Ko ɗabi'ar neman burgewa ce ke hana mata cigaba a wuraren aiki?

- Marubuci, Megha Mohan
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakiliyar harkokin jinsi
- Lokacin karatu: Minti 5
Faith mai shekara 24 na cikin zauren tattaunawa a ofishinta da ke birnin Nairobi a ƙasar Kenya, amma cikin fargaba. An fara ganawa lafiya ƙalau, har ma tana ta dariya saboda barkwancin da iyayen gidanta ke yi, kwatsam kuma sai abubuwa suka sauya.
Wani abokin aiki da ya fi ta matsayi ya ce Faith na jin cewa kamar ba za ta iya aiki tuƙuru ba. Amma kafin ta mayar da martani sai wani ya ambaci sunanta.
"Kuma Faith ta amince da maganata!" Sauran mambobu suka juya suna kallon Faith yayin da abokin nata ke ci gaba da cewa "ai kin yarda ko Faith?"
Faith ba ta amince ba, amma kuma yanzu tana cikin matsi.
"Ba ni son mutane su yi min kallon mai damuwa ko mai taurin kai," kamar yadda Faith ta faɗa mani. "Na ji kamar ana matsa min domin na yi murmushi, na amince, kuma kada na jawo cecekuce."
Shekara biyu kenan kacal a ɗaya daga cikin manyan kamfanonin da ake yawan neman aiki, kuma ita ce ta farko-farko a danginta da suka yi karatu a jami'a. Saboda tana da abubuwan da take so ta cimma da yawa a rayuwarta.
"Ta yaya zan samu cigaba idan na fara yin sa'insa da abokan aikina tun ina ƙaramar ma'aikaciya?" in ji ta.

Asalin hoton, 10,000 hours/Getty Images
A wannan shekarar, rahoton shekara-shekara na Women in the Workplace 2025 da cibiyar McKinsey ke wallafawa ya faɗaɗa a wannan shekarar, inda ya taɓo Najeriya, da Kenya, da Indiya.
Ya gano cewa akwai gurabe masu yawa da mata ba su samu a sawun shugabanci a wuraren ayyuka.
A Kenya, mata ne suke riƙe da rabin guraben aiki na matakin farko a masana'antu kamar na kiwon lafiya da harkokin kuɗi, amma adadin ya sauka zuwa kashi 26 cikin 10 a matakin shugabanci. Haka abin yake a Najeriya da Indiya.
Faith ba ta musu da abokin aikinta a wannan zaman. Ta yi murmushi kawai ba tare da cewa komai ba.
Yanzu ƙwararru na kiran abin da Faith ta yi da "likeability labour" - wato "neman burgewa".
Mene ne 'likeability labour' (neman burgewa)?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Wannan suna ne mai daɗin ji na wani abu mai maras kyau," a cewar Amy Kean, ƙwararriya a kamfanin sadarwa na Good Shout, wadda ta fito da sunan.
"Yana nufin yawan tuntuntuni, da fargaba, da neman sauya tunani da mata ke yi a kullum domin neman mutane su so su a wurin aiki."
Rahoton mai taken "Shapeshifters: What We Do to Be Liked at Work," ya ce kashi 56 cikin 100 na mata na jin matsi domin su nemi a so su a wurin aiki idan aka kwatanta da kashi 36 kacal na maza.
Bayan bincikar mata 1,000 a Birtaniya, rahoton ya bayyana yadda lamarin ya shiga zukatan mata sosai.
Ya bayyana yadda mata ke jin ya kamata su sassauta muryarsu wajen yin magana hatta a lokacin da su ne suka fi gaskiya. Daga cikin abubuwan da suke faɗa akwai: "Does that make sense?" or "Sorry, just quickly..." - "Hakan ya yi ma'ana?" ko "Afuwa, a gurguje...".
Irin wannan yunƙurin takure kai, in ji Kean, zai iya zama wata hanya ta hana abokan aiki su dinga kallon mace a matsayin mai wuyar sha'ani.
Ga matan da ba su saba kare kan su a wurare ba, lamarin zai wuce maganar su burge a wuraren aiki.

Asalin hoton, Amy Kean
Matsalar ƙasa da ƙasa
Ƙwararru na cewa matsalar matsi da mata ke shiga domin neman a ƙaunace su a wurin aiki ta duniya ce baki ɗaya.
Wani bincike a 2024 da aka yi a Amurka daga kamfanin Textio ya tabbatar da hakan. Bayan nazartar bayanai na mutum 25,000 a kamfanonin 253, ya gano cewa an fi yiwuwar faɗar halin mata idan aka nemi bayanai kan su kuma an siffanta kashi 56 cikin na matan a matsayin waɗanda ba a son ɗabi'unsu wajen bayar da shaida, yayin da maza suka samu kashi 16 kacal.
Sannan an fi sa ran maza su samu shaidar ana ƙaunarsu ninki huɗu sama da mata a wurin aiki.
"Mata kan aikata neman su burge bisa wasu dalilai masu yawa da suka shafi al'adu da zamantakewa," in ji Dr Gladys Nyachieo, wani masanin zamantakewa a jami'ar Multimedia University da ke Kenya.
"Akan yi wa mata kallon masu rainon al'umma, masu saka buƙatun wasu fiye da nasu kuma wannan abin ne yake bin su har wajen aiki," a cewar Dr Nyachieo.
"Akwai abin da ake kiran wannan ɗabi'a a harshen Kiswahili - office mathe - wato uwar mata."
Na tambaya cewa idan har wannan ne abin da mace ke son ta dinga yi a rayuwarta to mece ce matsala.
"Babu wata matsala dangane da shi," kamar yadda Dr Nyachieo. "Amma kuma ba za a biya ki albashi a kan wannan ba. Za a yi ta neman ki yi aikinki, ƙila ma har da ƙari."

Asalin hoton, Gladys Nyachieo
Mafita
Dr Nyachieo na ganin idan ana son daƙile ɗabi'ar neman burgewa a wurin aiki, dole ne sai an gudanr da sauyi mai ɗorewa tun daga tushe, kamar tsara wasu hanyoyi da za su bai wa mata damar yin aiki ba tare da takura ba da kuma sama musu jagorori.
Ita ma da kanta takan horar da matan da ke matakin farko na aiki a Kenya.
"Ina ɗaukar bai wa mata shawara da muhimmanci sosai," in ji ta. "Nakan faɗa musu cewa idan kuka zauna burge mutane ba za ku ci gaba ba. Dole ne ku nuna kan ku da kanku."
Daga cikin waɗanda take horarwa har da Faith.
"Ta koya min yadda zan guje wa jin matsi ta yadda dinga yi wa mutane murmushi kodayaushe. Kuma ina aiki a kan hakan."











