Dabarun da Amurka ta bi wajen kashe shugaban al-Qaeda shi kaɗai ban da iyalinsa

Awa ɗaya da 'yan mintuna bayan fitowar ranar 31 ga watan Yuli na 2022, daɗaɗɗen shugaban ƙungiyar al-Qaeda Ayman al-Zawahiri ya fito barandar wani gida da ke tsakiyar birnin Kabul - wanda aka ce nan ne wurin da ya saba zuwa don yin lazimi bayan Sallar Asuba.

Ashe shi ne abu na ƙarshe da zai yi a rayuwarsa.

Da misalin ƙarfe 06:18 agogon ƙasar (02:38 agogon Najeriya da Nijar), makamai masu linzami biyu suka afka barandar, inda suka kashe ɗan ƙasar Masar ɗin mai shekara 71 ba tare da sun taɓa 'yarsa da matarsa da ke cikin gidan ba.

Alamu sun nuna cewa an kai harin ne kan barandar ita kaɗai kawai.

Amma ta yaya aka iya kai harin daidai-wadaida?

A baya, Amurka ta sha suka kan yadda hare-hare da take kaiwa ke kashe fararen hula.

A wannan karon, ga yadda harin ya faru, da nazari kan halayen Zawahiri da suka taimaka wajen kashe shi - da kuma dalilin da ya sa za a ci gaba da kai hare-haren.

Saita maharba

Nau'in makaman da aka yi amfani da su ne sirrin nasarar - hukumomin Amurka sun ce shi ne makamin Hellfire da suka harba - wani nau'i na makaman da ake harbawa daga ƙasa zuwa sama da Amurka ke amfani da su a yaƙi da ta'addanci tun bayan harin 11 ga watan Satumba na 2001.

Ana iya hara makamin daga wurare da dama, ciki har da helikwafta, da na'urar girke a ƙasa, da jiragen ruwa, da jirgin sama - ko kuma a lamarin Zawahiri, daga kan jirgi maras matuƙi.

An yi imanin cewa Amurka ta yi amfani da Hellfires wajen kashe janar ɗin Iran, Qassem Soleimani, a birnin Bagadaza a farkon 2020, da kuma jagoran masu iƙirarin jihadi ɗan Birtaniya mai suna "Jihadi John" a Syria a 2015.

Daga cikin dalilan da suka sa ake yawan amfani da Hellfire shi ne saitin da suke da shi.

Duk sanda aka harba makami daga kan jirgi maras matuƙi - wani lokacin wani mutum ne da ke can a wata duniya mai nisa kamar Amurka zaune a wani ɗaki mai sanyi - yake kallon abin da ke faruwa ta bidiyo kai-tsaye ta hanyar tauraron ɗan Adam.

Ta hanyar amfani da baka da ke yake gani a jikin kyamara, ma'aikacin zai iya saita abin da yake nema kuma ya ɗana maharba a kansa.

Da zarar an harba makamin, shi kuma zai ci gaba bin wannan maharbar har sai ya dira kan inda aka saita shi.

Akwai hanyoyi bayyanannu da masu harba makamin ke bi kafin ɗaukar matakin don kauce wa kashe fararen hula.

A hare-haren Amurka da hukumar leƙen asiri na CIA na baya, sukan kira lauyoyin soja don neman shawararsu kafin a ba da umarnin sakin wuta.

Farfesa William Banks, ƙwararre kan kashe-kashe da gangan kuma wanda ya kafa cibiyar tsaro ta Syracuse University Institute for Security Policy and Law, ya ce a baya gwamnati sai ta auna yawan farar hular da za a yi asara da kuma girman da wanda ake so a kai wa hari.

Harin da aka kai wa Zawahiri, a cewarsa, "ya yi kama da na zamani" na irin wannan tsarin.

"Da alama sun yi kaffa-kaffa a wannan harin waje gano shi a wurin da kuma lokacin da za su ƙaddamar masa ba tare da sun taɓa kowa ba," in ji Farfesa Banks.

