Yadda ziyarar Tinubu zuwa Kano ta bar baya da ƙura

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Juma'a da ta gabata ne, shugaba Bola Tinubu ya kai ziyara zuwa jihar Kano, domin ta'aziyyar rasuwar hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Alhaji Aminu Ɗantata da ya rasu a ƙarshen watan da ya gabata.

Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce a lokacin da aka yi rasuwar Tinubu ba ya ƙasa, amma duk da haka ya aika tawaga ƙarƙashin ministan tsaron ƙasar domin wakiltarsa a wajen jana'izar.

Sai dai ziyarar tasa ta bar baya da ƙura, saboda rashin zuwa gidan gwamnatin jihar da kuma gidan Sarki.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa gwamna Abba Kabir Yusuf bai ji daɗin abin da ya faru ba saboda ƙin ziyarar gidan gwamnati inda aka shirya masa liyafar cin abinci.

A ɗaya gefen, shugaban Najeriyar bai je ko da gidan ɗaya daga cikin sarakunan jihar biyu da ke takun tsaka ba, Sarki na 16, Muhammadu Sanusi na II da Sarki na 15 Aminu Ado Bayero.

A bisa tsari dai, shugaban ƙasa na ziyartar gidan gwamnatin jiha da kuma fadar sarkin duk jihar da ya je.

Sai dai a ziyarar da ya kai Kano, a gidan marigayi Aminu Dantata ne kaɗai shugaban ya tsaya.

Gwamnan Abba Kabir ya nuna rashin jin daɗi

Kamar yadda wasu rahotanni suka bayyana, wasu na kusa da gwamnan jihar ta Kano - sun ce gwamnan ya nuna rashin jin daɗin rashin zuwa gidan gwamnati da Tinubu ya yi, ganin cewa ya buƙaci ƴan jihar su yi wa shugaban kyakkyawar tarba yayin ziyarar tasa.

Gwamnan Abba Yusuf ne ya tarbi shugaba Tinubu a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano tare da sauran magoya bayan jam'iyyar APC, waɗanda suka yi ta sowa da rera waƙoƙi.

An bayyana cewa gwamnan na Kano ya samu labarin cewa Tinubu ba zai je gidan gwamnati bane a lokacin da ya isa gidan marigayi Dantata, inda ya nuna fushinsa kan hakan kan tawagar jami'an tsaron shugaban ƙasar.

An kuma ruwaito cewa wasu jami'ai da masu aikin goge-goge a gidan gwamnati ne suka koma cin abincin da aka shiryawa shugaban ƙasar, bayan samun labarin cewa ya koma zuwa Abuja.

Ana ganin cewa shugaban ya ki ziyartar gidajen sarakunan ne kada a ɗauka cewa yana goyon bayan wane ɓangare a rikicin da ya dabaibaye masarautar jihar mai tarihi.

Haka ma wani abu da mutane suka yi ta tofa albarkacin bakinsa a kai shi ne rashin ganin tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje yayin ziyarar shugaba Tinubu.

'Dalilin da ya sa Ganduje bai je tarbar Tinubu ba a Kano'

Rashin ganin Ganduje yayin ziyarar ta Tinubu ya janyo dasa ayar tambaya cewa ko tsohon gwamnan na Kano ya samu rashin jituwa da shugaban ƙasar bayan sauke shi daga muƙaminsa na shugaban jam'iyyar APC mai mulki.

Sai dai sanarwar da makusancinsa Muhammad Garba ya fitar, ta ce Ganduje bai je tarbar shugaban ƙasa Bola Tinubu ba a Kano ranar Juma'a ba saboda balaguron da ya yi zuwa birnin Landan.

Ganduje wanda ya sauka daga shugabancin jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a watan Yuni ya shirya tafiyar ne kwana biyar kacal da saukarsa daga muƙamin, kamar yadda Muhammad Garba ya bayyana cikin wata sanarwa a ranar Asabar.

"Ba kamar abin da ake yaɗa wa ba cewa da gangan ya ƙi zuwa ko kuma ba shi da lafiya, Ganduje ya je Landan ne saboda tafiyar da aka shirya da daɗewa tun kafin ziyarar," in ji sanarwar.

Garba ya tabbatar cewa an sanar da Ganduje game da ziyarar shugaban ƙasar, "kuma ya yi niyyar zuwa amma duk ƙoƙarin da ya yi na sauya lokacin tashin jirginsa bai yi nasara ba".

"Sauka daga muƙamin da Ganduje ya yi bai shafi alaƙarsa da Tinubu ba ko kaɗan, wadda ta ginu tsawon shekaru cikin girmamawa da buƙata irin ta siyasa," a cewar Garba.

Garba wanda tsohon kwamashinan yaɗa labarai ne a gwamnatin Ganduje, bai bayyana abin da mai gidan nasa ya je yi Landan ba.

Tinubu bai je gidan Sarki ba

Bisa al'ada duk jihar da shugaban ƙasa ya ziyarta to yana zuwa fadar Sarkin garin kasancewarsu su ne iyayen ƙasa.

To sai dai kusan a karon farko wani shugaban ƙasa ya kai ziyara birnin Kano ba tare da ziyartar fadar Sarki ba.

Yanuz haka dai a Kano akwai mutaum biyu da ke kowa ke iƙrarin shi ne halastaccen sarki - Sarki na 15 Aminu Ado Bayero da Sarki na 16 Muhammaud Sanusi II.

Rikicin da ya dabaibaye masarautar jihar ta Kano mai ɗimbin tarihi ya soma ne a watan Mayun 2024, bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauke Sarki na 15 Aminu Ado Bayero da wasu sarakuna huɗu masu daraja ta ɗaya a jihar - inda ya mayar da Sarki na 16 Muhammadu Sanusi na II a matsayin sarki ɗaya tilo a jihar.

Wasu na ganin rashin ziyarar Tinubu zuwa kowacce fada daga cikin fadajin guda biyu da ke taƙaddama da juna ba zai rasa nasaba da ƙoƙarin shugaban na nuna rashin ɗaukar layi wanda hakan ka iya shafar siyasarsa.