Hikayata 2024: Gwaraza uku da suka ciri tuta a gasar bana

Hausawa kan ce wai rana ba ta ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya. Bayan kwashe watanni tara ana gwagwagwa dangane da gasar rubutun gajeru kuma ƙagaggun labarai ta mata zalla ta BBC Hausa wato Hikayata, a yau za mu bayyana muku sunayen mata guda uku da labaransu suka ciri tuta.
Da farko dai BBC Hausa ta samu labarai kimanin 450 da marubuta suka aiko mata inda kuma bayan tankaɗe da rairaiya aka miƙa labarai 400 ga alƙalai na sahun farko waɗanda duka malaman jami'a ne masana harshen Hausa inda suka tantance suka zaɓi guda 30.
Daga cikin 30 din ne kuma alƙalan na ƙarshe suka zaɓi guda 15, inda 12 suka cancanci yabo sannan kuma uku suka zama zakaru inda a ciki za a bayyana labari na ɗaya da na biyu da kuma na uku. Labarai ukun kuwa su ne:
- Labarin Tsalle Ɗaya wanda Zainab Muhammad Chubaɗo daga jihar Kaduna ta rubuta.
- Labarin Amon Ƴanci wanda Hajara Ahmed Hussaini daga garin Hadejia na jihar Jigawa ta rubuta.
- Labarin Kura a Rumbu wanda Amrah Auwal Mashi daga jihar Katsina ta rubuta.
A ranar Laraba 27 ga watan nan na Nuwamba ne dai za a gudanar da bikin karrama gwarazan a Abuja, babban birnin Najeriya.
Waɗanda suka yi nasara za su samu kyautar kuɗi da lambar yabo da kuma shaidar shiga gasa: wannan ya ƙunshi N1,000,000 (nairan miliyan ɗaya) ga wadda ta zo ta ɗaya, N750,000 (naira dubu ɗari bakwai da hamsin) ga wadda ta zo ta biyu, N500,000 (naira dubu ɗari biyar) ga wadda ta zo ta uku.
BBC za ta karanto labarai 12 da alƙalan suka ce sun cancanci yabo da guda ukun da suka yi nasara a tasharta ta BBC Hausa.