A wannan harin na Zawahiri, ana tunanin cewa - amma ba a tabbatar ba - Amurka ta yi amfani da wani nau'i na Hellfire - R9X - wanda ke da kaifi shida don ya kutsa cikin abin da aka hara.

A 2017, an kashe wani jagoran al-Qaeda leader kuma daya daga cikin mataimakan Zawahiri, Abu Khayr al-Masri, da makamin R9X Hellfire a Syria.

Amurka ta nazarci ɗabi'un Zawahiri na 'zuwa baranda'

Hotunan motarsa da aka ɗauka bayan harin sun nuna yadda makamin ya huda rufin motar sannan ya yi kaca-kaca da wanda ke ciki, amma ba tare da alamun wata fashewa ba ko kuma tarwatsa motar.

Har yanzu bayanai na ci gaba da fitowa kan hanyoyin da Amurka ta bi wajen tattara bayanan sirri kafin kai harin.

Bayan kai harin, hukumomi sun ce suna da isassun bayanai na "ɗabi'un rayuwar Zawahiri" a gidan - kamar zaman da yake yi a baranda.

Hakan ya nuna cewa masu tsegunta wa Amurka bayanai sun shafe makonni suna saka wa gida ido, ko ma watanni.

Wasu labaran da za ku so ku karanta

Marc Polymeropoulos, tsohon jami'i a CIA, ya faɗa wa BBC cewa da alama an yi amfani da hanyoyin tattara bayanai kafin kai harin, ciki har da mutane masu tsegunta bayanai da kuma alamomi.

Wasu kuma na cewa jiragen Amurka sun ɗauki lokaci suna dudduba wurin, waɗanda ba a iya ji ko ganinsu daga ƙasa.

"Dole ne ka tabbatar cewa mutumin ne, sannan kuma dole a kai harin ba tare da an kashe 'yan ba-ruwana ba, ma'ana ba a kashe fararen hula ba," a cewarsa.

"Abu ne da ke buƙatar haƙuri sosai. Muna da wannan ƙwarewar. Abu ne da Amurka ta ƙware a kai kusan shekara 20," in ji shi.

Sai dai ba koyaushe waɗannan hare-hare ke faruwa a yadda aka tsara su ba. A ranar 29 ga wata Agustan 2021, wani harin da aka kai kan mota a arewacin Kabul wanda aka yi niyyar harar gungun 'yan ISIS, ya kashe fararen hula 10.

Fadar tsaro ta Amurka Pentagon ta ce an yi "babban kuskure".

Bill Roggio, wani mai sa ido kan hare-haren Amurka a cibiyar Foundation for Defence of Democracies, ya ce ba mamaki harin Zawahiri "ya fi kowanne wahala" fiye da na baya saboda rashin dakarun Amurka a kusa da wajen.

Misali, hare-haren Amurka a Pakistan an kai su ne da jiragen da aka taso daga Afghanistan, yayin da hari a Syria ake kai su daga wurare masu aminci a Iraƙi.

"[A waɗancan wuraren] Abu ne mai sauƙi Amurka ta iya kaiwa ga wuraren saboda tana da mutane a yankunan. Amma wannan ya fi sarƙaƙiya," in ji shi.

"Wannan ne hari na farko kan al-Qaeda ko Islamic State a Afghanistan tun bayan ficewar Amurka. Wannan lamari ba abu ne da ya saba faruwa ba."

Za a iya sake kai irin wannan harin?

Mista Roggio ya ce "ba abin mamaki ba ne" idan aka sake kai irin wannan hari kan al-Qaeda a Afghanistan. "Akwai wuraren kai wa hari da yawa," in ji shi.

"Akwai yiwuwar sabbin shugabannin al-Qaeda za su koma Afghanistan, idan ma ba su riga sun je ba.

"Abin tambaya a nan shi ne, idan Amurka na da damar da har yanzu za ta iya aikata haka cikin sauƙi, to mene ne zai yi mata wahala kuma?"