Inter Milan ta je ta rike Barcelona a Champions League

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

An tashi 3-3 tsakanin Barcelona da Inter Milan a wasan farko zagayen daf da karshe a Champions League da suka kara a Sifaniya ranar Laraba.

Inter Milan ce ta fara cin ƙwallo a daƙiƙa 30 da take leda ta hannun Marcus Thuram, ya zama na farko da ya ci ƙwallo a ƙanƙanin lokaci a daf da karshe a Champions League.

Daga nan Inter ta kara na biyu ta hannun Denzel Dumfries, wanda ya zama na farko daga Netherlands da ya ci ƙwallo ya kuma bayar aka zura a raga a daf da karshe a Champions League, tun bayan Wesley Sneijder a Inter a karawa da Barcelona.

Dumfries shi ne ya bai wa Thuram ƙwallon farko da Inter Milan ta zura a ragar Barcelona cikin ƙanƙanin lokaci.

Barcelona ta sa namijin ƙwazo a wasan, inda Lamine Yamal ya zare ɗaye a minti na 24 a wasan na hamayya.

Haka kuma ƙungiyar Sifaniya ta farke na biyun ta hannun Ferran Torres, bayan da Raphinha ya samar masa damar zura ƙwallon a cikin raga cikin sauƙi.

Ana tsaka da wasa Inter Milan ta kara na uku ta hannun Denzel Dumfries, sai dai minti biyu tsakani mai tsaron ragar Inter, Yann Sommer ya ci gida.

Kenan ta sanadin Raphinha, wanda shi ne ya buga tamaular - hakan ya sa ya yi kan-kan-kan da Cristiano Ronaldo, wanda yake da hannu a cin ƙwallo 20 a Champions League a 2013/14.

Raphinha, ɗan wasan tawagar Brazil, ya zura 12 a raga ya kuma yi sanadin cin tara a bana a babbar gasar tamaula ta nahiyar Turai.

Champions League

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Barcelona da Inter Milan sun fuskanci juna karo na 17 a babbar gasar zakarun Turai, inda ƙungiyar Sifaniya ta yi nasara takwas da canjaras shida aka doke ta wasa uku.

Barcelona ta yi wasa shida ba tare da an doke ta ba a gida a fafatawa da Inter Milan kenan a Champions League, wadda ta yi nasara biyar da canjaras ta biyu.

Kocin Inter Milan, Simone Inzaghi, ya ja ragamar wasa na 50 a Champions League, ya zama mai horarwa na bakwai daga Italiya da ya yi wannan ƙwazon.

Ranar Talata 6 ga watan Mayu, Inter Milan za ta karɓi bakuncin Barcelona a wasa na biyu zagayen daf da karshe a Champions League a Italiya.

Barcelona ta kawo wannan matakin bayan yin waje da Borussia Dortmund, ita kuwa Inter Milan ita ce ta fitar da Bayern Munich a zagayen kwata fainal.

Barcelona tana matakin farko a teburin La Liga da tazarar maki huɗu tsakani da Real Madrid ta biyu a kakar nan.

Ita kuwa Inter Milan tana ta biyun teburin Serie A da tazarar maki uku tsakani da Napoli mai jan ragamar babbar gasar tamaula ta Italiya.

Inter za ta karɓi bakuncin Verona a gasar Serie A ranar Asabar 3 ga watan Mayu, sannan ta kece raini da Barcelona a Italiya a Champions League ranar Talata.

Barcelona kuwa za ta je gidan Valladolid a gasar La Liga ranar Asabar 3 ga watan Mayu, sannan ranar Talata ta ziyarci Inter a wasa na biyu a Champions League.