Darussa uku da suka kamata a ɗauka daga batun kama yara masu zanga-zanga a Najeriya

Tun bayan da Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin a saki yaran nan 27 daga cikin mutane 76 da aka kama aka kuma tuhuma da laifin cin amanar ƙasa yayin zanga-zangar matsin rayuwa a watan Agusta, ƴan Najeriya suka yi ta gargaɗin cewa lallai akwai darussa da suka kamata a ɗauka daga al'amarin.
Shugaban ya bayar da umarnin sakin dukkan ƙananan yaran yana mai cewa "a sake su kuma a sadar da su ga iyayensu," in ji ministan yaɗa labarai na Najeriya, Idris Mohammed.
Hakan ne ya sa wata kotu a Abuja ta soke tare da sakin yaran 26 da kuma sauran mutanen da gwamnatin ƙasar ta tuhuma da cin amanar ƙasa a ranar Juma'a.
Yanzu tambayar da ake yi ita ce waɗanne darasi ne suka kamata jama'a su ɗauka daga wannan al'amari?
Shawarwari uku
Dr Aliyu Usman Tilde masanin harkar ilimi ne kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum. Ya shaida wa BBC darussa uku da yake ganin za a koya domin guje wa afkuwar irin haka a nan gaba:
1) Gazawar al'umma
Darasi na farko wanda kuma yana da haɗari sosai musamman ga arewacin Najeriya, shi ne gazawar al'umma da suka haɗa da mahaifa da al'umma da kuma shugabanni.
"Ya kamata iyaye su sani cewa idan ba sun sanya ido a kan ƴaƴansu ba to lallai wata rana za su faɗa cikin haɗari. Idan ma a lokacin zanga-zangar an yi harbi da wasunsu sun sun mutu, duk da cewa an yi harbe-harben a wasu wuraren." In ji Dr Tilde.
Ya kuma ƙara da cewa bayan mahaifa, nauyin kula da yara musamman abin da ya shafi karatunsu ya rataya a wuyan gwamnati da sauran al'umma.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
2) Bincike
Masanin ya kuma ce ya kamata a yi bincike dangane da tsare da wahalar da ƙananan yaran kamar yadda shugaban ƙasa ya buƙata.
"Da ma haka ake yi idan aka yi zanga-zanga inda ake kama mutanen har ma da yaran domin a yi musu gwale-gwale na ɗan wani lokaci sai a sake su.
To amma kuma a wannan karon sai muka ga ba haka ba. An ɗauke yaran an tsare su tare da wahalar da su. Lallai kamar yadda shugaban ƙasa ya ce a yi bincike, a gano su waye suka bar su cikin wannan hali.
Sai dai kuma ya ce manyan cikinsu ya kamata a kai su kotu ta tuhume su domin zama izna ga masu son aikata laifi.
"Ya kamata duk wanda ya wuce shekaru 18 a kai shi gaban alƙali idan kotu ta same shi da laifi sai ta hukunta su idan kuma ba ta same su da laifi ba sai ta sake su."
3) Illar gangami a social midiya
Dr Tilde ya ce darasi na uku shi ne ya kamata jama'a musamman matasa su lura da irin yekuwa da ake yi a soshiyal midiya da ka iya tunzura yara aikata laifin da ba su yi niyya ba.
"Mutum ne zai tsaya yana zuga jama'a su yi kaza su yi kaza a soshiyal midiya amma sai ya noƙe a gidansa shi da ƴaƴansa.
Duk waɗannan yaran da aka kama babu ɗan babban mutum ko kuma ɗan boko. Kowa ya zulle aka bar yara talakawa har abin da ya faru ya faru. Saboda haka ya kamata a rinƙa yi wa yara da matasa matashiya dangane da illar zugar wasu da ka iya jefa su cikin matsala." In ji Dr Aliyu Tilde.











