Me kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce kan kamawa da tsare ƙananan yara?

Gurfanar da ƙananan yara 27 cikin mutum 76 da gwamnatin Najeriya ta yi a babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa tuhumar cin amanar ƙasa, ya tayar da hankalin ƴan Najeriya musamman ƴan arewacin ƙasar.
Bayan sukar da gwamnatinsa ta sha daga ƙungiyoyin kare haƙƙi, Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ba da umarnin sakin yaran da ake tsare da su a duk fadin ƙasar.
A ranar 1 ga watan Agusta ne dai ƴan Najeriya musamman matasa suka gudanar da wata zanga-zanga kan matsin rayuwa da ake yi wa laƙabi da #Endbadgovernance, wadda ta rikiɗe zuwa sace-sace da ƙone-ƙone.
Jami'an tsaro sun ce sun kama mutane da dama da suka zarga da tayar da tarzoma da kuma keta alfarmar Najeriya ta hanyar ɗaga tutar ƙasar Rasha.
A lokacin da aka gurfanar da su a ranar Juma'a a kotun, huɗu daga cikin yaran sun suma sakamakon yunwa, kamar yadda lauyoyinsu suka zarga.
Bayan komai ya lafa kuma an karanto musu tuhume-tuhumen da ake yi musu masu alaƙa da cin amanar ƙasa, amma sun musanta tuhumar.
Hotuna da bidiyon yaran da suka karaɗe kafafen sada zumunta sun nuna yadda suka rame kamar ba sa samun isasshen abinci a inda suke a tsaren fiye da kwana 90.
Wannan dai ya sa ƴan ƙasar ke neman sanin abin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanada dangane da kamawa da tsarewa da kuma tuhumar ƙananan yara da wani laifi.
Wane ne yaro?
Barrister Sulaiman Magashi lauya ne mai zaman kansa a birnin Kano, kuma ya shaida wa BBC cewa da farko ma tukunna sai an san wane ne yaro a dokar ƙasa.
Ya ce dokokin da ake amfani da su a arewacin Najeriya da ake kira "Penal Code" da kuma waɗanda ake amfani da su a kudancin Najeriya da ake kira "Criminal Code" sun kasa yaran zuwa gida uku.
- Yaro ɗan shekara bakwai: Sashe na 50 na penal code da sashe na 30 na ciriminal code, dukkansu sun amince cewa yaro ɗan shekara bakwai ba zai taɓa aikata laifi ba.
- Yaro mai shekara bakwai zuwa 12: Duk yaron da ke tsakanin wannan shekaraun ba za a iya tuhumar sa da wani laifi ba har sai idan an haƙiƙance cewa yana da masaniyar abin da ya aikata. Misali, idan yaro a waɗannan shekarun ya aikata kisan kai kuma za a iya fahimta daga yanayin aikinsa cewa ya san abin da ya aikata laifi ne kuma ga sakamakon abin da ya yi.
- Yaro ɗan shekara 12 zuwa 18: A tsarin waɗannan dokoki za a iya kama shi, a tuhume shi, a kuma hukunta shi, sai dai idan yana da kariya kamar kowane mutum da ya aikata laifi.
Yadda ake hukunta yara bisa doka
Barrister Sulaiman Magashi ya ce ba a tunanin yaron da ke ƙasa da shekara bakwai za a iya kama shi da laifi.
"Amma idan yaro ɗan shekara bakwai zuwa 12, ko ma zuwa 18, to akwai dokokin yara da ake kira "Children's and Young Persons Law" da jihohi da dama na Najeriya suka yi da ake amfani da su wajen yi musu shari'a," in ji lauyan.
"Dokokin sun fayyace yadda za a hukunta su, amma sun hana abubuwa kamar yin shari'ar a bayyane kamar yadda ake yi wa manya, sannan kuma akwai wasu kalmomi da ba a iya yin amfani da su kamar 'yanke hukunci', ko 'samun su da laifi'.
"Haka ma, idan aka same su da laifi to bai kamata a tsare su a gidan yari tare da manya ba. Wato ana killace su domin kada su cakuɗu da manya su samu gurɓatar tarbiyya."











