Bayani kan hanya ɗaya tilo da Falasɗinawa za su iya fita daga Gaza

Asalin hoton, Reuters
Falasɗinawa suna ci gaba da taruwa a kan iyakar Rafah da ke kusa da Masar a kudancin Zirin Gaza domin tsere wa hare-haren da ake tsammanin Isra'ila za ta kai nan gaba.
Kafafen yaɗa labarai na Amurka sun ruwaito cewa za a buɗe ne domin duka ƴan kasashen biyu su samu damar ficewa, da kuma damar shigar da kayan jin-ƙai, ba tare da bayar da wani wa'adi ba.
Har zuwa safiyar ranar Litinin kan iyakar a rufe take.
Iyakar Rafah tsakanin Gaza da Masar
Ita ce mashigar da ke kan iyakar kudancin Gaza da Masar ta hamadar Sinai.
Akwai iyakoki biyu da ake iya shiga Zirin Gaza ta kansu - Erez, iyaka ce da ake shiga Gaza daga yankin arewacin Isra'ila, sai kuma ta Kerem Shalom, wadda babu wani abu da ake a cikinta sai kasuwanci tsakanin Gaza da ISra'ila. Amma duka an rufe su.
Me ya sa iyakar take da muhimmanci yanzu?
A ranar 7 ga watan Oktoba ne dakarun Hamas suka lalata mashigar Erez da ke arewacin Gaza. Kwanaki kaɗan Isra'il ta sanar da rufe ta baki ɗaya babu shiga babu fita daga Gaza.
Rafah ita kaɗai ce mashigar da za a iya kai kayan agaji a yanzu.
A makon jiya, ministan harkokin wajen Masar ya ce Masar ta bai wa duka jirage da tawagogin bayar da agaji na duniya da za su shiga Gaza su karkata zuwa filin jirgin sama da Al-Arish da ke arewacin Sinai.
Kuma gwamman motoci ɗauke da man fetur da kayan agaji sun yi dogon layi a bakin mashigar ta Rafah, suna jiran umarni.

Me ke faruwa a mashigar?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun bayan fara kai harin da Hamas ta yi kan Isra’ila a ranar 7 ga watan Oktoba, an ta yaɗa rahotanni masu ruɗani a game da halin da ake ciki kan mashigar Rafah.
Hamas da Masar ne ke da iko kan wanda zai shiga ta wurin, amma Isra’ila na da damar kawo tsaiko ga mashigar ta hanyar kai hare-hare kusa da iyakar.
Kafafen yaɗa labarai na Masar sun ce an rufe mashigar ne biyo bayan wasu hare-hare biyu ta sama da Isra’ila ta kai a ranar 9 da 10 ga watan oktoba, wanda suka ce hakan ya raunata mutane daga ɓangare Masar da kuma na Falasɗinawa a mashigar.
A ranar 12 ga watan Oktoba, Gwamnatin Masar ta nemi Isra’ila ta daina kai hari kusa da mashigar Rafah, domin ta zama hanya guda ta ceton rayuwa ga mutanen da ke Gaza, kuma ta yi bayani a bayyane cewa ba za ta buɗe iyakar ba har sai an tabbatar da amincin ma’aikatanta da za su yi aikin ceto.
Ƙasashen yamma na ta ƙoƙarin ganin an tabbatar da amincin mutanen da ke Gaza masu fasfo ɗin wasu ƙasashen da kuma masu kai kayan agaji da za su bi ta mashigar Rafah.
Sakataren harkokin wajen Burtaniya, James Cleverly da takwaran aikinsa na Amurka, Antony Blinken suna aiki tare da Isra’ila da Masar da sauran manyan ‘yan siyasar da ke yankin kan buɗe mashigar.
A makon jiya, wani jami’i da ke magana da yawun ma’aikatar cikin gida ta Amurka ya shaida wa ‘yan ƙasar cewa su koma bakin mashigar Rafah “za a sanar idan har an buɗe mashigar amma za a buɗe ta ne na wani ɗan lokaci”.
A ranar Litinin, an samu dandanzon mutanen a iyakar, sakamakon labaran da aka riƙa yaɗawa cewa za a buɗe iyakar na wani ɗan lokaci saboda an cimma matsayar tsakaita wuta, sai dai duka ɓangarorin Isra’ila da Hamas sun musanta haka.

Me ya sa iyakar take a rufe ?
Isra'ila na son hana mayaƙan Hamas tserewa daga Gaza, kuma suna son duba duk wata motar kai ɗauki da za ta shiga Gaza domin tabbatar da cewa babu masu ɗauke da makamai.
Haka ita ma Masar tana aiki tare da sauran ƙasashe domin ganin an buɗe mashigar ga 'yan ƙasashen ketare da kuma kai kayan agaji, Gwamnatin Masar na nuna fargabar kada a samu tururuwar Falasɗinawa zuwa Sinai kuma da fargabar kada iyakar ta zama hanyar ficewa ga kowa.
Kuma tana fargabar kada a samu kwararar masu iƙirarin jihadi zuwa ƙasar.
Yaya ake amfani da mashigar Rafah gabanin rikicin?
Dama ba a barin Falasɗinawa ficewa daga Gaza cikin sauki ta mashigar Rafah.
Duk Bafalasɗinen da ke fatan tsallaka iyakar sai ya yi rajista da hukumomin Falasɗinawan, mako biyu ko hudu gabanin hakan, kuma zai iya yiwuwa a ƙi ba su damar ficewar.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya hukumomin Masar sun bar mutane 19,608 sun fita daga Gaza sun kuma hana 314 fita a watan Agustan 2023.















