Waɗanne manyan matakai Amurka za ta iya ɗauka domin kare Isra'ila?

Asalin hoton, Reuters
- Marubuci, By Jonathan Beale
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin BBC kan fannin tsaro, Ashkelon, Israel
Amurka ta yi alkawarin bayar da cikakken goyon baya ga Isra'ila kuma ta nuna hakan ta hanyar aika mata da taimakon soji.
Sai dai mutane na ci gaba da ɗanɗana kuɗarsu kan rikice-rikicen da aka yi a baya a yankin har yanzu, ta yaya Amurka za ta shigar wa Isra'ila faɗa?
A martaninsa na farko bayan harin da ƙungiyar Hamas ta kai wa Isra'ila, Shugaba Joe Biden ya fito ƙarara ya nuna ɓangaren da yake goyon baya: "Amurka na goyon bayan Isra'ila," in ji shi.
"Ga kowaye da yake tunanin amfani da damar don cimma manufarsa, ina da magana ɗaya: Kada ku kuskura," in ji Biden.
Wannan gargaɗi ne kai-tsaye ga Iran da kuma ƙawayenta.
Ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ta ce an kai wa sojojin Amurka hari a Iraqi da Siriya sau da yawa a 'yan kwanakin nan, kuma wani makamin kariya na Amurka da ke a cikin tekun Bahar Maliya ya katse hanzarin wani makami mai linzami da aka harba daga Yemen da nuufin kai wa Isra'ila hari.
Dama dai Amurka tana da dakarun kai farmaki a Gabashin Bahar Rum, waɗanda ake sa ran za su haɗe da wata rundunar da za a tura yankin nan ba da daɗewa ba a yankin.
Kowane daga cikin maka-makan jiragen ruwa masu ɗaukar jiragen saman yaƙi da Amurka ta girke a yankin na ɗauke da fiye da jiragen sama 70.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Mista Biden ya kuma umarci dubban sojojin Amurka su kasance cikin shirin ko-ta-kwana domin tafiya yankin idan buƙatar hakan ta taso.
Amurka ita ce ƙasa mafi girma da ke goyon bayan sojojin Isra'ila, tana bayar da tallafin tsaro na kuɗi kusan dala biliyan 3.8 a shekara ɗaya.
Amurka ce ta ƙera jiragen yaƙin da Isra'ila take amfani da su wajen kai hare-hare a Zirin Gaza, haka nan ma makaman da take amfani da su a yanzu.
Kuma Amurka ce ta ƙera wasu daga cikin makaman shingen tsaro na Iron Dome na Isra'ila.
Amurka na kan tura wa Isa'ila irin waɗannan makamai domin ci gaba da maƙare rumbunta tun ma kafin Isra'ila ta buƙace su.
Kuma a ranar Juma'a Shugaba Biden ya nemi majalisar dokokin Amurka ta amince da tallafin dala biliyan 14 don taimaka wa Isra'ilar, a matsayin wani ɓangare na tallafin soji na dala biliyan 105.
Washegari, Cibiyar tsaron Amurka ta Pentagon ta sanar cewa za ta aika da na'urorin tsaronta na makami masu linzami guda biyu zuwa Gabas ta Tsakiya.
Amma ko shugaban Amurka zai yarda ya shiga wani yaƙi, musamman a shekarar zaɓe?
Shiga tsakanin da sojojin Amurka suka yi a baya-bayan nan a yankin bai wanye da daɗi ba - ta fuskar siyasa, tattalin arziki da kuma ta fuskar rayuwar Amurkawa.
Michael Oren, tsohon jakadan Isra'ila a Amurka, ya yi amannar cewa shugaba Biden ya riga ya ɗauki matakin farko ta hanyar tura jiragen ruwan dakon jiragen yaƙin Amurka a yankin.
"Ba za ku fitar da irin wannan makami ba sai dai idan kuna son amfani da shi," in ji shi.
Amma Seth G Jones, darektan Tsaro na ƙasa da ƙasa a Cibiyar Dabaru da Nazarin ƙasashe a Washington, ya ce Amurka ba za ta yi gaggawar jefa kanta cikin yaƙi kai-tsaye ba a Gaza.
Ya ce kasancewar jiragen yaƙi a yankin "abu ne da zai iya zama mai amfani", koda kuwa ba a yi amfani da su ko sau ɗaya ba." Musamman ganin cewa za a iya amfani da su wajen tattara bayanan sirri da kuma samar da kariya ta sama. Duk wani yukuri na shiga yaƙin zai zama "mataki na karshe", in ji shi.
A yanzu babban abin da ke razana Amurka da Isra'ila shi ne barazanar ƙungiyar ƴan bindiga ta Hezbollah daga arewacin Isra'ila.
Ƙungiyar da ke samun goyon bayan Iran, babbar barazana ce fiye da Hamas ta Gaza.
Tana da rumbun makaman rokoki kimanin 150,000 waɗanda suke da karfi da inganci fiye da waɗanda Hamas ke amfani da su. Kuma tuni ta fara yin musayar wuta da Isra'ila, wadda take kallo a matsayin babbar maƙiyiyarta.
Mista Oren na fargabar cewa Hezbollah za ta shiga cikin yaƙin a daidai lokacin da Isra'ila ta riga ta yi nisa a cikin Gaza kuma ta riga ta jajirce sannan ta gaji.
Idan haka ta faru, to Mista Oren ya yi amammar cewa akwai yuwuwar a lokacin Amurka za ta yi amfani da jiragen samanta na yaƙi wajen wajen kai hari a cikin Lebanon, ko da yake ba ya tunanin Amurka za ta tura dakarunta ta ƙasa.

