Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Waɗanne kasashe ne suka samu gurbi a gasar Kofin Duniya ta 2026?
A yanzu dai mafarkin Najeriya ya kare game da batun zuwa gasar kofin duniya ta 2026 bayan ta sha kashi a hannun Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo a ranar Lahadi.
Hakan na nufin cewa Najeriya ba za ta halarci mashahuriyar gasar ba karo na biyu a jere.
Croatia ta kasance ƙasa ta baya-bayan nan daga nahiyar Turai da ta samu gurbi a Gasar ta Kofin Duniya ta 2026 da za a yi a ƙasashen Amurka da Mexico da kuma Canada - Wace ƙasa za ta iya samun gurbi a wannan wata na Nuwamba?
Kawo yanzu ƙasashe 30 sun samu gurbi, da suka haɗa da Ingila da Faransa da Argentina mai riƙe da kofin da Cape Verde baƙin gasar da Jordan da kuma Uzbekistan.
Ya zuwa yanzu akwai gurabe 18 da suka rage a gasar, da yawa daga cikinsu kuma daga nahiyar Turai ne.
Scotland ta yi rashin nasara hannun Girka da ci 3-2 a ranar Asabar, inda za ta fafata a Denmark a ranar Talata domin daya daga cikinsu ta samu gurbi.
Yanzu haka maki ɗaya ke tsakanin Denmark ta ɗaya da Scotland ta biyu a rukucin C.
A nata ɓangaren, Wales na da damar ƙarewa a matsayi na ɗaya a rukunin J, amma tana buƙatar doke Macedonia tare da fatan Belgium ta yi rashin nasara a hannun Liechtenstein a wasansu na ƙarshe a cikin rukunin.
Ƙasashen Belgium da Portugal kowanensu zai iya samun gurbi idan ya yi nasara a wasan gaba.
Norway da Netherlands na da dama mai ƙarfi ta samun gurbi saboda yawan ƙwallayen da suka ci a wasannin neman gurbi.
Ƙasashe uku da za su karɓi baƙuncin gasar, Canada da Maxico da Amurka, duk sun samu gurabe kai-tsaye.
Australia da Iran da Japan da Jordan da Qatar da Saudiyya da Koriya ta Kudu duka sun samu gurabe daga yankin Asiya.
New Zealand ta samu gurbi guda ɗaya da aka ware wa yankin Oceania.
Daga nahiyar Afirka kuwa, Tunisiya da Morocco ne suka fara samun gurbi a gasar, daga baya kuma ƙasashen Aljeriya da Cape Verde da Masar da Ghana da Ivory Coast da Senegal da kuma Afirka ta Kudu - wadda za ta buga gasar karon farko tun 2010 da ta karɓi baƙuncin gasar.
A yankin Kudancin Amurka kuwa ƙasashen Brazil da Ecuador da Uruguay da Paraguay kuma Colombia na daga cikin ƙasashen yankin da suka samu gurbi ya zuwa yanzu.
Duk da cewa ƙasashen, Bolivia da New Caledonia ba su samu gurbi kai-tsaye ba, amma za su buga wasannin neman gurbi na nahiyoyi a watan Maris na 2026.
Ƙasashen da suka samu gurbin Gasar Kofin Duniya ta 2026
Masu masauƙin baƙi: Amurka, Canada da Mexico
Africa: Algeria, Cape Verde, Egypt, Ghana, Ivory Coast, Morocco, Senegal, Afirka ta Kudu da Tunisiya
Asia: Australia, Iran, Japan, Jordan, Qatar, Saudi Arabia, South Korea da Uzbekistan
Turai: Croatia, England da France
Oceania: New Zealand
Kudancin Amurka: Argentina, Brazil, Colombia, Ecuador, Paraguay da Uruguay
Ya tsarin wasannin neman gurbin yake?
Kowace ɗaya daga cikin hukumar ƙwallon ƙafa ta Fifa ta nahiyoyi na amfani da hanya ta daban domin tantance ƙasar da za ta samu gurbin Gasar Kofin Duniyar.
Oceania ne yanki ɗaya da ya kammala nasa wasan neman gurbin, wanda dama gurbi ɗaya aka tanadar masa.
Daga cikin tawagogi 48 da za su halarci gasar, tuni aka ware wa kasashe ukun da za su karɓi baƙuncin gasar gurabe, sai kuma gurabe 43 da sauran ƙasashen duniya za su samu ta hanyar samun gurbi kai-tsaye, daga nahiyoyin duniya shida.
Sai kuma ragowar gurabe biyu da za a samu ta hanyar buga wasannin cike gurbi tsakanin nahiyoyin.
Nahiyar Turai
Guraben da aka ware wa nahiyar: 16
Ƙasashen da suka samu gurbi kawo yanzu: Croatia, Ingila, Faransa
An raba ƙasashen nahiyar zuwa rukuni 12, waɗanda suka ƙare a mataki na ɗaya a kowane rukuni za su samu gurbi kai-tsaye don zuwa gasar.
Su kuma ƙasashe 12 da suka ƙare a mataki na biyu a rukunonin, za su buga wasannin cike gurbi, tare da ƙasashe huɗu da suka fi yawan maki a matakin rukuni na gasar Uefa Nations League da ba su samu gurbin zuwa Kofin Duniyar ba.
A cikinsu ne za a tantance ƙasashe huɗu da za su samu ƙarin guraben nahiyar Turai a Gasar Kofin Duniyar.
Turai ce kawai nahiyar ba ta da wakilci a gasar cike gurbi ta nahiyoyi.
Kudancin Amurka
Guraben da aka ware wa nahiyar: Shida, da ƙasa ɗaya da za ta buga gasar cike gurbi ta nahiyoyi
Ƙasashen da suka samu gurbi: Argentina, Brazil, Colombia, Ecuador, Paraguay da kuma Uruguay
Wadda za ta je gasar cike gurbi ta nahiyoyi: Bolivia
Yankin Asia
Guraben da aka ware wa nahiyar: Takwas, da ƙasa ɗaya da za ta buga gasar cike gurbi ta nahiyoyi.
Ƙasashen da suka samu gurbi: Australia, Iran, Japan, Jordan, Qatar, Saudi Arabia, South Korea da Uzbekistan
Ƙasashen UAE da Iraƙi za su kara tsakaninsu don tantance wadda za ta je gasar cike gurbi ta nahiyoyi.
Nahiyar Afirka
Guraben da aka ware wa nahiyar: Tara, da ƙasa ɗaya da za ta buga gasar cike gurbi ta nahiyoyi.
Ƙasashen da suka samu gurbi: Algeria, Cape Verde, Egypt, Ghana, Ivory Coast, Morocco, Senegal, Afirka ta Kudu da Tunisiya.
Kasar da za ta je gasar cike gurbi ta nahiyoyi: DR Congo
Arewaci da tsakiyar Amurka da yankin Caribbean
Guraben da aka ware wa yankunan: Shida (ciki har da ukun da za su karɓi baƙunci), da ƙasashe biyu da za su buga gasar cike gurbi ta nahiyoyi.
Ƙasashen da suka samu gurbi: Canada, Mexico da Amurka, waɗanda suka samu kai-tsaye.
Yankin Oceania
Guraben da aka ware wa yankin: Ɗaya, da ƙasa ɗaya da za ta buga gasar cike gurbi ta nahiyoyi.
Ƙasar da ta samu gurbi: New Zealand
Ƙasar New Caledonia, za ta buga gasar cike gurbi ta nahiyoyi - wadda ta ƙunshi ƙasashe daga Afirka da Asia da kudancin Amurka da Arewacin Amurka.