An kama Jagoran ƴan awaren Kamaru a Norway bisa laifin iza wutar rikici

Asalin hoton, Ambazonia Governing Council
- Marubuci, Paul Njie
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Yaoundé
- Lokacin karatu: Minti 2
An kama shugaban 'yan awaren Kamaru a ƙasar Norway bisa zargin sa da taka rawa a rikicin masu ɗauke da makamai da ke gudana yanzu haka a ƙasar da ke tsakiyar Afirka.
An kama Lucas Ayaba Cho ranar Talata ''kan zarge-zarge masu alaƙa da furucin da yake yi a shafukan sada zumunta'', kamar yadda lauyansa ya shaida wa BBC.
Mista Cho na da ƙarfin faɗa a ji a yankin masu magana da Turancin Ingilishi da ke rajin samun 'yancin kai daga ƙasar Kamaru.
Fafutikar ta haifar da riciki da ya yi sanadin kisan fiye da mutum 6,000 tare da raba kusan miliyan guda da muhallansu, tun farkon fara rikicin a 2016.
Wasu mutane a larduna biyu da ke magana da Turancin Ingilishi sun ce suna fuskantar wariya daga masu magana da Faransanci masu rinjaye a ƙasar.
Ƙungiyar kare haƙƙin bil-adama ta 'Amnesty International' ta zargi duka dakarun gwamnati da 'yan awaren masu ɗauke da makamai da aikata kashe-kashe da fyaɗe da kuma muzgunawa fararen hula.
Wani jami'in gwamnatin Kamaru ya shaida wa BBC cewa ƙasar na da yarjejeniyar tsaro da Norway, wanda hakan zai bayar da damar mayar da mista Cho zuwa Kamaru a 'yan kwanakin da ke tafe.
Wane ne Lucas Ayaba Cho?
Cho, wanda ya ayyana kansa a matsayin jagoran ƙwatar 'yanci, na ɗaya daga cikin fitattun jagororin 'yan aware da suka sauya salon rikicin 'yan awaren yankuna masu magana da Turancin Ingilishi.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mai shekara 52, shi ke jagorantar majalisar gwamnatin Ambazonia (AGovC), wani sashe na dakarun tsaron yankin Ambazonia (ADF), ɗaya daga cikin ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ke neman 'yancin gashin kai.
Yana aiwatar da ayyukansa ta hanyar bayar da umarni daga inda yake zaune a ƙasar Norway, inda aka yi amanna cewa daga can ne ya bayar da umarnin baya-bayan nan na dokar kulle ta mako biyu a yankin, a wani ɓangare na gangamin 'yan awaren na ƙaurace wa makarantu.
Mista Cho da aka sani da zafafan kalamai da tattsauran ra'ayi, ya fara fuskantar suka bayan da a baya-bayan nan mayaƙan ADF suka farmaki direbobin tasi a yankin arewa maso yammacin ƙasar, bayan da aka umarce su su sauya wa motocinsu kala daga ruwan ɗorawa zuwa fari da shuɗi, wanda ya dace da kalar tutar yankin Ambazoniya.
Inda aka ƙona motocin waɗanda suka turjewa dokar.
A watan Janairun 2017, ya ce ya tsallake rijiya da baya kan yunƙurin kisan bayan ganawa da wasu jagororin 'yan awaren a ƙasar Belgium.
Hukumar binciken mayan laifuka ta ƙasar Norway ta ce Cho ya taka muhimmiyar rawa wajen rikicin da ke gudana yanzu haka a Kamaru.
A ranar Larana, masu shigar da ƙara na Norway suka nemi kotun gundumar Oslo ta ba su shi.
Muna matakin farko na gudanar da bincike, kuma akwai bincike masu yawa da za mu masa,'' Anette Berger mai shigar da ƙara a Norway.
Idan aka same shi da laifi a Kamaru, Cho zai iya fuskantar ɗaurin shekara 30 a gidan yari.
Cho ba shi ne jagoran 'yan aware na farko da aka kama a ƙasashen waje ba, bisa zargin alaƙa da rikicin Kamaru.
Tun bayan ɓarkewar rikicin, gwamnatin Kamaru ke kira ga ƙasashen duniya da jagororin 'yan awaren ke zaune a cikinsu da su taimaka wajen kama su tare da mayar mata su gida don fuskantar shari'a kan rawar da suka taka kan rikicin ƙasar.
A shekarar 2018, aka kama wani jagoran 'yan awaren yankin masu magana da Turancin ingilishi, Julius Sisiku Ayuk Tabe, da wasu mutum 46 a Najeriya daga baya kuma aka mayar da su Kamaru.











