Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Manyan abubuwa da suka ɗauki hankali game da gasar Kofin Duniya ta 2026
A ranar 5 ga watan Disamba ne za a rarraba rukunnan gasar Kofin Duniya ta 2026 da za a buga a birnin Washington DC, inda tuni magoya bayan ƙasashen da suka samu gurbi suka fara hanƙoron ganin yadda za ta kaya.
Sai dai ƙasashen India da China da Indonesia da Pakistan da Nigeria - ƙasashe biyar cikin shida da suka fi yawan mutane a duniya - ba su samu gurbin shiga gasar ba, wadda ƙasashen Amurka da Canada da Mexico za su ɗauki nauyi.
Daga cikin ƙasashen duniya 209 da suka fafata wasannin neman gurbi, guda 64 ne kacal suke da damar shiga gasar, sannan lambar za ta ragu zuwa 48 bayan wasannin cike-gurbi da za a buga.
Idan babu ƙasarka a gasar, wace ƙasa za ka mara wa baya?
Ƙananan ƙasashe
Ƙasar Curacao ce ƙasa mafi ƙanƙanta da ta samu gurbin shiga gasar cin kofin duniya, kasancewar mutanenta ba su wuce 155,000 ba.
Kusan duk ƴan ƙasar, wadda ke kusa da gaɓar Venezuela za su iya shiga cikin filin wasan da za a buga wasan ƙarshe mai suna MetLife a birnin New Jersey mai ɗaukar mutum 82,000.
Haka kuma mai horar da tawagar ƙasar Dick Adovocaat mai shekara 78 zai kasance koci mafi tsufa a gasar.
Kafin samun nasarar ta Curacao, Cape Verde ta kasance mafi ƙanƙanta ta biyu da ta shiga gasar, ƙasar da ta samu gurbi bayan doke Eswataini da ci 3 da nema a watan jiya, inda ta ƙara a matsayin ƙasa ta farko a rukuninta, sama da Kamaru.
Ƙasashen da za su buga gasar a karon farko
Uzbekistan an fara samun labarin ƙwallon ƙafa a ƙasar ne bayan wata ƙungiya a ƙasar Bunyodkor ta ɗauki ɗanwasan gaban Brazil Rivaldo a shekarar 2008 a daidai lokacin wani tsohon ɗan wasan na Brazil Zico yake shirin karɓar aikin horar da ita.
Duk da cewa bai daɗe a ƙungiyar ba, tun daga lokacin harkar ƙwallo take ci gaba da haɓaka, inda har ƙasar ta kai matakin wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin nahiyar Asia a 2011.
Wannan karon ƙasar ta samu gurbin zuwa gasar cin kofin duniya a karon farko, inda za ta je a ƙarƙashin horarwas tsohon ɗan wasan Italiya Fabio Cannavaro.
Jordan tawagar ta samu tikitin shiga gasar ne a karon farko bayan ƙasar ta doke Oman da ci 3 da nema a watan Yuni.
Kocin tawagar, wanda ɗan asalin ƙasar Morocco ne, Jamal Sellami ya sadaukar da nasarar samun gurbin "ga waɗanda suka yarda da mu."
Haiti
Kocin Haiti mai shekara 52 Sebastien Migne wanda ɗan asalin ƙasar Faransa ne bai taɓa zuwa ƙasar ba kafin ya karɓi ragamar da horar da tawagar ƙasar kimanin wata 18 da suka gabata.
Kusan miliyan 1.3 ne rikice-rikice suka raba da muhallinsu a ƙasar, sannan aka kashe dubbai.
Gasar cin kofin duniya ta ƙarshe da aka ga Haiti ita ce wadda aka buga a shekarar 1974.
Ya ce yana fata ƴanwasansa su zama wakilan ƙasar na gari ta hanyar nuna bajinta da ƙwarewa a gasar.
Ƙasashen da ke fata
Wata ƙasa da ita ma take fama da rikice-rikice ita ce ƙasar DR Congo, wadda ta yi kusan shekara 30 tana fuskantar matsaloli daban-daban na cikin gida.
Ita ma rabon da a ganta a gasar cin kofin duniya tun a 1974, inda yanzu za ta fafata da ko dai Jamaica ko New Caledonia domin samun gurbin shiga gasar.
Ita ma Iraq wata ƙasa ce da ke sa ran zuwa gasar idan ta samu nasara a wasannin cike-gurbi. Ta samu damar buga wasannin cike-gurbin ne bayan ta doke Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
Iraq ta taɓa zuwa gasar cin kofin duniya shekara 39 da suka gabata.
New Caledonia, wata ƙasa ce mai ƙarama, wadda mutanenta kusan 250,000 ne. Amma ita ma tana sa ran zuwa gasar ta hanyar buga wasannin cike-gurbi.
Za ta fafata ne da ƙasar Jamaica, idan ta samu nasara kuma sai ta fafata da ƙasar DR Congo, sannan a samu wadda za ta shiga gasar a cikinsu.
Sai kuma ƙasar Suriname wadda ita ma take fata za ta samu shiga gasar kasancewar tana cikin ƙasashen da za su fafata wasannin cike-gurbi da za a yi.