Ko sauya sheƙa zai iya durƙusar da jam'iyyar PDP?

Lokacin karatu: Minti 5

Abubuwa na ta sauyawa a siyasar Najeriya, musamman a baya-bayan nan da aka samu yawaitar ƴan siyasa da ke ficewa daga babbar jam'iyyar adawa ta ƙasar - PDP.

Ficewar gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori daga PDP zuwa APC ta sanya a yanzu yawan gwamnonin jam'iyyar sun ragu.

A Litinin ɗinnan ne mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima da shugaban jam'iyyar APC Abdullahi Umar Ganduje da kuma sauran ginshiƙan jam'iyyar suka karɓi gwamnan.

Wannan ya sanya a yanzu APC ke da gwamnoni uku daga cikin shida a shiyyar Kudu maso kudancin Najeriya, yankin da a baya jam'iyyar PDP ke da ƙarfi cikinsa tsawon shekara 20.

A yanzu jihohin Cross River da Edo da Delta duk sun koma hannun APC, yayin da Rivers da Akwa Ibom da Bayelsa ke hannun jam'iyyar hamayyar ta PDP.

Sai dai wasu rahotannin na cewa akwai yiwuwar wasu gwamnonin na PDP za su sauya sheƙa.

PDP ita ce babbar jam'iyyar adawa a Najeriya, sai dai rikice-rikicen cikin gida ya yi mata dabaibayi, lamarin da ake ganin ya hana ta taka rawar da ta kamata a ɓangaren adawa.

Haka nan kasancewar ɗaya daga cikin manyan ƴaƴanta - Nyesom Wike - a cikin gwamnatin APC ta Bola Tinubu ya sanya wasu ke zargin ta da kasancewa tamkar "wani reshe na jam'iyyar APC".

Duk da cewa wasu manyan ƴan siyasa a Najeriyar sun nuna alamun cewa za su haɗe domin samar da adawa mai ƙarfi a zaɓen 2027, gwamnonin PDP a taron da suka yi na baya-bayan nan sun nesanta kansu daga haka.

Sai dai ficewar da ƴaƴan jam'iyyar ke yi da kuma karkatar da wasu daga cikin jigajiganta, kamar Atiku Abubakar ke yi ga batun haɗakar ƴan hamayya ba abin da jam'iyyar za ta so ne ba.

Shin wace irin illa hakan zai yi wa PDP?

"Tabbas, PDP na neman ta rasa ƙarfinta a Najeriya duba da yanayin yadda jihohin da jam'iyyar ta mallaka a 2015 da kuma yadda suke yanzu," in ji Lekan Ige, masani a fannin siyasa, a wata hira da BBC.

"A shekarar 2015, PDP ta mallaki jihohi 11, amma yanzu, bayan canjin gwamnan jihar Delta, sun rage zuwa 10. Kuma jita-jita na cigaba da yaɗuwa cewa gwamnonin Akwa Ibom da Rivers na iya canza jam'iyya su shiga APC nan ba da jimawa ba.

"Akwai wani lokaci a wannan ƙasa da PDP ta shugabanci ɓangaren zartarwa da kuma majalisar tarayya, amma yanzu ta zama jam'iyyar adawa. Saboda haka ta bayyana ƙarara cewa PDP ta rasa ƙarfin ikonta a Najeriya." In ji Ige.

Har wa yau, masanin ya ƙara da bayanin cewa " babbar illar sauya sheƙar ƴan PDP zuwa jam'iyya mulki shi ne yadda abin ke faruwa a daidai lokacin da ya kamata su haɗe kansu su tunkari APC. Amma yanzu a yadda ake tafiya da wuya jam'iyyar ta iya taɓuka wani abin arziƙi a kakar zaɓe mai zuwa ta 2027. Abin da ke nuna ƙarara cewa jam'iyyar ta durƙushe."

Yunƙurin rusa PDP hatsari ne ga dimokuraɗiyyar Najeriya - Sule Lamido

Jigo a babbar jam'iyyar hamayya ta Najeriya, PDP, Sule Lamido, ya yi gargadin cewa ƙoƙarin rusa jam'iyyar tamkar yunƙurin murƙushe dimokaradiyya ne.

Sule Lamido wanda tsohon gwamnan jihar Jigawa ne a arewacin ƙasar kuma tsohon ministan harkokin waje, ya ce ficewar wasu jiga-jigan PDP zuwa APC mai mulki tuggun ne da ba zai yi wa 'yan siyasa daɗi ba nan gaba.

"Murƙushewa da gana azaba, su ne alamun cewa mulki ya zo - haka abin yake a tarihi," in ji shi cikin wata hira da BBC.

"Ya kamata a ce Shugaba Bola Tinubu ya yi adalci, ya san cewa shi shugaban kowa da kowa ne, ya ƙyale mu mu 'yansiyasa mu yi kokawa da APC a jam'iyyance. Amma idan bai yi hankali ba dabarar za ta ci shi."

A jiya Litinin Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da wanda ya gada Ifeanyi Okowa suka koma jam'iyyar APC a hukumance bayan sun bar PDP.

A baya-bayan nan wasu 'yanmajalisa daga jam'iyyun adawa na Labour da NNPP sun koma APC ɗin, yayin da ake raɗe-raɗin wasu gwamnonin na kan hanyar komawa APC ɗin.

Illa ga al'ummar Najeriya

Malam Kabiru Sufi ya ce babbar illar da durƙushewar jam'iyyar adawa ta PDP za ta yi ga al'ummar ƙasa ita ce "za a kai lokacin da babu wata jam'iyya mai hamayya mai ƙarfi da za ta rinƙa taka wa jam'iyya mai mulki burki dangane da daidai ko rashin dai-dai.

Gwamnati za ta rinƙa abubuwa gabagaɗi ba tare da shakkar suka daga masu hamayya ba. Misali, mun ga yadda gwamnatin nan ta fasa zaratar da shirye-shirye da dama sakamakon caccakar da jam'iyyun hamayya ke yi kan batutuwa."

'Najeriya na fuskantar haɗarin zama ƙasa mai jam'iyya ɗaya'

Yayin da jam'iyyar adawa ta PDP ke cigaba da fuskantar manyan koma baya tare da samun yawaitar mambobinta suna canzawa zuwa jam'iyya mai mulki ta APC, masana siyasa sun fara nuna damuwa kan makomar dimokuraɗiyya a Najeriya.

Wasu na ganin cewa yawancin waɗanda ke sauya sheka zuwa jam'iyyar APC na yi ne domin kare kansu daga bincike ko hukunci kan abubuwan da suka aikata a baya.

Babban abin damuwa, in ji su, shi ne irin wannan yanayi na iya jefa Najeriya cikin tsarin jam'iyya ɗaya, inda babu isasshen ƙarfi daga jam'iyyun adawa ko kuma a rage ko a kawar da muryar 'yan adawa gaba ɗaya.

Akinola Ayobami, wani masani a fanni siyasa ne kuma ya bayyana cewa wannan salo yana da haɗari ga makomar siyasar Najeriya.

A cewarsa, wannan tsarin jam'iyya ɗaya na nufin jam'iyya daya ce ke riƙe da mulki, babu wata dama da aka bai wa jam'iyyun adawa su bayyana ra'ayinsu ko ƙalubalantar gwamnatin da ke mulki.

"Idan aka kalli yadda siyasar Najeriya ke tafiya a yanzu, kamar muna tunkarar tsarin jam'iyya ɗaya ne. Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya saba da irin wannan salon a lokacin da ya ke gwamnan Jihar Legas, kuma kamar yana ƙoƙarin amfani da wannan dabarar a matakin tarayya," in ji Ayobami.

To sai dai Malam Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen jami'a ya ce duk da irin wawason da jam'iyya mai mulki ta APC ke yi a yanzu haka ba ya nuna cewa jam'iyyar ka iya zama jam'iyya ɗaya tilo a Najeriya.

"Duba da cewa har yanzu ana jin motsin sauran jam'iyyun na hamayya da ma ƙoƙarin haɗa da masu hamayyar ke yi na nuna cewa ba a ɗauki hanyar komawa tsarin jam'iyya ɗaya a ƙasar ba.

Har yanzu jam'iyyar APC ba ta yi shekarun da jam'iyyar PDP mai hamayya ta yi a baya ba tana mulki. PDP ta kwashe shekaru 16 kuma ƴan jam'iyyar sun ta yin iƙrarin cewa ba za su bar wata jam'iyya ta yi mulki ba. Amma bayan haɗaka da abokan hamayya suka yi daga ko'ina sai ga shi sun kayar da ita. To ita ma APC hakan ka iya faruwa a kanta." In ji Malam Kabiru Sufi.