Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Messi da Ronaldo za su je gasar kofin duniya karo na shida kowanne
Tawagar Argentina da ta Portugal za ta buga gasar cin kofin duniya da za a yi a baɗi a Amurka da Canada da kuma Mexico, karo na shida da Lionel Messi da Cristiano Ronaldo za su je gasar kowannensu.
Ranar Juma'a 5 ga watan Disambar 2025 aka raba jadawalin gasar a birnin Washington DC da tawaga 48 za ta kece raini daga 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2026.
Wannan ce gasa ta 23, sannan fafatawa 104 za a yi, bayan da aka raba rukuni zuwa 12 ɗauke da kasa hurhuɗu kowanne.
Argentina, wadda take riƙe da kofin da ta lashe a 2022 tana rukuni na 10 da ya haɗa da Algeria da Austria da kuma Jordan.
Ita kuwa Portugal tana rukuni na 11 da ya ƙunshi Uzbekistan da kuma Colombia da gurbi ɗaya da aka baiwa wadda za ta yi wasan cike gurbi daga nahiyar Turai.
Messi da Ronaldo za su buga gasar cin kofin duniya karo na shida kowanne, kenan sune kan gaba da za su kafa wannan tarihin a babbar gasar tamaula ta duniya.
Amma dai Messi ne a matakin farko a yawan buga wasanni a kofin duniya, mai 26, wanda ya halarci gasar a 2006 da 2010 da 2014 da 2018 da kuma 2022.
Wanda yake na biyu shi ne Lothar Matthaus da ya yi fafatawa 25 a gasar kofin duniya da ya wakilci Jamus a 1982 da 1986 da 1990 da 1994 da kuma 1998.
Na uku shi ne ɗan ƙwallon Jamus, Miroslav Klose mai wasa 24 a gasar kofin duniya da ya buga a 2002 da 2006 da 2010 da kuma 2014.
Paolo Maldini na Italiya ne na huɗu mai karawa 23 a gasar da ya buga a 1990 da 1994 da 1998 da kuma 2002.
Cristiano Ronaldo ne a mataki na biyar mai wasa 22 da ya je gasar kofin duniya a 2006 da 2010 da 2014 da 2018 da kuma 2022.
Tsakanin Ronaldo da Messi sun ci ƙwallo sama da 800 kowannensu a ƙungiyoyi da tawaga da lashe Champions League tara da Ballon d'Or 13 tsakaninsu.
Gasar cin kofin duniya da za a buga a baɗi, Ronaldo zai cika shekara 41 da haihuwa, shi kuwa Messi zai cika mai shekara 39, kuma gasar karshe da dukkansu za su halarta.
Messi dai ya lashe kofin duniya a 2022 a Qatar, kuma ƙyaftin ɗin Argentina shi ne kan gaba a yawan buga wa kasar wasa har 196 da ci mata ƙwallo 115.
Shi kuwa Ronaldo ƙyaftin din tawagar Portugal ya ci ƙwallo 954 ciki har da 143 a kasarsa a karawa 226 da ya yi.
Gasar kofin duniya ta 2006 da aka yi Jamus
Cristiano Ronaldo yana da shekarun haihuwa 21, shi kuma Messi ya kusan kaiwa 19 a lokacin da suka fara buga wa kasashensu gasar cin kofin duniya kuma a matakin matasa masu ƙarancin shekaru da aka gudanar a Jamus.
Messi bai buga zagayen kwata fainal ba, inda Jamus mai masaukin baƙi ta fitar da Argentina.
A washe gari ne Ronaldo ya ci fenaritin da suka waje da Ingila, amma daga baya Faransa ta cire su a zagayen daf da karshe.
Gasar kofin duniya da aka yi a Afirka ta Kudu a 2010
Ƙyaftin ɗin Portugal, Ronaldo ya ci ƙwallo tilo a gasar da Afirka ta Kudu ta shirya daga baya suka yi rashin nasara a hannun wadda ta lashe kofin Sifaniya a zagayen ƴan 16.
Shi kuwa Messi bai ci ƙwallo ko ɗaya ba a gasar da Jamus ta yi waje da su karo na biyu a jere.
Daga nan ne aka yi ta caccakar Messi, wanda ke taka leda a Barcelona da cewar ya fi mayar da hankali da ƙwazo a ƙungiyar Sifaniya fiye da kasarsa.
Gasar kofin duniya da aka yi a Brazil a 2014
Portugal ba za ta mance da gasar kofin duniya ba da Brazil ta shirya, domin Ronaldo ya yi wa rayuwarsa ta tamaula ganganci, bayan da ya je gasar da raunin gwiwa.
