Abin da masana suka fahimta da matakin Tinubu na naɗa masu magana da yawunsa uku

Asalin hoton, X/Sunday Dare
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 5
Masana harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na ganin garambawul da Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi game da ayyukan masu magana da yawun gwamnatinsa a matsayin "sabon salo na yaɗa farfaganda da ba a saba gani ba".
Ƙwararru a fannin sadarwa da aikin jarida da BBC ta yi magana da su sun bayyana mabambantan ra'ayoyi kan hakan, amma dukkansu sun yarda cewa yunƙurin zai iya jawo rashin tsari da rigegeniya wajen fitar da bayanai.
A ranar Talata ne fadar shugaban ƙasar ta bayyana cewa daga yanzu gwamnatin Tinubu ba ta da mai magana da yawunta guda ɗaya tilo, a madadin haka ta sanar da mutum uku da za su dinga yin hakan.
Idan ba a manta ba, a watan Satumban 2024 ne tsohon mai bai wa Tinubu shawara na musamman kan kafofin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ya ajiye aikinsa bisa dalilan jinya da ya ce iyalinsa na fama da ita. Sai dai rahotonni sun ce ya yi hakan ne sakamakon rikicin da ya dinga faruwa tsakaninsa da Bayo Onanuga, abokin aikinsa a a sashen magana da yawun fadar shugaban ƙasar.
Su wane ne maƙogwaron gwamnatin ta Tinubu?
Sanarwar da Bayo Onanuga - mai bai wa Shugaba Tinubu shawara na musamman yaɗa labarai da tsare-tsare - ya fitar ta ce an yi sauye-sauyen ne da zimmar "kyautata aiki".
"Mista Sunday Dare - wanda kafin yanzu shi ne mai bai wa shugaban ƙasar shawara na musamman kan yaɗa labarai da saita ƙasa [Public Communication and National Orientation] - yanzu ya zama mai ba da shawara na musamman kan yaɗa labarai da sadarwa," in ji sanarwar.
"Mista Daniel Bwala - wanda a makon da ya gabata aka bayyana a matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan kafafen yaɗa labarai da sadarwa - yanzu zai riƙe muƙamin mai ba da shawara na musamman kan yaɗa manufofin gwamnati.
"Waɗannan sauye-sauye, tare da muƙamin mai ba da shawara na musamman kan yaɗa labarai da tsare-tsare, na nuna cewa babu wani mutum ɗaya tilo da ke magana da yawun shugaban ƙasa.
"Saboda haka dukkanin mashawartan na musamman uku za su haɗu su zama masu magana da yawun gwamnati."
Sharhi daga Farfesa Farooq Kperogi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Farfesa Farooq Kperogi ɗan Najeriya ne kuma malami a sashen sadarwa na jami'ar Kennesaw State University da ke Amurka. Ga abin da ya shaida wa BBC a rubuce:
Wannan naɗi da Tinubu ya yi, wanda ba a saba gani ba, na masu magana da yawunsa gwamnatinsa uku - baya ga manyan masu taimaka masa na musamman 10 a fannin yaɗa labarai - na nuna halin gwamnatin na fifita farfaganda sama da walwalar al'umma.
A tarihi, shugabannin Najeriya kan yi aiki da ƙaramar tawaga a fannin yaɗa labarai, wanda hakan ke fayyace layin aiki ɗoɗar. Faɗaɗa waɗannan muƙamai da Tinubu ya yi yayin da ake tsaka da matsalolin tattalin arziki na jawo ayar tambaya game da abin da gwamnatinsa ta fi sakawa a gaba.
Gwamnatin da ke neman 'yan ƙasa su nuna sadaukarwa yayin da ake fama da hauhawar farashi, da cire tallafin mai, da matse bakin aljihu, ya kamata a ce ta zama abar koyi. A madadin haka, gwamnatin Tinubu ta fi mayar da hankali kan farfaganda sama da shawo kan matsalolin 'yan Najeriya.
