Najeriya ta naɗa Éric Chelle a matsayin kocin Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF ta naɗa tsohon kocin tawagar Mali, Éric Sékou Chelle, a matsayin kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles.
Chelle mai shekara 47 ya jagoranci Mali har zuwa zagayen kwata fayinal a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2023 a Ivory Coast, kafin mai masaukin baƙi ta doke su.
NFF ta ce ta amince da naɗin nasa ne bayan kwamatinta na musamman ya bayar da shawarar yin hakan a yau Talata.
"Kocin zai fara aiki nan take, kuma zai mayar da hankali wajen sama wa Najeriya nasara a wasannin neman shiga gasar Kofin Duniya ta 2026," in ji NFF cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata da dare.
Sai dai ba ta bayyana tsawon kwantaragin da ta ƙulla yarjejeniya da shi ba.
Naɗin nasa na zuwa ne bayan NFF ta kasa daidaitawa da Bruno Labbadia ɗan ƙasar Jamus game da batun biyan haraji bayan sanar da ba shi aikin a watan Agustan 2024.
Kafin naɗin nasa, shugaban NFF Ibrahim Musa Gusa ya faɗa wa manema labarai cewa sabon kocin da za su bai wa aikin shi ne zai jagoranci tawagar Super Eagles ta 'yanwasan cikin gida zuwa gasar kofin Afirka ta CHAN - wadda ake gudanar da wasannin neman gurbi a yanzu.
Kociyan ya taka wa ƙasarsa Mali leda sau huɗu, a cewar sanarwar NFF, kuma ya jagoranci kulob da dama a sana'arsa.











