Gyokeres zai iya komawa Man United, Arsenal na son Rogers

Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan gaba na Sporting Viktor Gyokeres a shirye yake ya sake haduwa da Ruben Amorim a Manchester United, Arsenal ta saka dan wasan Aston Villa dan kasar Ingila Morgan Rogers, mai shekara 22, da kuma dan wasan gaban Brazil Igor Paixao, mai shekara 24, wanda ke taka leda a Feyenoord, cikin jerin wadanda za su nema a bazara. (Times)

Dan wasan gaban Sporting dan kasar Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 27, yana shirye ya sake haduwa da tsohon kociyan kungiyar Ruben Amorim a Manchester United. (Talksport)

Arsenal ta saka dan wasan Aston Villa dan kasar Ingila Morgan Rogers, mai shekara 22, da kuma dan wasan gaban Brazil Igor Paixao, mai shekara 24, wanda ke taka leda a Feyenoord, cikin jerin wadanda za su nema a bazara. (Times)

Brentford ta ki amincewa da tayin farko da Manchester United ta yi na neman dan wasan Kamaru Bryan Mbeumo. An yi imanin kulob din na Old Trafford ya yi tayin fan miliyan 45, sai dai Bees na son sama da fan miliyan 60 kan dan wasan mai shekara 25. (Independent)

Tottenham za ta biya babban kocinta Ange Postecoglou fam miliyan 4 a matsayin diyya idan ta yanke shawarar korar dan kasar Australian mai shekaru 59. (Telegraph)

Dan wasan Isra'ila Manor Solomon, mai shekara 25, yana shirin samun dama ta biyu a Spurs bayan da ya taka rawar gani a inda ya je aro wato Leeds a bara. (Sun)

Dan wasan Borussia Dortmund dan kasar Ingila Jamie Gittens, mai shekara 20, shine babban wanda Chelsea ke zawarcin a bazara. (Sky Sports)

Kocin Bayer Leverkusen Erik ten Hag na bibiyar dan wasan gaban Manchester United Antony mai shekaru 25, wanda ya kawo Old Trafford (Sky Germany)

Kulob din Al-Hilal na Saudi Arabiya ya yi wa Napoli tayin fan miliyan 55 don sayen dan wasan gaba na Najeriya Victor Osimhen. (Fabrizio Romano)

Manchester City na gab da kulla yarjejeniya da Wolves don siyan dan wasan baya na Algeria Rayan Ait-Nouri mai shekaru 23. (ESPN)

Arsenal na sha'awar sayen dan wasan gaban Real Madrid dan kasar Brazil Rodrygo, mai shekara 24. (Sky Sports)

Dan wasan bayan Inter Milan da Italiya Francesco Acerbi, mai shekara 37, na iya bin tsohon kocin kungiyar Simone Inzaghi zuwa kulob din Al-Hilal na Saudiyya. (Florian Plettenberg)