Matar da mijinta ya ɗaure a daji tsawon wata ɗaya ba tare da abinci ba

Lalita Kayi kenan lokacin da 'yan sanda ke taimakonta a jihar Maharashtra state.
    • Marubuci, Geeta Pandey & Cherylann Mollan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
    • Marubuci, Mushtaq Khan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Marathi
  • Lokacin karatu: Minti 4

Ana cike da mamaki da ta’ajibi, kan Ba'amurkiyar da aka gano ɗaure cikin sarƙa a jikin wata bishiya cikin dokar daji, tana ihu da kururuwar neman ɗauki a jihar Maharashtra da ke yammacin Indiya.

An gano Lalita Kayi, mai shekara 50, a makon da ya wuce, a surƙuƙun dajin da ke gundumar Sindhudurg, bayan ta yi ta ihu da kururuwar neman ɗauki inda wani makiyayi ya jiyo ta, tare da shaida wa jami'an tsaro, su kuma suka yi nasarar kuɓutar da ita.

An garzaya da Ms Kayi - wadda ta fita daga hayyacinta - zuwa asibiti. Tun daga lokacin yanayin lafiyarta ke ƙara inganta.

A ranar Juma'a aka mayar da ita asibitin masu lalular ƙwaƙwalwa domin tabbatar da lafiyarta kamar yadda likitoci suka shaida wa BBC.

Kamar yadda ta bayyana wa 'yan sanda, Ms Kiya ta zargi mijinta da ɗaure ta cikin sarƙa, ya kuma tsere ya bar ta ita kaɗai cikin matsananciyar yunwa a tsakar daji domin ta mutu.

'Yan sanda sun ce suna neman mijin nata - wanda ke kudancin jihar Tamil Nadu, kamar yadda matar ta shaida musu.

Sai dai kwanaki bakwai bayan ceton Ms Kayi, har yanzu ana ta kokarin gano ainahin abin da ya faru.

Kayi kenan lokacin da aka fito da ita daga dajin
Bayanan hoto, Ms Kayi na cikin mawuyacin hali lokacin da aka ɗauko ta a kan gadon ɗaukar marasa lafiya

Makiyayin - da ya gano ta a makon da ya wuce mai suna Pandurang Gawkar - ya shaida wa sashen BBC Marathi cewa yana tsaka da kiwon shanunsa a cikin dajin, sai ya ji muryar mace tana ƙwala ihu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Muryar na fitowa daga cikin dajin, ɓangaren inda tsaunuka suke. Da na isa wurin, sai na ga an ɗaure ɗaya daga cikin ƙafafunta a jikin bishiya kamar wata dabba. Tana ihu kamar dai dabba, nan da nan na kira mutanen ƙauyen da kuma 'yan sanda."

'Yan sanda sun ce sun gano kwafin fasfon matar, wanda ya nuna ita 'yar asalin Amurka ce, da katin shaida na musamman da ya nuna mijinta Ba'indiye ne, da adireshin gidanta a jihar Tamil Nadu.

Sun kuma gano wayar salula a tare da ita, da kwamfiyutar hannu, da kuɗi Rufin Indiya 31,000 kwatankwacin dalar Amurka 370, lamarin da ya kawar da shakkun zargin an yi niyyar mata sata ne.

Mazauna yankin sun ce, matar ta auna arziki da har makiyayin ya je ɓangaren tsaunin da take domin kiwo, sakamakon wuri ne mai cike da sarƙaƙiya da hatsarin gaske, dalilin da ya sa ta jima tana neman taimako babu wanda ya jiyo ta.

Tun da fari, 'yan sandan sun kai ta asibitin yankin, kafin daga bisani a mayar da ita asibitin Goa mai makwabtaka da jihar Maharashtra.

Shugaban asibitin koyarwa na Goa Medical Collage, Dakta Shivanand Bandekar, ya shaida wa jaridar 'The Indian Express' cewa Ms Kayi ta ji raunuka a jikinta, kuma alamu sun nuna tana fama da matsalar taɓin hankali.

"Ba mu san tsawon lokacin da ta ɗauka ba tare da cin abinci ba, amma sauran sassan jikinta na aiki yadda ya kamata," in ji Dakta Bandekar.

A ranar Juma'a, Ms Kayi ta ɗan murmure, lamarin da ya bai wa likitoci ƙwarin gwiwar mayar da ita asibitin masu lalurar ƙwaƙwalwa da ke gundumar Ratnagiria Maharashtra.

"A halin da ake ciki tana murmurewa," in ji Dakta Sanghamitra Phulena asibitin.

"Ana ba ta magungunan da suka dace, tana iya cin abinci, tana kuma ƙoƙarin yin hira da mutane. Idan tana buƙatar wani abu, za ta yi magana da wanda ke kusa da ita, amma fa turanci kaɗai take magana da shi."

Kayi ta rubutu abin da ya same ta a takarda
Bayanan hoto, Ms Kayi ta rubuta duk abin da ya faru da ita a jikin takarda

'Yan sanda sun ce Ms Kayi ƙwararriyar mai rawar Ballet ce, tana kuma yin Yoga a can Amurka, wasu rahotannin sun ce ta fito ne daga jihar Massachusetts a Amurka, ta koma zama a Indiya shekara 10 da suka wuce domin karantar fannin Yoga a jami'ar jihar Tamil Nadu.

A nan ne ta haɗu da mijinta, wanda 'yan sanda suka ce sunansa Satish, sun kuma fahimci sun samu saɓani da mijin nata.

Wasu rahotannin sun ce ta kwashe kwanaki biyu a wani Otal a jihar Goa, daga nan ta yi balaguro zuwa Mumbai birnin hada-hadar kasuwanci a Indiya.

Sai dai babu bayanin lokaci da yadda aka yi har ta samu kanta a tsakiyar dajin da aka gano ta a makon jiya.

Ms Kayi - wadda ba ta iya magana sosai - ta yi ƙoƙarin magana da likitoci da 'yan sanda ta hanyar rubutu a na'ura mai ƙwaƙwalwa ta hannu da aka gano tare da ita.

A nan ta ɗora haƙƙin abin da ya same ta kan mijinta, ta ce ya ɗaure ta a jikin bishiya, babu ruwa ko abinci har tsawon kwanaki 40.

Ta yi ikirarin ya yi mata wata muguwar allura da ta sanya mukamukinta ciwo, dan haka sai da dabara ake iya ba ta abinci ta hanyar sanyawa cikin ruwan da ake kara mata.

"Ni aka cuta, kuma na kuɓuta amma ya tsere ba a san inda yake ba" in ji ta.

'Yan sanda sun ce sun shigar da bayanai kan tuhumarsa da yunƙurin aikata kisa, an kuma tura tawagar 'yansanda zuwa jihar Tamil Nadu da Goa da Maharashtra, domin gudanar da bincike.

Sai dai har yanzu ba a gano inda mijin nata yake ba.

Kafafen yaɗa labarai sun ce ofishin diflomasiyyar Amurka a birnin Delhi, na matsawa 'yan sanda su matsa kaimi domin gano mutumin, amma sun ƙi amincewa yin magana da 'yan jarida.

Mai magana da yawun ofishin diflomasiyyar Amurka a Delhi, ya shaida wa BBC ba za su bayyana yadda binciken ke gudana ba kamar yadda aka san Amurka da ƙoƙarin kare bayanan sirri, wanda hakan ya shafi bayanan sirrin ɗan ƙasa.