauna ƙasashen waje reshen Najeriya ya ce ya gamsu da wannan rajista, amma a cewarsa akwai wasu kurakurai.
"Yawancin mutanen mu takardu ne ba su da su, ka haifi ƴaƴanka a nan, kai ɗan Nijar matarka ƴar Nijar ce ƴaƴan kuma sunan ƴan Nijar ne kuma ba ka yi musu ba.
"Irin wannan idan ya taso sai kai yi ta faɗa ka ce sai an yi wa ƴaƴanka rajista saboda su ma ƴan Nijar ne ," in ji Alhaji Abubakar.











