Ko PDP za ta iya ɗinke ɓarakarta kafin zaɓen 2027?

Lokacin karatu: Minti 3

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP ta ce ta soma ɗaukar matakan ɗinke ɓarakar da ta dabaibaye ta a ƴan shekarun nan.

Matakin baya bayan nan shi ne na taron masu ruwa da tsaki da jam'iyyar ta gudanar.

Shin ko hakan zai kawo ƙarshen matsalolin da jam'iyyar ke fuskanta tun bayan faɗuwa zaɓen 2023?

Daga cikin matsalolin da suka kunno kai a cikin babbar jam'iyyar adawa ta Najeriya bayan faɗuwwa zabe a 2023, akwai bambarwa a kan yadda za ta ɗinke ɓarakar da aka samu a lokacin zaɓen fitar da gwani, da rikicin shugabanci a matakai daban-daban da kuma kasa tsayawa da ƙafarta domin samar da adawa mai nagarta a siyasar ƙasar.

Sau tari dai an sha jin masu ruwa da tsaki a cikin gidan jam'iyyar na cewa suna ƙoƙarin ɗinke ɓarakar tasu da kuma dawowa da ƙarfi, har ma a wasu lokutan sukan sha alwashin ƙwace mulki daga hannun jam'iyyar APC.

A tsakanin ranar Lahadi da dare zuwa wayewar garin jiya Litinin ma an ga yadda masu ruwa da tsaki a jam'iyyar PDPn suka yunƙura domin samar da mafita ga ɗimbin matsalolin nasu, inda har suka kafa ƙwamitin da zai jagoranci cimma nasarar hakan.

Tuni dai masana harkokin siyasa a Najeriya, irin su Dr Yakubu Haruna Ja'e na jami'ar jihar Kaduna suka fara sharhi a kan wannan batu.

Ya ce, '' To gaskiya abu ne da ya kamata a ce sun yi shi tun a baya duk da kuma cewa akwai barazana mai karfi da ke fuskantarsu, kasancewa shi shugaban kasa na yanzu na jam'iyyar APC mutum ne dansiyasa kuma zagaye yake da 'yansiyasa suna kokarin su ga sun janyo abin da zai zama duk wata jam'iyya mai rikicin cikin gida to mutum ya kauce ya dawo ita jam'iyya mai mulki.''

To ko me ya janyo jinkiri wajen ɗinke ɓarakar PDPn, Sanata Umar Tsauri, mamba ne a kwamitin amintattu na jam'iyyar.

Dangane da hasashen da ake ta yi cewa ƴan adawar, ciki harda PDP suna neman ƙulla haɗaka domin fuskantar zaɓen 2027 kuwa, Dr Yakubu Ja'e na ganin cewa har yanzu ba a makara ba.

Ya ce, '' Shugaban da yake kai gaskiya yana da karfi duk da ana ganin kamar ba a son shi amma yana da abin da zai sa a so shi saboda yana da kudi mutane kuma ba a raba su da kudi idan siyasa ta taso.

''To amma idan da waɗannan jam'iyyu za su iya haɗa kai kwarai da gaske za su iya kaiwa ga nasara tun da akalla idan ka lura masoya APC sun yi rauni a wasu manyan jihohi akalla biyar - idan ka duba a Lagos daman APC ba su ci zabe ba kuma har yanzu suna da rauni, sannan a Rivers abin da suka yi suka cire zababben gwamna suna sa nasu wannan zai iya sa su rasa jihar a Kano shi ma haka ne a Kaduna shi ma haka ne.

To idan ka dubi wadannan manyan jihohi lalle da PDP za ta hada kai da wasu jam'iyyu zai iya ba ta dama ta ci zabe in an cire kwadayi

Ita dai jam'iyyar PDP ta yi amanna cewa ko yanzu aka shiga zaɓe tana da hajar tallatawa ƴan Najeriya, kamar yadda Sanata Umar Tsauri ke cewa.

''Ba za ka iya gane mutum fari ba ne sai akwai baki a tare da shi, ba za ka iya gane mutum gajere ba ne sai akwai dogo a tare da shi.

''Idan mutane suka kwatanta mulkin APC na shekara biyu da kuma mulkin PDP na shekara 16 sai su yanke hukunci.'' In ji shi

Masu sharhi dai na ganin cewa duk waɗannan dabaru da salon fille ƙafafun juna dake gudana a tsakanin jam'iyyun siyasar Najeriya ba su wuce fafutukar neman mulki a 2027 ba, wanda kuma lokaci ne kawai zai iya tabbatar da ɓangaren da ya fi iya allon sa.