Waɗannan naɗe-naɗe na nuna abu biyu: rashin kwanciyar hankali da rashin tsari. Rashin kwanciyar hankali, saboda gwamnatin da take fargabar gobenta da kuma tsoron farin jininta ce za ta damu da farfaganda sama da magance matsaloli. Rashin tsari, saboda yawan mutanen da aka naɗa zai jawo gwamutsuwar aiki, da aika saƙonni daban-daban, da rikicin cikin gida, da kuma rigegeniya kan manufofi.
Ina ganin, maimakon faɗaɗa sashen sadarwa, kamata ya yi gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali kan rage sharar gwamnati, ta kyautata aikin gwamnati, da kuma cika alƙawurran da ta ɗauka.
Sharhi daga Dr Sule Yau Sule
Dr Sule Yau Sule malami ne a Jami'ar Bayero ta Kano, kuma ƙwararre a fannin hulɗa da jama'a. Ga abin da ya shaida wa BBC:
Da farko dai a ƙa'idar aiki irin wannan, idan ana son ya tafi daidai, dole ne ka tsayar da mutum ɗaya wanda shi ne zai dinga fitar da bayanai.
Tasirin abin shi ne idan ka ce kowanne cikin mutum ukun nan ya yi jawabi, to duk ɗan'adam yana da yadda yake kallo da fahimtar abu, kodayake dai ina kyautata zaton za su zauna su tsara aikin a tsakaninsu.
Idan aka bar abin wannan ya faɗa wannan ya faɗa to za a dinga samun mabambantan bayanai saboda yanayin fuskantar abubuwa na kowane ɗan'adam daban ne.
Hanyar da wannan sauyin zai iya taimakar gwamnatin ita ce, ɓangarorin da a baya ba su samun kula wajen yaɗa labaransu to yanzu za su samu, saboda na san yanzu za a faɗa wa kowa ɓangaren da zai kula da shi.
Amma kuma fa idan aka zo maganar rikici - irin wanda gwamnatin Tinubu ke ciki - idan aka samu wani yanayi na rikici na musamman, dole ne a samu mutum ɗaya da za su saka ya dinga magana shi kaɗai a kansa.
Sharhi daga Mannir Dan-Ali
Kafin ya zama shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya yi gwamnan jihar Legas - babban birnin kasuwancin Najeriya - tsawon shekara takwas a wa'adi biyu.
Ɗanjarida kuma tsohon babban editan jaridar Daily Trust, Mannir Dan-Ali, ya ce:
Da ma can Tinubu ya fi bai wa farfaganda muhimmanci a lokacin da ya yi gwamnan Legas. Shi ya sa ma lokacin da ya yi gwamna, an fi jin maganar ayyukansa ta yadda sai mutum ya ɗauka Legas ta koma Aljanna, alhalin kuma kowa ya san ba haka ba ne.
Ina ganin yanzu haka irin wannan abin ake so a maimaita a tarayyar Najeriya ta yadda ko iska ya ratsa za a yi ta sharhi a kai cewa ƙoƙarin gwamnatinsa ne.
Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa Tinubu bai ɗauki wannan mataki ba shi ne "rashin tsari. Kamar abin da yake faruwa ne a Amurka bayan zaɓen Trump, sai 20 ga watan Janairu zai karɓi mulki amma har ya kusa gama kafa majalisar ministocinsa, saɓanin Tinubu wanda ya daɗe yana sha'awar shugabancin amma sai da ya ɗauki lokaci kafin ya fito da ministocinsa.
Babban abin da ya fi dacewa da Tinubu shi ne, maimakon ya tara tarin jami'an farfaganda, gara ya mayar da hankali wajen yin aiki tuƙuru domin ayyukan su yi masa kamfe da kansu.
Mutane ba wawaye ba ne. Misali, ta yaya mutumin da ba shi iya cin abinci da mutumin da kasuwancinsa ya lalace a ƙarƙashin mulkin wannan gwamnatin zai yarda da duk wata farfaganda da za a yaɗa?











