Akwai yiwuwar Saka zai dawo wasa cikin mako mai zuwa

Bukayo Saka pictured in an Arsenal training session

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Bukayo Saka bai yi wasa ba tun daga watan Disamba sanadiyyar rauni
    • Marubuci, Sami Mokbel
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Senior football correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 1

Akwai yiwuwar dan wasan gaba na Arsenal, Bukayo Saka zai shiga jerin wadanda za su buga wasa a karawar da kungiyar za ta yi da Fulham cikin mako mai zuwa.

Rabon Saka da buga wasa tun watan Disamban bara sanadiyyar rauni da ya samu a karawar da kungiyarsa ta yi da Crystal Palace, lamarin da ya kai yi masa tiyata a kafa.

Saka ya samu waraka kamar yadda aka tsara kuma tuni ya koma atisaye gadan-gadan.

To sai dai Arsenal na yin kaffa-kaffa da batun komawarsa wasa gadan-gadan, amma ana tunanin kungiyar za ta yanke hukunci kan lamarin gabanin wasan da za ta buga a ranar Talata.

In dai ba wani abu ne ya sauya ba akwai kwakkwarar alamar cewa dan wasan zai taka leda a karawar da za a yi tsakanin kungiyarsa ta Arsenal da Real Madrid a zagayen kwata-fainal cikin watan Afurilu.

A makon da ya gabata ne BBC ta ruwaito cewa

Arsenal ta shirya tsaf domin tattaunawa domin tsawaita kwantaragin dan wasa wanda yanzu haka kwantaragin nasa ta shiga shekara biyu na karshe.