Me ya sa ake ce-ce-ku-ce kan sauya kundin tsarin mulkin Najeriya?

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu

Asalin hoton, STATE HOUSE

    • Marubuci, Ibrahim Haruna Kakangi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
    • Aiko rahoto daga, Abuja
  • Lokacin karatu: Minti 6

Muhawara ta sake kaurewa a Najeriya game da buƙata ko rashinta ta sauya kundin tsarin mulkin ƙasar.

Lamarin ya sake tasowa ne bayan buƙatar da wasu mashahuran mutane a ƙasar suka gabatar wa shugaban ƙasar Bola Tinubu a wata ziyara da suka kai masa ranar Juma'a.

Tawagar ƙarƙashin jagorancin tsohon babban sakataren ƙungiyar ƙasashe renon Ingila (Commonwealth), Cif Emeka Anyaoku, ta shawarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da ya ɗauki matakin samar da sabon kundin tsarin mulkin ƙasar.

Najeriya na amfani ne da rubutaccen kundin tsarin mulki, wanda matakan sauya shi ke da tsauri.

Kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, wanda aka yi wa gyaran fuska, ya tanadi tsari ne na tarayya, inda ya raba ƙarfin iko tsakanin matakan mulki uku, wato gawamnatin tarayya da na jiha da kuma na ƙananan hukumomi.

Wannan ne ya sa wasu ke ganin cewa ɗauko batun yin gyara ga kundin tsarin mulkin a wannan lokaci tamkar jajibo wani jan aiki ne.

Sai dai ɗaya daga cikin ƴan tawagar da suka gabatar wa shugaba Tinubu da shawarar sauya kundin, Kwamared Shehu Sani, ya ce: "mun bai wa Tinubun shawarwarin ne ganin (kundin tsarin mulkin) na daga cikin abubuwan da ke haifar wa ƙasar matsala maimakon magance ta."

Sai dai jim kaɗan bayan haka ne lamarin ya fara samun martani daga al'umma da kuma ƙungiyoyi.

A martanin da ya mayar, ɗaya daga cikin fitattun mutane a ƙasar kuma tsohon ɗan siyasa, Alhaji Tanko Yakasai ya buƙaci shugaban ƙasa ya yi taka-tsantsan da shawarwarin da ƙungiyar ta ba shi.

Ya ce: "ba a bi ƙa'idojin da suka dace ba wajen gabatar da wadannan shawarwari ga shugaban ƙasa."

A cewar Yakasai, akwai buƙatar tattaunawa sosai da tuntuɓa kafin ɗaukan mataki irin wannan mai muhimmanci ga ƙasa.

A gefe guda kuma wasu na da ra'ayin cewa akwai matsalolin da ke addabar ƙasar, waɗanda aka fi buƙatar mayar da hankali a kai fiye da batun sauya kundin tsarin mulkin Najeriya.

'Ba kundin tsarin mulki ne matsalar ba'

Wani masanin siyasa a Najeriya, Farfesa Kamilu Sani Fagge, ya ce an daɗe ana samun irin waɗannan kiraye-kiraye.

Kuma ya ce wani yunƙuri ne da ake yi na ganin an sake fasalin yadda ake tafiyar da mulkin Najeriya.

Ya ce wasu al'ummar Najeriya na kallon cewa "kundin tsarin mulkin Najeriya ba halastacce ba ne saboda sojoji ne suka yi shi.

"Don haka wannan wani yunƙuri ne na fito da siyasar ɓangarenci, wanda aka samu damar yi a yanzu," in ji farfesa Kamilu a wata tattaunawa da BBC.

"Jama'ar Najeriya ba tsarin mulki ne ya dame su ba, abin da suke fama da shi yanzu shi ne yunwa, talauci da rashin tsaro, kuma su ne ya kamata a duba."

Ko a martanin da ya bayar a lokacin da ya karɓi baƙuncin waɗanda suka gabatar da shawarar yin gyara ga kundin tsarin mulkin, shugaba Bola Tinubu ya ce babban "abin da na fi mayar da hankali a kai yanzu shi ne yadda za mu gyara tattalin arziƙi."

Yadda tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya samo asali

A ranar 29 ga watan Mayun 1999 ne tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya fara aiki, bayan amincewa da shi a ranar 5 ga watan Mayun shekarar.

Akasarin abubuwan da kundin tsarin mulkin na 1999 ya ƙunsa sun samo asali ne daga kundin tsarin mulkin shekarar 1979, wanda ya fara amfani a farkon jamhuriya ta biyu.

Kundin tsarin mulkin na 1979 shi ne ya yi watsi da tsarin tafiyar da gwamnati irin na Firaiminista inda ya aro tsarin tarayya irin na ƙasar Amurka.

An yi hakan ne domin kauce wa rikita-rikitar da aka samu a lokacin jamhuriya ta farko, inda aka yi amfani da tsari irin na Birtaniya.

Me doka ta ce kan sauya kundin tsarin mulkin Najeriya?

