COP29: Ana zargin Azerbaijan mai masaukin baƙi da kama masu rajin kare muhalli

Gubad Ibadoglu na leƙa waje ta tagar gidansa inda ake yi masa ɗaurin talala

Asalin hoton, Aziz Karimov/Getty Images

Bayanan hoto, Hukumomin Azerbaijan sun tsare Farfesa Gubad Ibadoglu na jami'ar LSE har kusan wata 18
    • Marubuci, Esme Stallard
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Sashen Kimiyyar Yanayi
    • Marubuci, Ilkin Hasanov
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Azerbaijani
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam sun zargi gwamnatin Azerbaijan da yin amfani da taron COP29 wajen murƙushe masu fafutikar kare muhalli da sauran 'yan adawar siyasa.

Wannan ce shekara ta uku a jere da ake zargin ƙasar da ke karbar baƙuncin taron sauyin yanayi da muzgunawa da hana masu fafutikar dama.

Ƙungiyar 'Climate Action Network' - gamayyar ƙungiyoyin rajin kare muhalli kusan 2,000 - ta shaida wa BBC cewa kare fararen hula na da matuƙar muhimmanci ga duk ƙasashen da ke son samun cigaba a fannin sauyin yanayi.

Gwamnatin Azerbaijan ta yi watsi da iƙirarin tana mai cewa gwamnatin ba ta tsare da kowane irin fursunan siyasa.

Shugabannin ƙasashen duniya na taro a Azerbaijan domin tattauna yadda za a warware matsalolin ɗumamar yanayi.

To sai dai ƙungiyoyin kare haƙƙin bil-adama na kiran a sake duba ƙa'idojin da ake bin wajen zaɓar ƙasashen da za su riƙa karɓar baƙuncin taron, bayan abin da suka kira ƙaruwar matsalar kama masu rajin kare muhalli a Azerbaijan.

Natalia Nozadze daga ƙungiyar Amnesty International ta faɗa wa BBC cewa tun da aka ayyana ƙasar Azerbaijan a matsayin wadda za ta karɓi baƙuncin tarin sauyin yanayi na COP29 a watan Nuwamban bara, nuna adawa da gwamnati ya ƙara zama wata abbar matsala.

“Mun ga ƙaruwar kama tare da ƙoƙarin murƙushe duk waɗanda gwamnati ta ga tamkar suna nuna adawa da manufofin na siyasa,'' in ji ta.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A karon farko tun farkon shekarun 2000, adadin fursunonin siyasa, ciki har da 'yanjarida da masu rajin kare muhalli da 'yan adawar siyasa ya kai fiye da mutum 3,00, kamar yadda ƙungiyar 'Gwagwarmayar tabbatar da 'yancin fursunonin siyasa a Azerbaijan' ta bayyana.

Farfesa Gubad Ibadoglu, mai shekara 53 na jami'ar LSE da ke Landon ya gudanar da bincike kan fannin man fetur da gas da matsalolin da suka shafi muhalli, amma an kama shi a bazarar 2023 kan zargin zamba.

Yanzu fiye da shekara guda yana cikin ɗaurin talala. Ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta HRW ta ƙira tuhume-tuhume da ''marasa ƙwari'', sannan kuma 'yar Gubad Ibadoglu ta yi kira da firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer ya taimaka ya sa baki wajen sakin mahaifin nata.

"Ina tunanin hakan ɗaya ne daga cikin dokokin gwamnatin mulkin kama-karya, kamawa da tsare mutanen da za su iya yin tasiri a ra'ayoyinsu,'' kamar yadda Mista Ibadoglu ya bayyana wa BBC a wannan makon.

Ya ce rayuwarsa na cikin hatsari, sakamakon dalilai na rashin lafiya.

Wata rijiyar tonon mai da wasu manyan gine-gine a bayanta.

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto, Azerbaijan na ƙoƙarin faɗaɗa amfani da man fetur da iskar gas nan da shekaru masu zuwa, duk kuwa da yunƙurin da duniya ke yi na daina amfani da makamashin da ke gurɓata muhalli.

An kama Anar Mammadli a watan Afrilu bisa zargin fasa-ƙwauri wata biyu bayan da ƙungiyarsa ta yi kira ga gwamnatin Azerbaijan ta yi duk mai yiwuwa don aiki da yarjejeniyar Paris, wadda ta buƙaci rage amfani da makamashin da ke gurɓata muhalli.

Mai rajin kare muhallin na son Azerbaijan ta rage dogaro da man fetur da iskar gas, wanda ke samar da kashi 60 cikin 100 na kasafin kuɗin gwamnatin ƙasar.

A watan Janairu an bayyana cewa ƙasar Azerbaijan na shirin faɗaɗa tono iskar gas da man fetur nan da shekara 10 masu zuwa. Haka kuma a ranar Talata shugaban ƙasar Iham Aliyev ya shaida wa taron COP29 cewa man fetur da iskar gas ''kyauta ce daga Allah''.

“Taron COP29 - wanda aka tsara a matsayin dandalin kare kare muhalli - amma an bayar da shi a wani abu daban,'' in ji Bashir Suleyman, wani makusancin abokin Mista Mammadli.

“Ƙungiyoyin fararen hula, waɗanda su ne za su faɗa wa gwamnati gaskiya an mayar da su saniyar waye ko ba a yi da su'', in ji shi.

A watan Oktoba aka yanke wa Nazim Beydemirli, mai shekara 61, ɗaurin shekara takwas a gidan yari saboda samunsa da laifin yi wa mutane ƙwace.

A shekarar da ta gabata ne aka kama shi bayan ya nuna adawa da masu haƙar zinare a kusa da ƙauyensa.

Babu wata hujja da aka gabatar a tsawon wata 15 da aka ɗauka ana sauraron shari'ar, lokacin da yake zaman jiran shari'a.

Lauyansa, Agil Lajic, ya kafe cewa zarge-zargen marasa tushe ne, kuma yana daga cikin matakan yin shiru kan batun gabanin taron COP29.

Yayin da yake magana a farkon taron, babban jami'in ma'aikatar harkokin ƙasashen waje na ƙasar Elchin Amirbayov ya faɗa BBC cewa, duka waɗanann zarge-zarge ne marasa tushe ake yi wa ƙasarsa.

''Ba zan amince da duka zarge-zargen nan ba, saboda ba a gina su kan gaskiya ba''.

Su ma ƙasashen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Masar da suka karɓi baƙuncin tarukan da suka gabata sun fuskanci zarge-zarge da suka kan yadda suke muzguwa ƙungiyoyn fararen hula.

A kowace shekara akan zaɓi mai masaukin baƙin taron Cop daga wata nahiya ta daban, kuma dole ne sai duka ƙasashen nahiyar sun amince da wannan ƙasa kafin a ba ta dama. To sai dai ba a san matakin da suke bi ba don hana ƙasar da ke muzgunawa ƙungiyoyin fararen hula damar ɗaukar nauyin taron.

Majalisar Dinkin Duniya ba ta bai wa 'yan gwagwarmaya nuna adawa a taron COP, amma a nata martani UNFCCC, hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da kare muhalli, ta ce ''a karon farko, sharaɗin da aka bi wajen zaɓen mai karɓar baƙuncin wannan taron ya haɗa da batun kare ƙungiyoyin fararen hula, wanda muke maraba da shi amatsayin ci gaba''.