Abin da ya faru tsakanin kwamishiniya da likita a Kano

Abba Kabir Yusuf

Asalin hoton, Abba Kabir/Facebook

    • Marubuci, Rabiatu Kabir Runka
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 5

Kawo yanzu bincike ne kawai zai bayyana haƙiƙanin abin da ya faru tsakanin kwamishiniyar da likita.

Kuma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin kafa kwamitin bincike kan lamarin tare da fitar da sakamako cikin awa 48, kamar yadda kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dr Abubakar Labaran Yusuf, ya bayyana.

Kungiyar likitoci ta Najeriya reshen jihar Kano ta bai wa gwamnatin Kano wa’adin awa 48 na ko dai ta sallami kwamishiniyar ayyukan jinƙai, Amina HOD ko kuma su janye ayyukansu daga asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad a wani mataki na nuna ɓacin ransu kan zargin cin zarafin likitar.

"Kwamishiniyar ba ta cancanci matsayin da aka ba ta ba." in ji shugaban ƙungiyar likitoci ta Najeriya reshen jihar Kano, Dr Abdulrahman Aliyu.

Abin da likita ta ce an yi mata

A cikin wani bidiyo da likitar ta fitar ta bayyana cewa, tana aiki tun ƙarfe huɗu na yamma har zuwa ƙarfe 12 na dare a asibitin Murtala, inda take kula da marasa lafiya sama da ɗari biyu.

Likitar ta ce an kawo mata wata yarinya ƴar kimanin shekara biyu wadda take fama da rashin lafiya, inda ta duba yarinyar ta rubuta mata wasu magunguna ciki har da na ciwon mashaƙo da take tunanin yana damun yarinyar.

"A cikin magungunan akwai na mashaƙo, wanda akwai shi a asibitin sai dai yana wani wuri da yake kulle, sun samu guda ɗaya, sai suka riƙa cewa anya na san ma abin da nake kuwa, ganin haka sai na kira wadda take wa marasa lafiya allura na ce ta fara yi masu amfani da waɗanda suka samu," In ji likitar.

Likitar ta ce bayan ta ci gaba da duba marasa lafiya a daƙin kula da marasa lafiya na gaggawa, "sai kawai wasu mutane suka zo kaina kuma babu kowane jami'in tsaro a tare da ni, sai mutanen suka fara yi mani hayani, daga cikinsu akwai wata mata wai ita kwamishiniya, ta zo tana ta hayaniya tana faɗa, tana buga teburin da nake zaune.

Ni ko ƴar gidan gwamna ce sai an hukunta ni,bayan mutane sun shigo sai na samu dama na kira maigidana da hukumar asibitin, sai dai ban samu wani agaji daga hukumomin asibitin cikin lokaci ba."

Martanin kwamishiniya

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cikin wani bidiyo da ita ma kwamishiniyar jinƙan ta jihar Kano, Hajiya Amina HOD ta fitar ta ce an kira ta a waya ne aka shaida mata cewa wata yarinya na ta suma a asibitin birni na Murtala kuma likita ta ƙi ta duba ta.

Hajiya Amina ta ce bayan ta isa asibitin domin gane ma idon ta sai ta iske likitar zaune ko da ta same ta, ba ta ansa mata sallama ba, " Na ce mata baiwar Allah sannu, ba ta ansa mani ba, sai na sake yi mata magana ba ta ansa ba sai kallona da ta yi a shagiɗe, sai kawai ta tashi daga kan teburin, ta shige cikin wani ɗaki ta buga ƙofa.

Ta kira kwamishinan lafiya da SSG ba su Ɗauki waya ba domin ta shaida masu abin da ke faruwa. An rubuta allurar tun safe sun kasa samun ta cikin gari, sun ce a rubuta masu madadinta amman taƙi ta rubuta masu, gashi yarinyar na jin jiki kuma ko gado ba a ba su ba, kuma akwai alluran da yawa a asibitin amman an ɓoye su." In ji Hajiya Amina.

Kwamishiniyar ta ƙara da cewa mijin likitar ya same ta inda take ya yi mata rashin kunya, Inda ya ce "za ku zo ku ci wa matata mutunci na zo na ɗauke ta, an ce ke kwamishina ce, wace ce kwamishina? Waye ma gwamnan ? Bayan haka ma shekara huɗu za ku yi ku sauka."

Kwamishinar ta ce yaran da ke zagaye da ita sun so tayar da tarzoma saboda kalaman mijin, sai dai ita ce ta taka masu birki.

Hajiya Amina ta ce bayan ta isa gida shugaban jami'an tsaron asibitin ya kira ta ya shaida mata cewa mijin matar ya ɗauke ta, sai shugaban asibitin ne ya ƙarasa duba marasa lafiya.

Me ke janyo irin wannan tankiya?

Masana kiwon lafiya na ganin cewa idan an budi jaki sai a bugi taiki, kasancewar likitoci na fuskantar matsaloli a wuraren aikinsu sannan su ma mutane kan shiga wani hali a lokacin da mutum da suka kawo ke cikin matsananciyar rashin lafiya kuma idan ba a kai zuciya nesa ba sai a samu matsala.

"Yawan aiki ne ke yi wa likitocin Najeriya yawa saboda wani lokacin aikin da ya kamata mutum 10 su yi sai a bar wa likita guda, wanda hakan ke sanyawa suna saurin fushi, ga kumarashin kayan aiki." In ji wani tsohon ma'aikacin lafiya da ba son a ambaci sunansa.

Masani a fannin lafiya ya ƙara shaida wa BBC cewa, "ba aikin likita ba ne nemo magani ko allura saboda haka bai kamata likitar a bayaninta ta ce ta san akwai allurar a asibitin ko kuma an kulle ta ba. Aikin Likita shi ne rubuta magani ko allura, idan kuma wanda ta bada ba a same shi ba sai ta canza wanda zai maye gurbinsa."

Dangane kuma da halayya, ƙwararren likitan ya ce "akwai wasu likitoci da yawa da suke da girman kai kuma ba su tsayawa su kula da marasa lafiya yadda ya kamata, abin da ke tunzura wasu marasa lafiya".

Ya kuma ce wani lokacin wasu mutane ne ke janyo likitocin ke ƙin bai wa marasa lafiya kula ta musamman. "Misali wani lokaci mutanen da ke da hannu da shuni idan sun kai marasa lafiya su kan nemi a ba su kulawa ta musamman alhali akwai waɗanda suka fi su buƙatar hakan."

Rahotanni na cewa ana yawan samun rashin jituwa tsakanin likitoci da ‘yan uwan marasa lafiya a akasarin asibitocin jihar Kano, ko a farkon shekarar nan ma wasu mutane sun yi yunƙurin auka wa wani likita a asibitin Murtala, bisa zargin sa da ƙin kula dan'uwansu yadda ya kamata, inda aka yi ta kai ruwa rana da gwamnati, kafin daga bi sani aka daidaita da likitocin.

Kwamishinan lafiyar na jihar Kano, Dr Abubakar labaran Yusuf ya ce suna fatan likitocin asibitin za su ci gaba da aiki yayin da ake ci gaba da bincike.

"Mutanen gari da likitocin kowa zai zo zuciya a hannu ko ya aka yi masu wani abu, shi ya sa ake yawan samun hatsaniya. Mun fito da hanyoyin da za a warware ire-iren waɗannan matsaloli ta yadda nan gaba ba za a sake samun irin haka ba."