Asalin hoton, Reuters
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken da sakaren tsaro Lloyd Austin dukkansu sun jaddada cewa Amurka za ta mayar da martani idan yaƙin ya fantsama kuma aka far wa jami'anta ko kuma sojoji.
Amurka na da ikon kare kanta, a cewar Mista Austin a ranar Lahadi, kuma ba za ta yi jinkirin ɗaukar "matakin da ya dace ba".
Mista Jones ya yarda cewa akwai hatsari idan yaƙin ya ci gaba da faɗaɗa, sai dai ya yi imanin cewa, matakin Amurka na yin gargaɗi "yana kara barazana ga Iran da muƙarrabanta".
Ya ce idan Hezbollah ta shiga yaƙin daga arewacin Isra'ila, "Akwai yiwuwar za su gamu da martani mai tsanani". Ya bayyana cewa a baya sojojin Amurka a yankin sun fuskanci hare-hare nan-da-can daga ƙungiyoyin da ke samun goyon bayan Iran.
Isra'ila ba ta neman taimakon soji na kai-tsaye a yaƙinta da Hamas.
Danny Orbach, farfesan tarihin sojoji a Jami'ar Hebrew a Jerusalem, ya bayyana cewa dokokin sojojin Isra'ila sun bayyana cewa ya kamata su iya kare kansu da kansu.

Asalin hoton, Getty Images
Ziyarar da shugaba Biden ya kai Isra'ila a wannan mako ta nuna cewa goyon bayan da Amurka za ta bai wa Isra'ila yana da wani sharaɗi.
Yana son Isra'ila ta ba da damar shigar da agaji zuwa yankin Gaza, kuma ba ya son ganin Isra'ila ta mamaye tare da yin zaman dirshan a Zirin Gaza.
Ya gaya wa shirin gidan talabijin na CBS cewa yin hakan zai zama "babban kuskure".
Tallafin Amurka kuma yana iya zama ƙayyadajje.
Yaacov Katz, wani manazarci a fannin soji kuma mawallafi a jaridar Jerusalem Post, ya yi imanin cewa, goyon bayan da Amurka ke bai wa Isra'ila zai fuskanci matsin lamba da zarar aka fara aikin soji a zirin Gaza, sannan kuma fararen hular da ake kashewa suka riƙa ƙaruwa.
Ya yi imanin tallafi na iya yin kasa cikin makonni. "Ba na ganin Isra'ila za ta samu ƙarin dama daga Amurka ko kuma duniya don kai hare-hare ta kasa wanda zai ɗauki tsawon lokaci," in ji shi.
A fili dai Amurka na fatan goyon bayan soji da take bai wa Isra'ila da haɗin gwiwarta na soji a yankin zai isa ya hana yaɗuwar rikicin.
Akwai 'yan misalan yadda Amurka ke shiga tsakani kai-tsaye a madadin Isra'ila.
Aika wa Isra'ila da makamai da Amurka ta yi don kare kanta daga hare-haren makamai masu linzami na Iraqi, gabanin mamayewar da ta yi a yaƙin Gulf na 1991, ba kasafai ba ne.