Sai dai kuma ya ci ƙwallo ɗaya, waɗanda aka fitar da su a karawar cikin rukuni.
Messi a lokacin da ya ɗaura ƙyallen ƙyaftin a Argentina, ya nuna kansa a gasar, wanda ya ci ƙwallo a kowanne wasan cikin rukuni da lashe ƙyautar fitatcen ɗan ƙwallo karo huɗu a jere a Brazil
Koda yake Argentina ta yi rashin nasara a wasan karshe a hannun Jamus, amma cikin kuka Messi ya lashe ƙyautar ƙwallon zinari, bayan takaicin kasa ɗaukar kofin.
Shekara biyu bayan kammala gasar kofin duniya, Argentina ta kasa cin Copa Amrica da Copa America Centenario duk a hannun Chile a bugun fenariti.
Daga nan ne Messi ranshi ya ɓaci har ya sanar da cewar ya yi ritaya daga buga wa Argentina tamaula, daga baya aka rarrashe shi ya kuma hakura ya koma da taka mata leda.
Gasar kofin duniya da aka yi a 2018 a Rasha
Tawagar Argentina da ta Portugal duk sun sha kashi a wasannin zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya a Rasha. Messi ya ci ƙwallo ɗaya a wasan cikin rukuni daga baya Faransa ta yi waje da su a zagayen ƴan 16.
Shi kuwa Ronaldo, wanda ya lashe kofin nahiyar Turai tare da Portugal shekara biyu kafin gasar cin kofin duniya ya ci ƙwallo uku rigis a wasan farko a cikin rukuni da suka tashi 3-3 da Sifaniya a Rasha.
Sai dai ya ɓarar da fenariti a karawa da Iran daga baya Portugal ta yi rashin nasara a zagaye na biyu a hannun Uruguay.
Shekara ɗaya da kammala gasar kofin duniya a Rasha da Faransa ta lashe, Ronaldo ya bayar da gudunmuwar da Portugal ta ɗauki Nations League, har da cin ƙwallo uku rigis a fafatawar daf da karshe.
Gasar cin kofin duniya da aka yi a 2022 a Qatar
Portugal ta taka rawar gani a gasar da aka yi a Qatar, amma ba don ƙwazon Ronaldo ba, wanda ya koma zaman benci da aka shiga zagayen ziri ɗaya ƙwale, daga baya aka yi waje da kasar a ƙwata fainals.
Shi kuwa Messi ya ɗauki alhakin jan ragamar Argentina tun daga lokacin da aka fara gasar har ranar karshe.
Messi sai da ya zama ɗan wasan da ya ci ƙwallo a dukkan zangon wasannin a gasar cin kofin duniya, mai bakwai a raga tun daga fara ta zuwa rufe labulenta.
Haka kuma har guda biyu ya zura a ragar Faransa da cin fenaritin farko da ta kai sun lashe kofin da cin 4-2.
Daga nan ne Messi ya faɗa zuciyar ƴan Argentina suka ƙaunace kamar yadda suka yi wa Maradona, bayan ɗaukar wa kasar babban kofin tamaula na duniya.
Ana kammala wasannin Qatar a 2022, kai kace ita ce gasar karshe da Messi da Ronaldo suka halarta - to sai dai gashi sun kuma sa ƙwazon da za su sake wakitar kasashensu a gasar kofin duniya a Amurka da Canada da kuma Mexico.
Shi dai Messi ya ce zai buga gasar ne domin ya bayar da gudunmuwar da za su kare kofin da yake hannunsu, shi kuwa Ronaldo na fatan lashe kofin a karon farko a tarihi.
Tarihin da Ronaldo da Messi suka yi a kofin duniya
Cristiano Ronaldo:
- Ya halarci gasar kofin duniya karo biyar
- Ya ci ƙwallo takwas
- Ya bayar da biyu aka zura a raga
Lionel Messi:
- Ya je gasar kofin duniya sau biyar
- Ya ci ƙwallo 13
- Ya bayar da takwas aka zura a raga
- Ya lashe takalmin zinare karo biyu
- Ya ɗauki kofin duniya a 2022
Bajintar da suka yi bayan kowanne ya yi wasa 1,000
Lionel Messi:
- Ya zura ƙwallo 789 a raga
- Ya bayar da 348 aka zura a raga
- Ya lashe manyan kofuna 41
Cristiano Ronaldo:
- Ya ci ƙwallo 725
- Ya bayar da 216 aka zura a raga
- Ya ɗauki manyan kofuna 31