Majalisar dokokin Najeriya

Asalin hoton, NATIONAL ASSEMBLY

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sashe na 9 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ne ya bayar da damar yin gyara ga kundin tsarin mulkin ƙasar.

Najeriya ta aro tsarin tafiyar da mulkinta da kuma na yin gyara ga kundin tsarin mulki ne daga ƙasar Amurka.

Sashen ya tanadi cewa za a iya gabatar da batun yin gyara ga kundin tsarin mulki ta hanyar hanyar samun goyon bayan kashi biyu cikin uku na wakilan Majalisar dattijai da kuma wakilan majalisar wakilan tarayya, ta hanyar kaɗa ƙuri'a.

A irin wannan hali, kundin tsarin mulki ya ce ne ’yan majalisa za su nuna amincewa ne ko akasin haka ta hanyar kada kuri’a a zauren majalisa, ba ta amfani da murya ba, wanda wasu za su iya amfani da damar wajen cimma wasu muradu na daban.

Sai dai akwai wasu sassa biyu na kundin tsarin mulkin waɗanda su kuma idan za a yi musu gyara dole ne sai an samu amincewar kashi huɗu cikin biyar na ƴan majalisar dokokin tarayya da kuma ƴan majalisar dokokin jihohi.

Waɗannan sassa su ne: Babi na huɗu na kundin tsarin mulkin Najeriya, wanda ya yi magana kan ƴancin ɗan ƙasa.

Sai kuma sashe na takwas na kundin tsarin mulkin, wanda ya yi magana kan ƙirƙirar sabbin jihohi.

Matakan yin gyara ga kundin tsarin mulkin Najeriya

Gabatar da ƙuduri

Za a iya fara batun yin gyara ga kundin tsarin mulkin Najeriya ne ta hanyar gabatar da ƙudurin doka a zauren majalisar dokoki.

Waɗanda za su iya gabatar da ƙudurin gyara ga kundin tsarin mulkin Najeriya su ne shugabanni ko kuma wakilan majalisar tarayya.

Akwai kuma shugaban ƙasa ko alƙalin alƙalai na tarayya ko wani jami'in gwamnati.

Sai kuma ƙungiyoyin fafaren hula ta hannun ɗan majalisar wakilan tarayya ko na majalisar dattijai.

Muhawara a majalisar dokokin tarayya

Majalisar dokokin tarayya za ta amshi ƙudurin, ta yi masa karatu na farko da na biyu da na uku tare da tura wa kwamitin majalisar kan kundin tsarin mulkin ƙasawa domin dubawa da amincewa.

Haka nan majalisar za ta gudanar da zaman jin ra'ayin jama'a kan gyaran.

Miƙa wa majalisun dokokin na jihohi

Idan har aka samu amincewar kashi biyu cikin uku na kowane zauren majalisar dokoki (wato majalisar wakilai da majalisar dattijai) daga nan sai a miƙa dokar zuwa ga majalisun dokokin jihohi domin yin nazari a kai.

Majalisun dokokin jihohi za su tattauna tare da yin muhawara game da ƙudurin sauyi ga kundin tsarin mulkin.

A wannan matakin ma ana buƙatar samun amincewar mafi rinjayen wakilai a majalisar dokokin kowace jiha.

Haka nan wajibi ne a samu amincewar kashi uku cikin huɗu na jimillar majalisun jihohin Najeriya 36.

Hakan na nufin dole ne a samu amincewar majalisun jihohi aƙalla 24, kafin a ayyana ƙudurin a matsayin wanda ya zama doka.

Amincewa

Da zarar aka samu duk amincewar da ake buƙata a majalisun jihohi, za a mayar wa Majalisar dokokin tarayya da ƙudurin, kuma ya zama doka.

Sai dai akwai ruɗani guda ɗaya; akwai bambancin ra'ayi game da cewa ko idan aka gama bin duk matakan da aka ambata, a ƙarshe dole sai an miƙa wa shugaban ƙasa dokar domin sanya hannu ko a'a.

Wasu na ganin cewa da zarar aka amince a dukkanin matakai da kuma aka cika duk ƙa'idoji, to dokar za ta fara aiki kai-tsaye, sai dai wasu na ganin cewa ana buƙatar shugaban ƙasa ya sanya mata hannu kafin ta fara aiki.

Ƙa'idojin yin gyaran kundin tsarin mulki

  • Da zarar ƙudurin yin gyara ga kundin tsarin mulkin ya samu rashin amincewa ko naƙasu a kowane mataki, za a yi watsi da shi sannan a sake ɗauko matakin tun farko.
  • Yin gyara ga kundin tsarin mulki ba zai zarce wa'adin majalisa ba; saboda haka da zarar wa'adin majalisa ya kai ƙarshe, ba za a iya ɗorawa kan gyaran a majalisa ta gaba ba, kuma duk wani mataki da aka biyo a baya ya riga ya warware.

Tare da gudumawar Dr. Sulaiman Santuraki (Masanin shari’a a Najeriya).

Ƙarin labarai daga BBC Hausa: