Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Hotunan yadda Shugaba Bazoum ya karrama Buhari a Yamai
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ya karrama takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari inda aka sanya sunasa a jikin wani fitaccen titi da ke Niamey, babban birnin kasar.
Shugaban na Najeriya da 'yan tawagarsa sun samu tarba ta musamman a taron karramawar na ranar Alhamis.
Ga wasu daga cikin hotunan taron: