Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Za mu kashe shi' – Yadda masu aƙidar Alawi suke fuskantar barazana a Syria
- Marubuci, Feras Kilani
- Aiko rahoto daga, BBC News Arabic, western Syria
- Lokacin karatu: Minti 6
"Shi kaɗai ne ɗana ƙwaya ɗaya tal mai shekara 25," in ji Dalaal Mahna, a cikin hawaye. "A gaban idona suka ɗauke shi, suka faɗa mani cewa, "za mu kashe shi."
Wannan ne lokacin ƙarshe da Dalaal ta ga ɗanta, inda ta ce ƴanbindigar da suka ɗauke shi ne suka harbe shi.
Tana cikin ƴan Alawi na ƙasar, waɗanda ake farauta tun bayan da rikicin ya ɓarke a makon jiya.
"Kowa ya san ɗana yana da ciwon sukari da borin jini, ƙoƙarinsa kawai yadda zai cigaba da rayuwa."
Mun tarar da Dalaal ne tana samun mafaka tare da dubban wasu mutanen a wani ƙaramin sansanin sojin saman Rasha da ke yammacin yankin.
Wata ƙungiyar bibiyar yaƙi ta ce sama da fararen hula 1,400 ne aka kashe tun daga ranar 6 ga Maris - mafi yawansu ƴan Alawi - a Latakia da Tartous da Hama da Homs.
Dalaal na cikin waɗanda suka amince su yi magana da mu domin bayyana irin bala'in da suke fuskanta.
'Kisan rashin imani'
A makon jiya, jami'an tsaro suka ƙaddamar da aiki na musamman a yankin, a matsayin martani kan ƙaruwar rikici tsakanin magoya bayan tsohon Shugaban Ƙasa, Bashar al-Assad, wanda shi ma ɗan Alawi ne, kuma ƴan ƙungiyar suke mamaye gwamnatinsa.
Rikicin ya ƙara zafi ne bayan an yi wa wasu jami'an tsaron ƙasar harin ƙwanton ɓauna, aka kashe 13 daga cikinsu a birnin Jableh.
Ƴanbindiga masu alaƙa da gwamnatin ƙasar, wadda ta Sunni ce ake zargi da kashe-kashen na ramuwar gayya, inda suka fi kashe ƴan Alawi ɗin tun bayan harin na farko.
An kashe iyalai, ciki har da ƙananan yara da mata, kamar yadda ofishin kare haƙƙin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana.
A ranar Laraba, kakakin ofishin ya ce Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙididdige an kashe fararen hula 111, amma suna tunanin asalin waɗanda aka kashe ɗin sun haura haka.
Sannan ya ƙara da cewa mafiya yawa waɗanda aka kashe ɗin, kisan rashin imani aka musu.
A babbar hanyar, mun ga wata mota da harsasai suka lalata.
Sai dai babu tabbacin mutane nawa ne suka mutu a cikinta, ballantana sanin su wane ne.
Amma da wahalar gaske idan akwai wanda zai tsira daga cikin motar.
Manyan titunan ƙasar an tsare su, sannan an share duk wata alama da ke nuna an kai wani harin da ake zargin magoya bayan tsohon shugaban, da ma na ramuwar gaya.
Amma har yanzu akwai gomman gawarwaki a watse a cikin dazuka, da ma waɗanda aka binne a manyan ramuka, kamar yadda muka gani a ziyarar tamu, wadda wasu mayaƙan haya na ma'aikatar tsaron Syria suka mana rakiya.
Neman mafaka tsaunuka
Majiyoyin tsaro sun shaida wa BBC cewa ba a kashe magoya bayan Assad da suka kitsa harin na Jableh ba.
Domin sun tsere ne zuwa wasu tsaunuka a lokacin da aka turo ƙarin jami'an tsaron gwamnati.
"Dukkansu ƴan wannan ƙauyen ne," in ji Mahmoud al-Haik, wani soka da ke aiki da sabuwar ma'aitakar tsaron ƙasar, wanda aka tura aiki a Baniyas da ke Latakia.
"Duk waɗanda suke da hannu a wannan harin ƴan garin nan ne, amma yanzu sun tsere."
Na tambaye shi, "amma a harin na farko, sun ƙwace iko da mafi yawan garin (Baniyas), ko ba haka ba?
"Gaskiya a kwana biyu na farko an sha daga," in ji shi.
"Amma yanzu muna godiya ga Allah domin mun samu nasarar ƙwato garin. Mutane sun fara komawa gidajensu, kuma suna kiran sauran su dawo."
Har yanzu ƙauyukan babu mutane sosai a cikinsu, saboda mutane sun tsere suna rayuwa a tsaunuka a filin Allah.
A wani ƙauye da ke bayan garin Baniyas, mun tarar da wasu mutane da suka koma domin duba gidajensu da shagunansu.
Wani ɗan Alawy, Wafiq Ismail ya ce yana nan lokacin da harin ya auku, amma bai yi cikakken bayani ba.
"Gaskiya ba zan ce komai ba. Babu ruwana. Ba na cikin waɗanda suka yi, kuma ba zan taɓa shiga ba."
"Ba abin da nake magana ba ke nan, tunda kana nan aka kai harin, me ka gani da idonka?"
Sai dai yana magana ne cikin tsoro da fargaba. "Ba zan ce komai ba fa. Allah dai ya kare mu daga cutarwa."
'Kariya daga ƙasashen ƙetare'
A yankin Latakiya, sojojin Syria ne suke sintiri tare a samar da tsaro a sansanin sojin saman Rasha.
Mun samu shiga wani ɓangare na sansanin na sojin Rasha, wanda suka ba Assad goyon baya a yaƙin basasr ƙasar na shekara 13.
Dubban magoya bayan Alawy suna samun mafaka ne a sansanin bayan sun tsere daga hare-haren sojojin Syria, amma suna rayuwa cikin mawuyacin hali.
A wurin ne Dalaal ta ce an kashe mata ɗanta.
Sansanin na cike ne da labarai masu tayar da hankali.
Yawancin waɗanda suke rayuwa a sansanin sun taɓa rasa wani: ko dai ɗa ko ɗanuwa da maƙwabci.
Wata ƴar Alawy ta faɗa mana cewa, "muna buƙatar tallafin ƙasashen waje domin kare mu daga bala'in da muke fuskanta. Mun tsere daga gidajenmu, mun dawo nan da zama."
Har yanzu ba a samu cikakken bayani ba kan harin da ya auku a ranar Alhamis ba, da kuma irin illar da abin ya haifar, wanda shi kansa shugaban Syria Ahmad al-Sharaa ya yi magana a kai.
Sharaa ya yi alƙawarin kamawa tare da hukunta waɗanda suka kai harin, ko da kuwa mutanensa ne, inda ya ce, "ba zan amince da zubar jinin mutanen da ba su ba, ba su gani ba."