Yadda mijina ya datse min hannu da wuƙa

Chinonso Echege, matar Mista Sunday Echege, wadda mijinta ya sare mata hannu a unguwar Ibagwa-Agu da ke ƙaramar hukumar Nsukka ta jihar Enugu, ta bayyana musabbabin faruwar lamarin.
A lokacin da BBC ta ziyarci asibitin da matar ke jinya, ta ce mijin nata ya yi yunƙurin sare mata kai ne da adda amma da ta yi ƙoƙarin kare kanta sai ya yi amfani da addar ya yanke mata hannu.
Yadda lamarin ya auku
Chinonso Echege ta ce wannan ba shi ne karon farko da mijinta ke lakaɗa mata duka ba.
"Mijina ya taɓa yi min duka, sai na gudu, na ɗauki yarona na biyu a hannuna na gudu zuwa wurin mahaifina, na zauna a gidan mahaifina na tsawon shekara biyu.
"Mijina ya ƙona dukkan kayan ciki har da gadon da nake kwana a kai da duk wani abu da na mallaka."
"A ƙarshe ya zo gidan mahaifina, ya durƙusa ya roƙe ni in gafarta masa, cewa aikin shaiɗan ne, ya tuba, ba zai sake yin haka ba."
"Dangi na sun gaya masa duk abin da ya kamata ya yi, kuma ya yi, kuma a watan Satumba (2024) ne na dawo gidansa."
"Nan da nan ya fara nuna min rashin mutunci, ya ƙarar da duk kayan abincin da mu ke da shi, daga nan kuma sai ya soma duka na."
"Ba ya bari na amsa waya, ya fasa wayoyi na biyu ya kuma karya katin layin wayata."
"Na sayi wata waya, amma na barta a garinmu, sai ya ce idan bai ga wayar ba, sai ya halaka ni."
"Na gudu, na tafi wurin surukina."

"Lokacin da na dawo don na shirya zuwa coci, sai ya tare kofa ya daɓa min wuƙa.
"Ya yi ƙoƙarin sare min kaina amma da na yi ƙoƙarin kare kaina, sai ya kai min sara a hannu ya kuma yanke mun hannuna."
"Na je gidan wasu tsofaffin ma'aurata, da su ka ga abun da ya faru sai suka fara kururuwa suna kiran mutane su taimaka."
"Mijina ya gudu ya ɓuya a cikin daji, sai mutanen ƙauyen suka same shi suka miƙa shi ga ƴan sanda."
Chinonso ta ce addu'arta a yanzu ita ce ta samu lafiya domin ta koyi ɗinki maimakon haɗa buhunan siminti ta sayar kamar yadda ta ke yi kafin faruwar lamarin.
Abin da ya sa na sari matata

Mutumin mai suna Sunday Echege, wanda ya yanke hannun matarsa, ya shaida wa ƴan sanda cewa ya yi hakan ne saboda a tunaninsa tana lalata ne da wani mutum.
Daniel Ndukwe, kakakin Rundunar ƴan sandan Jihar Enugu, ya bayyana cewa a halin yanzu mutumin yana hannun su yayin da ake ci gaba da bincike.
Ya ce da taimakon al'umma ne suka kama mutumin, inda aka karɓe addar daga hannunsa aka kuma miƙa shi ga ƴansanda.
Matsalar cin zarafi tsakanin ma'aurata a Najeriya
Rahotannin cin zarafi tsakanin ma'aurata ya zama ruwan dare a Najeriya.
A ranar 21 ga watan Janairun shekarar 2025 ne wani mutum ya kwararawa matarsa man fetur sannan ya banka mata wuta a garin Abagana da ke jihar Anambra sakamakon rikici da ya kaure tsakaninsu.
Haka kuma an samu wani lamari a cikin watan Afrilun 2022 a jihar Ebonyi inda aka zargi wani mutum da dukan matarsa da ta haifa masa ƴaƴa bakwai .
Haka kuma rikicin cikin gida ne ya yi sanadin mutuwar shahararriyar mawakiyar nan Osinachi Nwachukwu .
Iyalanta sun yi zargin cewa dukan da mijin nata ya yi mata ne ya yi sanadiyyar mutuwar ta.
Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil'adama da dama sun yi kira ga gwamnati da ta tabbatar an hukunta waɗanda ke cin zarafin matansu domin a rage samun aukuwar irin waɗannan al'amuran.










