Ko samame ta ƙasa da Isra’ila ke shirin kai wa Gaza zai yi nasara?

Asalin hoton, Saeed Qaq/Anadolu via Getty Images
- Marubuci, Paul Kirby
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC NEWS
Shugabannin Isra'ila sun bayyana aniyarsu ta shafe Hamas daga doron kasa, domin hana Gaza komawa yadda take a baya.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewar:
"Sunan kowanne ɗan Hamas gawa" bayan mayakan Hamas sun kashe mutane 1,300 sakamakon harin da suka kai Isra'ila.
Manufar Operation Swords of Iron ta zarta duk wani shirin hari da sojoji suka shirya kaiwa Gaza, shin ko wannan kudiri zai tabbata, kuma wace hanya kwamandojin yaƙin za su yi amfani da ita wajen jagorancin farmakin?
Harin ƙasa na Zirin Gaza zai haɗa da gidaje, al'amarin da ya ke da matukar hatsari ga fararen hula. Tuni dai hare-haren jiragen sama ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane yayin da sama da mutane 400,000 suka tsere daga muhallansu.
Aikin da sojojin Isra'ilan za su yi zai haɗa da batun tseratar da akalla mutane 150 da aka yi garkuwa da su a wurare daban-daban a Gaza.
Shugaban Dakarun Isra'la, Herzi Halevi, ya ci alwashin kawo ƙarshen Hamas, ko yaya Gaza za ta koma bayan shekaru 16 na mulkin Hamas?
Amir Bar Shalom mai sharhi ne kan ayyukan sojoji a gidan Rediyon sojojin Isra'ila ya ce:
"Ba na jin Isra'ila za ta iya kawo ƙarshen mambobin Hamas gada ɗaya domin aƙida ce ta tsattsauran ra'ayin Addinin Islama, amma za ku iya rage musu ƙarfi yadda ba za su iya gudanar da ayyukasu ba.''

