Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jihohin da aka fi kashe mutane a Najeriya daga farkon 2025 – Rahoto
Sassa daban-daban na Najeriya na ci gaba da fama da matsalar tsaro, lamarin da ke haifar da kisa da satar mutane domin karɓar kuɗin fansa.
A rahoton da kamfanin Beacon Security Intelligence mai nazari kan matsalar tsaro a Najeriya da yankin sahel ya fitar kan rashin tsaro a watan Maris da kuma watanni uku na shekarar 2025, ya nuna cewa an samu ƙaruwar yawan mutanen da aka kashe a cikin watanni uku na farkon 2025 idan aka kwatanta da mutanen da aka kashe a watanni uku na ƙarshen shekarar 2024.
Rahoton ya nuna cewa an kashe mutum 3,610 a tsakanin watan Janairu zuwa Maris na 2025, lamarin da ya zarta yawan mutanen da aka kashe daga watan Oktoba zuwa Nuwamban 2024.
A tattaunawarsa da BBC, shugaban kamfanin Beacon Security Intelligence ya ce "an samu ƙarin ƙaimin kai hare-hare a ɓangaren ƙungiyoyin Boko Haram da kuma Iswap a arewa maso gabas, sai kuma Lakurawa da kuma ƴan fashin daji a yankin arewa maso Yamma."
Ko a cikin makon nan gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya koka kan yadda Boko Haram ke samun nasarar karɓe yankunan jihar sanadiyyar hare-haren da take kai wa tana kashe mutane da kuma tayar da sansanonin sojoji.
Waɗanne jihohi ne aka fi kashe mutane a 2025?
Jihohin da matsalar tsaro ta fi ƙamari daga farkon shekarar 2025 a Najeriyar su ne:
Neja: An kashe mutum 631, an sace mutum 251 a hare-hare 178 da aka kai jihar.
Zamfara: An kashe mutum 585, an sace mutum 918 a hare-hare 250 da aka kai a jihar.
Borno: An kashe mutum 514, an yi garkuwa da mutum 357 a hare-hare 397 da aka kai a jihar.
Katsina: An kashe mutum 341, an yi garkuwa da mutum 495 a hare-hare 247 da aka kai a jihar.
Kaduna: An kashe mutum 106, a hare-hare 128 da aka kai a jihar.
Haka nan kuma sauran jihohin da aka kakkashe mutane a watannin farkon na shekarar 2025 su ne Sokoto, inda aka kashe mutum 93 da kuma Kebbi inda aka kashe mutum 91, kamar yadda rahoton ya bayyana.
Kashe-kashe a watan Maris
A watan Maris, kamar yadda rahoton ya bayyana an samu ƙaruwar kashe-kashen al'umma a Najeriya idan aka kwatanta da watan Fabarairu da ya gabace shi.
Rahoton ya nuna cewa a watan na Maris, jihar Neja ce aka fi kashe mutane, inda aka kashe mutum 368, lamarin da ya nunnunka yawan mutanen da aka kashe a watan Fabarairu inda aka kashe mutum 112.
Sai jihar Zamfara a matsayi na biyu, inda aka kashe mutum 179 a watan Maris, ƙasa da mutum 302 da aka kashe a jihar cikin watan Fabarairu.
Borno ce jiha ta uku da aka fi kashe mutane a watan na Maris inda aka kashe mutum 151, ƙasa da mutum 181 da aka kashe a watan Fabarairu.
Me ya sa matsalar ta ƙara muni?
Rahoton ya lissafo wasu abubuwa da ya bayyana a matsayin waɗanda suka taimaka wa ta'azzarar matsalar tsaron a Najeriya, waɗanda suka haɗa da:
-Sake yunƙurowar ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai a yankin arewa maso gabashin Najeriya da kuma ayyukan ƴan ƙungiyar Lakurawa a Arewa maso Yamma.
-Rikicin siyasa: Rahoton ya ce ƴan siyasa sun fara fafutikar ganin sun shirya wa zaɓen shekara ta 2027, lamarin da ke haifar da rikice-rikice, ciki har da rikicin siyasa na jihar Rivers wanda ya kai ga cewa shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kafa dokar ta-ɓaci a jihar.
-Rikicin al'umma: Munanan rikice-rikice tsakanin al'umma a a jihar Osun da kuma kisan da aka yi wa mutanen a jihar Edo.
-Zanga-zanga: Zanga-zangar da aka gudanar a wasu sassan ƙasar domin ganin an inganta tsaro.
Me ya sa Boko Haram ke ƙara ƙaimi?
A tattaunawarsa da BBC, shugaban kamfanin Beacon Security and Intelligence mai nazari kan tsaro, ya bayar da wasu hujjoji guda biyu da ya ce suna cikin abubuwan da suka sa ake ganin hare-haren Boko Haram na farfadowa:
“Ƙungiyar Iswap na fitar da wata ƙasida wajen bayar da umarni, kuma a duk lokacin da ta fitar da irin wannan umarni mayaƙanta kan ƙara azama wajen kai hare-hare.
“Rundunar sojin Najeriya ta raba hankalinta wajen gudanar da ayyukanta, wato Arewa maso Gabas da kuma arewa maso Yamma,” in ji Adamu.