Dalilan da suka sa wasu ƴan Najeriya ba za su je Umara a lokacin azumi ba

Asalin hoton, Getty Images
Umarah na ɗaya daga cikin ibadu mafiya tarin lada da al'ummar Musulmai ke yi domin samun gwaggwaɓan ladan da ke tattare da yin ta musamman a watan Ramadan.
Adadin masu zuwa Umrah a lokacin watan Ramadan galibi ya kan fi na sauran lokuta saboda kwaɗayin dacewa da tarin ladan da ke tattare da yin ibadar a cikin watan na azumi.
Miliyoyin musulmi ne daga ƙasashe da dama na duniya ke zuwa yin umarah a irin wannan lokaci na azumin Ramadan.
Sai dai da alama a wannan shekarar, wasu maniyyatan da ke son yin wannan muhimmiyar ibada sun gamu da cikas sakamakon rahotannin da ke cewa hukumomin Saudiyya suna jan ƙafa wajen bayar da biza.
Lamarin ya shafi maniyyata da dama daga wasu ƙasashen duniya har da Najeriya.
Baya ga maniyyatan, su kan su masu kamfanonin jigilar sun ce matakin ya shafi harkokinsu kasancewar abokanan hulɗarsu da dama ba su samu biza ba.
Me ya sa Saudiyya ta daina bayar da biza?
Bayanan da BBC ta samu daga wasu kamfanonin jigilar alhazai zuwa umara sun alaƙanta matakin na Saudiyya da ƙoƙarin rage yawan mutanen da ke ƙasar domin bai wa wasu damar yin ibadar kasancewar akwai mutanen da suka je umara da dama da suka maƙale a ƙasar ba tare da sun koma ƙasarsu ba.
Usman Ambursa, shugaban kamfanonin maniyyata Hajji da Umarah a Abuja, ya ce matsalar ta samo asali ne daga yadda Saudiyya ta sauya tsarin bayar da biza daga wata ɗaya zuwa uku.
Ya ce "Saudiyya na da tsarin bayar da biza, da duk shekarun baya, suna bayar da biza mai tsawon kwana 30, sai suka fito da tsarin bayar da biza mai tsawon kwana 90 wato wata uku kenan."
"Ka san yadda halayyarmu ta ƴan Najeriya take, muna son amfani da kowace dama gare mu, sai suka yi biza suka jira sai lokacin Ramadan [su je], da suka ga haka, sai suka dakatar." in ji shi.
Wasu kamfanonin jigilar sun ce akwai mutanen da tun farko ake yi masu biza domin yin umarah amma sai yi jinkirin tafiya ko kuma da zarar sun je Saudiyyar sai su maƙale su ƙi komawa ƙasarsu har ma wasu su jira lokacin aikin hajji domin su sauke ibadar ta farilla.
Yadda matsalar ta shafi masu kamfanin jigila
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Aliyu Abdullahi Jega, shugaban kamfanin Firdausi Services Limited ya shaida wa BBC cewa suna cikin matsala kasancewar ya kama otal ɗaya da kuɗinsu ya kai na fiye da naira miliyan 200 sannan ya sayi tikiti da dama na abokan hulɗarsa da suka zarce naira miliyan 300.
Ya bayyana cewa "duk wanda ba a samu ba, asara ce a wurinmu." in ji Aliyu Jega.
"Mutum ba zai iya ƙiyasta girman asarar da ya yi ba, asara yanzu ake yin ta, mutum ba zai gane an yi asara ba, sai an rufe tsarin bayar da bizar ta umara." kamar yadda kamfanin ya ce.
A cewarsa, ya shafe sama da mako biyu yana bibiyar bisa kuma har zuwa lokacin rahoton nan, bai samu ba.
Ya ce kamfaninsu na da maniyyata 350 amma cikinsu, 59 ne kaɗai suka samu biza saɓanin bara da suka kai mutum 400 zuwa aikin umarah kuma ba a fuskanci wani cikas ba a lokacin.
Aliyu Jega ya ƙara da cewa suna tattaunawa da hukumar alhazai ta Najeriya domin gano hanyoyin da za a bi domin sauƙaƙa lamarin.
Ita ma, Hajiya Maimuna Dabo ta ce kamfaninsu yana fuskantar ƙalubale wajen samun biza kasancewar a baya, a rana ɗaya suna iya samun biza saɓanin yanzu da suke shafe kamar kwana 12 zuwa 14.
"Idan aka nemi biza ta mutum 10, sai ka ga ta mutum ɗaya ko biyu ne za su samu." in ji ta.
Ta alaƙanta hakan da rashin komawar wasu 'yan ƙasashensu sannan "da yawa an musu biza amma ba su shirya tafiya ba, suka zauna, ya nuna kamar an yi biza kuma ba a tafi ba har ma a ce sun koma ƙasarsu."