Asalin hoton, Ahmed Zakot/SOPA Images/LightRocket
Isra'la ta fafata yaƙi huɗu da Hamas, kuma a kowanne lokaci ba ta yin nasarar daƙile harin rokokinta.
Kakakin Soji, Kanar Jonathan Conricus ya ce a karshen wannan yaƙi Hamas ba za ta sake samun ƙarfin soji da yi wa fararen hular Isra'ila barazana ba.
Mamayar ƙasa mai cike da haɗari
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Farmakin sojan zai iya fuskantar kalubalen da zai hana shi nasara.
Bangaren Hamas masu ɗauke da makamai watau dakarun Izzedine al-Qassam sun shirya wa harin Isra'ilan.
Tuni sun tanadi abubuwan fashewa tare da shirya kwanton ɓauna. Kuma za su iya amfani da hanyoyinsu na ƙarƙashin ƙasa wajen kai wa dakarun Isra'ila hari.
A shekarar 2014, rundunar ƙananan sojin Isra'la ta yi asarar rayuka yayin da wasu suka samu muggan raunuka sakamakon tashin nakiya da harbin bindiga da kuma kwanton ɓauna yayin da daruruwan farar hula suka mutu a Arewacin Gaza.
Wannan ne dalilin Isra'la na buƙatar Falasɗinawa sama da miliyan ɗaya su fice daga arewacin Zirin Gaza.
An gargadi Isra’ilawa cewa, yakin na iya daukar watanni, kuma dakarun kar-ta-kwana akalla 360,000 sun shiga cikin sojoji don gudanar da aiki tare.
Tambayar ita ce har yaushe Isra'ila za ta ci gaba da yaɗa manufofinta na yaƙin ba tare da ƙasashen duniya sun buƙaci ta janye ba?
Hukumar Kula da Ƴan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin ana samun ƙaruwa a adadin wadanda suke mutuwa a yayin da aka datse hasken lantarki da ruwa da kuma mai a Gaza.
Yossi Melman, Jami'in Hukumar Leken Asiri a Isra'la ya ƙara da cewar:
"Gwamnati da Sojoji na ganin sun samu goyon bayan ƙasashen duniya musamman shugabannin ƙasashen Yamma, abin da ya fi muhimmanci shi ne, in da akwai lokaci kamata ya yi a nemi ƙarin gayon baya.''
Ya tabbatar da cewar nan ba da jimawa ba ƙasashen ƙawancen Isra'ila za su yunƙoro idan suka fuskanci al'umma na fama da yunwa.
Ceto waɗanda aka yi garkuwa da su
Da dama daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin ƴan Isra'ila ne, da kuma wasu ƴan ƙasashen ƙetare, wannan ce ta sa wasu gwamnatoci da suka haɗa da Amurka da Faransa da kuma Birtaniya suke da hannu a wannan aiki don ceto al'ummarsu lafiya.
Shugaba Emmanuel Macron ya sha alwashin karɓo iyalan Faransawa ƴan Isra'la:
"Faransa ba za ta watsar da ƴaƴanta ba."
Babu tabbas ko makomar waɗanda aka yi garkuwa da su za ta yi tasiri a tsarin sojojin yayin da shugabannin Isra'ila na fuskantar matsin lamba.
Amir Bar Shalom ya kwatanta yanayin da abin da ya faru a birnin Munich a shekara ta 1972 lokacin da wani Bafalasɗine ɗan bindiga ya yi garkuwa da ƴan wasan Isra'ila sannan ya kashe 11 daga cikinsu.
Tseratar da mutane da dama daga wurare daban-daban a Gaza zai iya yi wa kwamandojin Sayeret Matkal na Isra'ila wahala. Tuni Hamas ta yi barazanar harbe wadanda ta yi garkuwa da su a matsayin martanin harin Isra'ila.
A shekara ta 2011 Isra'ila ta yi musayar fursinoni sama da 1,000 a madadin wani soja mai suna Gilad Shalit, wanda Hamas ta tsare har tsawon shekaru biyar. Amma a yanzu Isra'la za ta sake yin duba kafin musayar fursunoni la'akari da yadda Yahya Sinwar ya zamo jagoran siyasar Hamas a Gaza bayan an sako shi a matsayin fursunan musaya.
Maƙwafta sun sanya idanu
Abin da kuma zai iya shafar tsawon lokacin da yaƙin zai ɗauka shi ne ra'ayi da martanin ƙasashen da suke maƙwaftaka da Isra'ila.
Tana iya fuskantar ƙarin wasu bukatu daga Masar, wadda ke kan iyaka da Gaza kuma tuni ta fara neman a bayar da agaji ta kan iyakar Rafah.

Asalin hoton, SAID KHATIB/AFP
An sanya tsaro a iyakar Isra'la da Lebanon bayan hare-haren ƙungiyar Hezbollah a kan iyakokin ƙasashen biyu.
Iran, wadda ke ɗaukar nauyin Hezbollah ta yi barazanar kaddamar da harin martani a Isra'la, al'amarin da ya sa Shugaban Amurka Joe biden ya gargadi Kasashe ko Ƙungiyoyi da su guji amfani da wannan dama wajen kai hari.
Mene ne ƙarshen matakin Isra'ila a Gaza?
Idan aka yi nasarar rage wa Hamas ƙarfi, tambayar ita ce mene ne zai maye gurbinta.?
A shekara ta 2005 Isra'ila ta janye dubban sojojinta daga Zirin Gaza kuma ba ta da niyyar komawa.
Ofir Winter na ganin canji a shugabanci zai bayar da hanyar dawowar Hukumar Falasɗinawa watau (PA) wadda Hamas ta kora daga Gaza a shekara ta 2007.
A yanzu PA ce ta ke iko da wasu yankunan Gabar Yamma da kogin Jordan.
Ƙasar Masar ma za ta yi maraba da maƙwafciyar da ta dace.
Za a sake ginin Gaza kamar yadda ta ke a baya kafin yaƙe-yaƙe.
Tun kafin ta'addancin Hamas a Isra'ila, an sanya takunkumi kan shigar da kaya Gaza, a yanzu Isra'ila za ta sanya takunkumai masu tsauri.
Duk yadda makomar yaƙin ta kasance, babu shakka Isra'ila za ta tabbatar irin wannan harin ba zai sake faruwa ba.










